Sashe 20
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana tafe, za mu yi fada, in Allah ya kawo mana ita ai kin ga yau sa wadata in dai don nama ne, don na ji an ce ta yi mai kwarai." Kura ta dubi biri, ta ce, "Ka ji ko, gaskiyata ce da na ce lalle abin nan ya fi ni karfi, ka ji jiya ma sai da ya kashe wani kura. Na san lalle bunsuru ba ya iya daurewa ya yi mini haka ba, ko daji ma ba ya yarda ya fito ba, wanda kullum yana can boye cikin gari. Ni zan koma tun bai rigaya ya gan ni ba!" Biri ya ce, "Kada ki lura da zancensa, fankama kawai ya ke yi 80 miki da karairayi, na gan shi dan karamin abu ne, kuma da ganin tafiyarsa ka ga raggo. Da kura ta ji haka zuciyarta ta yi dan karfi, ta ce, "To, mu tafi." Ko da bunsuru ya hango ta, sai ya tura 'ya'yansa a cikin kogon kura, suka soma kuka gaba daya. Ya ce wa akuya, "Don Allah gaya musu su yi shiru, biri ya yi mini alwashin zai yi dabara ya kawo mini kura har nan gidana, in sun yi hayaniya yaya za ta yarda ta iso, balle mu samu mu kashe ta mu sami abin kalacin? Kun gani fa yau saboda ita ba mu yi tanajin kome ba, a gare ta muka dogara." Da kura ta ji haka sai ta kama biri, ta ce, "Ashe da munafunci aka kulla da kai, don ka sa a kashe ni a banza? To, Allah ya tona asirinka, dan banza!" Zai yi magana ta sa kafa ta taka shi, ta kashe. Ita kuwa ta yi baya da gudu tana zawo. Da bunsuru ya ga sun sami sa'a haka sai suka kwashe duk kayan da ke gidan suka kama hanya suka koma gari gidansu. Aku ya dubi Musa, ya ce, "To, mu tafi, kyaun dan halas duk abin da ya yi niyya ya cika. Abin da ke aukuwa ga mai yin alkawari ba ya cikawa, in ka ji ai sai ka yi kurum." Musa ya ce, "Me ke faruwa ga mai saba alkawari? Don mutum ya yi niyyar abu, ya koma ya fasa, sai wani abu ya same shi?" Aku ya ce, "Babban mugun abu kuwa zai same shi." 81 Labarin Sarkin Busa Abin da ya sa na ce haka, a wani gari can ketaren Bahar Maliya a cikin kasar Jamus, tun shekaru da yawa da suka wuce, Allah ya saukar musu da wani babbar bala'i. Aka saukar musu da beraye ko'ina cikin garin. Berayen nan suka yi ta karuwa, har mutane suka rasa abin da su ke ciki, duk inda mutum-ya duba garin ba ya ganin kome sai beraye. Ko wajen barci mutum in ya zo sai ya tarad da kamar ashirin tuku-tuku suna kwance. In hula ka ajiye, ko riga, kafin da safe sai ka tarar aljihun cike da beraye. In takaice maka labari, yawansu ba su kidayuwa. In da za ka kidaya su, ka kidaya kudajen da ke garin, sai ka ga sun fi yawan kudajen nan kamar sau dari. Gari dai ba wajen sa kafa, duk beraye ne. Abinci kuwa mutum ko ya fi Aula dabara, ba yadda zai yi ya ajiye shi. Kome za a dafa sai a yi daidai da yadda za a iya cinyewa, don ko cikin akwati ka sa abinci ka kulle, sa san yadda za su yi wa akwatin nan huda, su shiga su cinye. Duk wani abu da ka sani ana yi da fata sun cinye. Ba ka ganin mai takalmi, ko matashin kai, ko gafaka, ko buzu a garin. In ko sun kai ga abin da ba su ci, sai su yi masa hudoji, su bata shi. Ta ishe ka ma ko jariri suka tarar yana barci, sai su tasam masa da cizo za su cinye. Sai in ya yi kuka iyayen su kwace shi. In dare ya yi kuma su kan hana mutane barci da kuka da gujeguje. In sun ga jikin mutum waje, sai su kama da cizo, wai za su cinye shi. To, kada ka zargi mutanen garin, ka ga kamar sakarci ya hana su kashe su. Bala'i sai sa'ad da Mai abu ya sawwake abinsa. Da sun ga kare sai su tasam masa, su nuna masa Sarkin Yawa ya fi Sarkin Karfi. Don kyanwa kuwa, wannan karamar alhaki, ba su kula da ita ba. Abin mamaki, mutane kuma in sun tasam ma kashe su, sai ka ga kamar kara su su ke yi. Don a sa tarko kuwa, ko a sa dafi cikin abinci a ajiye, duk wannan ba ya rudinsu. Da sun gani sai su kewaye, kamar gaya musu a ke yi. Duk mutanen gari suka rasa yadda za su yi, sai suka tasam ma mai garin, suna cewa shi ne ke da gashin tsiya, don tun da aka 82 halicci duniya ba su taba jin irin wannan ba, sai cikin wannan zamani da ya ke sarauta. Suka ce ko dai ya san yadda zai yi da berayen nan, ko kuwa su fitad da shi, su kore shi daga kasar. Sarkin ya rasa inda zai sa kansa. Mutanen gari kuwa sai kara matsa masa lamba su ke yi. Ran nan yana zaune zugum, wadannan dattijai su zö su zazzage shi su wuce, wadannan su zo su zunzungure shí su wuce. Sai ga wani dan tsoho bako ya zo, ya duka ya gai da Sarki. Sarki ya dube shi, ya gan shi wani iri, sai ya ce, "Malam, daga ina? Wace sana'a ka ke yi?" Tsoho ya ce, "Ga ni dai. Inda na fito da nisa, amma sana'ata busa, har mutane na kirana Sarkin Busa." Sarki ya ce, "To, sai ka je ka sauka, in kana iya sauka nan, mu ba ta busa mu ke yi ba yanzu, ta kawunammu mu ke yi da wannan bala'i." Sarkin Busa ya ce, "Ai ni ma ba busar banza na ke yi ba, wani asiri Allah ya ba ni wanda in na yi busa duk ko wane abu mai rai ya biyo ni. Da kwadi, da macizai, da beraye, da dukan naman ruwa da na tudu, da tsuntsaye, har da masu tafiya da kafa biyu, duk wanda ya ji na yi busa, ba sauran zama, sai ya yi ta bi na. Don wadannan 'yan berayen da suka dame ku, in ka iya ba ni abin da na ce, yanzu sai in raba ku da su." Sarkin ya ce, "Don Allah ka taimake mu! Kome ka ke so nan duniya na ba ka. Tambayi, mu ji." Sarkin Busa ya ce, "Ka ba ni sule dari, in na raba ku da su?" Sarkin ya dube shi, ya ce, "Yau ga abin mamaki, mene ne sule dari kuma! Sule dubu goma ma, in kana so sai in ba ka. Kai dai mu rabu da wannan bala'i." Sarkin Busa ya ce, To, madalla." Ya sa wata irin mabusa bakinsa, ya yi ta-busa, yana yawo cikin gari rariya rariya. Sai berayen nan suka yi ta fitowa ko ta ina, suna binsa tururururu, wadansu manya, wadansu kanana, wadansu tultul, wadansu kyamas-kyamas. Ga wadansu ja wur, wadansu fari fat, abin har da shudda da rawaya. Ka ga wadansu ruku-ruku da ciki wadansu kuwa ga 'ya'ya kanana ke biye da su. Sai tsalle-tsalle su ke yi, suna 'yan kuka tsui tsui, kamar suna fara'a da wata bushara. Da ya kwashe duk, sai ya nufi kogi yana busa, suna biye, mutane na kallo na murna. Da isarsa bakin kogi sai ya fada cikin ruwa yana busa, beraye kuma ba su san sa'ad da suka bi shi ba, duk suka mutu cikin ruwa, sai daya kadai ya tsere. Mutane suka yi ta yi wa juna barka. A tsaya ma a fadi farin cikin da mutanen garin nan su ke yi da rabuwa. da wannan bala'i, ya zama kauyanci. 83 Da Sarki ya hangi Sarkin Busa na dawowa, sai ya ce wa mutane kowa ya koma gidansa, su kwaba kasa su lillike ramummukan da berayen nan süka giggina. Da Sarkin Busa ya iso, Sarki ya yi masa godiya kwarai. Sarkin Busa ya ce, "To, madalla, sai ka cika alkawarinka ko? Allah ya ba ka nasara." Sarki ya bata fuska, ya ce a ransa, "To; yanzu in na ba shi sule dai dai har dari, to, ni yaushe zan tara kudi in ina haka? Beraye dai ne ganin idon kowa sun mace, ba su ko komowa. In ma ba zarinsa ba dan tsoho da shi tukuf haka, me zai yi da sule dari?" Ya dubi Sarkin Busa, ya ce, "Ai da wasa na ke yi maka da na ce zan ba ka sule dari. Ashe kai ba ka san wasa ba? Ga dai sule sha biyar sun ishe ka. Me za ka yi da kudi da yawa ga shi ka tsufa?". Sarkin Busa ya harari Sarki, ya ce, "Zancen banza. Kai din ba ka tsufa ba da ka ke alkawari ba ka cikawa? Yi maza ka ba ni in kana ba ni, in ci gaba. Ba a kanku na fara ba!" Sarki ya ce, "In ba rashin hankalinka ba, yanzu yanzu da isowarka har ka yi aikin sule dari? Ko sha biyar din da na ce ai don dad'in girmana ne. In an bi kididdiga ne, ni ke uku da sisi ba ka ci ba. Dubi fa tun da safe har la'asar mutum ke aiki a ba shi sisi, balle kai yanzu yanzu!". Sarkin Busa ya ce, "In fa ba ka ba ni abin da ka yi alkawari ba, yanzu na sake mabusa, ka ga kuma abin da zai faru." Sarki ya yi fushi, ya ce, "Sake mana! Mu-ze a ci da burga, sai ka ce ba mutanen birni ba? Wanda ya mutu ban da Allah wa ke iya rayad da shi?" &4 Sarkin Busa ya ce, "Ko ni ban ce ina iyawa ba, amma ka ga abin da zai faru." Sai ya dauko wata mabusa ya fara busa, ya shiga gari titi titi yana busawa. Sai yaran gari duk mai iya tafiya, tun daga mai shekara uku har goma, suka yi ta fitowa suna binsa da gudu, suna tafa hannu suna rawa. Wani yaro mai dan dama daga cikin 'ya'yan Sarki ya rika ba da waka, saura