Sashe 17
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya sayo, ya kuma biya mahauta, ya sayo musu tsire ya dora kan tuwon, ya dauko ya nufo daji. Yana kulle-kullen abin da zai aikata da kuďin nan, da nasa ne shi kaďai. Sai ya ga itacen tinya, ya ajiye kayansu, ya ce, "Alhamdu lillahi! Bari in debi ruwan tinya in zuba wa abincin nan, in kai musu. Ni kuwa ko sun ce in ci, sai in ce na ciwo daga kasuwa. Ka ga da sur ci duk sai su mace, ni kuwa in kwashe karfena, in shiga gari in yi ta kece raini." Ya karya tinya ya zuba. Shi kuma ashe kafin ya dawo 'yan'uwansa sun yi shawara da ya zo su kashe shi, su kwashe kudi, su raba su kadai. Suka ce ai haka abin ya fi auki. Can sai wannan karamin ya iso da kayan abinci. Ko da ajewarsa sai suka hau masa da bugu, bai san hawa ba, bai san sauka ba, suka kashe shi. Suka fada abinci da ci, in sun gama sa'an nan su kwashe kudi su san inda suka nufa. Da gama cinye abinci, sai kowanensu ya fara kaduwa, yana faduwa yana tashi, kafin kiftawa da bismilla duk suka kai takarda. Can bayan kamar kwana bakwai sai Kado ya ce a ransa, "Bari in koma wurin nan, in na tarar suna kwashe kudinsu in tsuguna in yi kala, ko Allah ya ba ni dan taro. In kuwa na tarad da su sai in ce na zo ne in gaya musu Sarki zai aiko da dogarai a kama su gobe, abin da ya fi kowa ya yi ta kansa. In ce kuma abin da ya sa na gaya musu don haka, sun ji kaina ne ran nan. Ka ga watakila ma sa ba ni dan sule. Kuďin dai ga su nan tsibe kamar ba su so, ba su da alamar karewa." Da isarsa wurin sai ya tarad da su duk sun mutu. Ya yi juyayin abin da ya kashe su, ya rasa. Da ya lura har kuraye sun ci su, sai ya yi zaton su ne suka kashe su. Ya rasa abin da zai yi don murna. Ya shimfida gwadonsa, ya kwasa. Ya yi 'yan kirare ya dora, don kada a gane, ya kai gida, ya gina rami ya binne. Magariba na yi kuma ya kira dansa, suka tafi suka kwashe saura. Ya zauna ya yi ta cin kudinsa sannu kan hankali, da shi da dansa, ba wanda ya gane. Musa ya bingire da dariya, ya ce, "Allah mai girma! In rabo ya rantse, sai mai shi!" 66 Ya Saurara haka sai ya ji kiran salla, ya ce wa aku, "Wancan kiran sallan fa, na fari ne, ko na biyu?" Aku ya ce, "Sai dai na fari. Amma bari mu ji." Sun yi shiru suna saurare, sai suka ji ladani ya ce, "Assalatu!" Musa ya ce, "Subuhana lillahi, ashe har gari ya waye ba mu sani ba!" Sai ya tashi fuu ya shiga cikin gida. Tun safiyan nan kar magariba bai sa ko loma bakinsa ba don bakin ciki. Ko da wata ya fadi, tun ba a ko yi kiran sallar asuba ba sai ga Musa ya shiryo. Ya zo ya ce wa aku, "Sai na dawo." Aku ya ce, "Ka dawo lafiya." Ya sake duban Musa, ya ce,"А! Kam ba Waziri ba, a dubi kakkarfan dan Sarki kamarka a ce za a hana shi zuwa yaki? Shin halin Waziri wane iri ne?" Musa ya ce, "Rabu da shi tsohon wofi! Ko da ya hana, ai ga shi yanzu za ni yana gani." Aku ya ce, "Tafi abinka, rabu da shi! Kome mutum ke aikatawa dai ai, kul ba jima, kul ba dade, ya ga sakayya. Da Allah ya sa ya ji labarin Hafaru da dansa, da ya rage wadansu abubuwa." Musa ya ce, "Wane labari ne na Hafaru da dansa? Gaya mini, ko ni ma in karu.'" Aku ya cе: 67 Abin Da Mutum YaShuka Shi Zai Girba, In Hairan Hairan, In Sharran Sharran Wata rana an yi wani mutum wanda ba shi da da, ba shi da jika. Ya yi maganin duniyan nan don ya sami da, Allah bai nufa ba, y gaji ya dangana. Ran nan yana zaune a kofar gidansa, sai ya ga wani ya kama dansa yana ta duka, ba ji ba gani, sai ya ce, "M, Allah mai girma! Dubi wani Allah ya ba shi har yana bugu, ni kuwa ga shi ina nema ruwa a jallo, Allah bai nufe ni da samu ba. In da ni Allah ya ba wannan, kome rashin jin kansa, me zai sa in buge shi? Da da ya yi jin kai, da kada ya yi, ai duk uwarsu daya, in ba dai don batan basirar mutane ba." A kwana a tashi, ran nan sai Allah ya ba matar mutumin nan ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji. Aka yi suna, aka sa wa yaron nan Hafaru. Yaron ya girma a sangarce, kome ya yi uban ba ya ce masa kanzil. Ta kai dai fagen yaron nan ba ya jin kan uban, balle ya taimake shi. Don son da uban nan ke yi wa dan har abinci ma tare su ke ci, har ya kai ga aure ba su raba kwarya da ubansa ba. Da ubansa ya fara tsufa sai Hafaru ya rika kyamar cin abinci da shi. In suna ci sai ya hana uban ya taba gabansa, yana cewa wai uban ya faye kazanta, duk yana-barin majina a hanci, wai kuma ga shi da yawan tari, yana zuba musu yawu a ciki. Uban dai bai ce masa kome ba. Ana nan dai har ya kai ga fagen yana ci hannu na rawa, na baka na fadowa cikin kwarya. Sai dan ya buga masa tsawa, ya janye kwanon abincin, ya ce sai ya ci kana ya ba uban. Suna nan haka, sai ran nan Hafaru ya ce wai uban ba ya sude kwarya, kullum sai ya bar kwano cakal, duk ya bata shi da yawu. Saboda haka sai ya samar wau uban akushi, aka rika zuba masa nasa abincin dabam. Ran nan yana ci garin makyarkyata sai ya tuntsurad da dan akushin, tuwon ya zuba. Hafaru ya zo ya yi ta yi masa fada, wai ya faye gidi-gidi. Saboda haka sai ya tafi kasuwa ya sawo kwami irin na ban ruwan shanu, ya kawo gida ya rika zuba wa uban abinci a ciki, ya ce, "Ture wannan kuma, mu gani!" 68 Uban dai bai ce kome ba, sai in abin ya dame shi ya yi ta kuka yana. cewa, "Wannan dai duk laifina ne da na ki kwabonsa tun yana karami. Amma ba kome, Allah ya ba da mai rama mini." A kwana a tashi, sai ran nan Allah ya ba matar Hafaru ciki, ta haifi da namiji, aka sa masa suna Ishiye. Da ya kai shekara hudu ya yi wayo, sai ya zama ba shi da wajen wasa sai tare da kakansa, ko abinci ma tare su ke ci. Uban ya yi ya yi ya hana shi cin abinci da kakan, yaro ya ki. Saboda yaron nan har aka rika sa wa abincin tsohon mai da nama. Kome yaron nan ma ya samo sai ya nufo kakansa. Ana nan har Ishiye ya kai shekara shida, ran nan suka tafi gona da uban, yana rike masa da goran ruwa. Da suka isa uban ya yi ta noma, har rana ta yi tsaka, sai ga matarsa, uwar yaron, ta kawo masa abinci, ya kakkabe hauyarsa, ya zo ya zauna yana ci, matar kuwa ta zauna kusa da shi. Sai yaron ya dauki wani dan guntun gatari da ke nan, ya shiga gona ya fara saran wata 'yar itaciya da ke ciki, kwas, kwas, kwas. Da uban ya hanga ya gan shi, sai ya се, "Kai me ka ke yi nan? Ajiye wannan abin banza, ka zo ka ci abinci. Haka ku ke yi har ku sare 'yar kafarku, ku bar mutane da jiyya." Da yaron nan ya ji haka, sai ya ce wa uban, 'Ci naka, ka bar mini nawa nan. Ni ina nan sai na sare itacen nan tukuna, ina so in gyara rassan ne in yi maka dan kwami da shi, in kai gida in ajiye, don in ka tsufa in rika zuba maka abinci a ciki!"" Da iyayen yaron nan suka ji haka, sai suka yi nadama, suka rike baki suka ce, "Ashe gaskiya ne abin da mutane ke fadi, kome ka shuka shi ka kan girba." Daga nan Hafaru bai sake dukawa noma ba, sai ya tashi, suka kwashi 'yan hauyoyinsu, suka iza keyar yaron nan har gida. Da isarsu gida Hafaru ya kama' hannun dansa har wajen kakan.a durkusa, ya gaya wa tsohon abin da yaro ya ce a gona, ya kuma sake durkusawa ya roki tsohonsa gafara, yana ahi da kuka bisa ga abubuwan da ya yi masa. Yaro na kallo, bai san abin da a ke yi ba. Tsohon nan ya ce, "Mhm. Ai duk abin nan da aka yi, ni na ja. Je ká, na gafarta maka duniya da lahira." Hafaru ya tashi yana murna. Daga ran nan bai sake, tozarta ubansa ba, har Allah ya nufa ya cika a hannunsa, suka rabu da alheri. Kullum in Hafaru ya ga dan nan nasa, in ya tuna da maganar da ya yi, sai ya rike baki ya ce, "Ya'yan zamani, saninku ba sanin halinku ba!" Da Musa ya ji aku ya kai karshen wannan labari, ya cе, "Wannan labari naka gargadi ne mai amfani ga wanda ya ji shi." Aku ya се, "Ва wannan kadai ba, duk labarin da na ke 69 bayarwa, in ka lura, ka ga haka ya ke. Ai ba muni ga mutum da ya fi ya kai muddin mutane bai iya bakinsa ba. Ga wani karamin misali nan na kunkuru da gauraki: 70 Fara Koyon Mulki Da Baki, Kafin Ka Koyi Mulki Da Hannu Wata rana wadansu gauraki guda biyu suka gane wani itacen baure a bakin wani rafi. Kullum suka tashi sai su nufi can su hau, su yi ta ci. Gindin bauren nan kuwa ashe akwai wani kunkuru. Kullum idan gaurakin na cin baure, wadansu 'ya'yan su kan kucce musu su fado kasa, Da kunkuru ya ga suna fado masa