← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 31

Sashe 7

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai ya ja wani kakari mai karfi, ya yi shiru. Sauran barayin suka buga salati baki daya, suka ce, "Ya cika." Ko da 'Yan Gadi suka ji haka, ba su tsaya su gama shawarwarinsu ba, sai kowa ya ce in ba ka yi ba ni wuri. Kazunzumi da jin tif tif tif na 'Yan Gadi suna gudu, sai ya tashi ya shiga gaba, sauran na biye har gida. Da zuwa suka sami ruwa mai sanyi, suka kyankyama. Ka san na gaya maka kafin su debi rogon nan sai da suka ci daya daga cikinsu tukuna. Abinka da kayan zalunci, ko da suka sha ruwan nan sai danyen rogon nan da suka ci ya taso, ya murde su, kowane ya yi ta murde-murde abinsa, yana nishi. Kafin asalatu cikunansu suka haye tim, sai amai sai zawo, gari bai waye ba, sai da duka suka hauri arewa. Da safe da aka tarad da su kowane cikin nan ya kumbura kamar salka. Ga su kace-kace cikin amai da zawo. Rogo na fita har ta hanci. Aka duba sako aka ga kwanduna cike da danyen rogo, sai aka hakikance danyen rogo suka yi wa cin yunwa, ya halaka su. Aka yi 'yan koke-koke, aka yi musu jana'iza, aka kare. 20 Garin nan ya faye yawa, 'Yan Gadin nan ba su san wannan abin ya auku ba. Da suka gamu da hantsi sai guda ya ce, "Shin wa ku ke tsammani ya harbi mutumin nan ne na jiya? Ni dai na tabbata ba ni ba ne." Na biyu ya ce, "Balle fa ni da na ke biye da ku daga baya." Na uku ya dubi na fari, ya ce, "Amma ko da ku ke neman ku maka mini laifi, ai ku kuka ce in harba." Na fari ya ce, "I, gaskiya ne, amma ai kai ka san abin da na ke nufi. Ka harba ta ketare kansa, ba ka same shi ba." Na uku ya ce, "Ni ma tsammani na ke koli na harba ta. Ina mamakin yadda ta same shi. Kaddara dai ce ta tarad da ajali kusa." Sauran suka ce, "Gaskiya ne, sai dai mu yi kurum, kada mu tona kammu." Daga'ran nan duk sa'ad da biyu daga cikinsu suka gamu sai su ta da taďin, su rika kokari su lika wa wanda ba ya nan laifin. Suka zauna kan hakanan dari dari har iyakar ransu, suna tsammani a gane su yau, a gane su gobe, ba su ji magana ba. Suna son su tambaya, suna jin tsoron kada son iyawa ta tona su. Musa ya ce, "Wadannan 'Yan Gadi sun kuwa isa sakarkaru." Aku ya ce, "Su ma ai suna da hankali bisa ga wani Bahaushe wanda ya tafi fatauci cikin kasar Yarbawa." Musa ya ce, "Har ya fi wadannan sakarci? Haba, wanda ya fi wadannan sakarci, ai sai yanka." Aku ya ce, "Bari ka ji gogan naka, ka san ko cikin Hausawa akwai Yausawa." 21 Sauna Kira Mana Shashasha, In Ka Ga Sakarai Ku Taho Tare Wata rana wani Bahaushe wai shi Wawa za shi fatauci, sai ya bi ta kasar Yarbawa, Wawa ba ya jin Yarbanci, mutanen da ya tarar a wannan gari su kuma ba su jin Hausa. Amma duk da wannan Wawa bai lura ba. Yana cikin tafiya, ya kawo kofar gari, sai ya ga wani katon garken shanu fari fat suna kiwo. Wawa ya yi mamakin wanda ke da wadannan shanu masu yawa haka, sai ya tambayi wani mutum nan kofa ya gaya masa ko shanun wane ne wadannan. Mutumin ya amsa da Yarbanci, ya ce, "Ni baı ji ba." Wawa da ya ji haka tsammani ya ke "Ni ban ji ba" shi ne mutumin da ke da shanun. Don haka ya ce, "Ni-ban-ji-ba lalle yana da sukuni." Ya wuce ya shiga gari, sai ya kai ga wani babban gida. Ya daga kai, ya ga lalle gidan nan ya amsa sunansa, sai ya ce wa wani yaro da ke nan kofar zidar, "Don Allah, samari, wa ke da wannan babban gida haka?" 22 Yaron ba ya jin Hausa, shi kuma sai ya ce a cikin harshensa "Ni ban ji ba." Da Wawa ya ji haka, sai ya ce, "Kai, ba shakka Ni-ban-ji-ba ba wanda ya fi shi sule garin nan. Wannan irin gida sai ka ce na Sarki. Da ganin wannan ai ko ba a gaya maka ba ka san wurin nan sule ya zauna da gindinsa." Ya haura takalmansa ya wuce faram, faram, faram, faram, har bakin kogin garin. Yana zuwa sai ya tarad da wani jirgi ya zo, ana ta fid da kaya daga cikinsa. Wawa ya dubi kaya, ya ce, "Oi! Wannan jirgi ya yiwo kaya!" Ya dubi wani nan kusa gare shi, ya ce, "Dan'uwa, duk ko kayan nan na mutum guda ne?" Shi Bayarabe bai ji abin da ya ce ba, sai ya dube shi, ya ce, "Ni ban ji ba." Da Wawa ya ji haka sai ya rike baki, ya ce, "Masu gari! Hakika Ni-ban-ji-ba ya huce haushinsa. Ina ma Allah zai sa in gamu da wannan mutum, ko wajen adonsa ma in more ma idona!" Sai ya zauna ya huta, ya debi ruwa ya sha, ya kama hanya zai wuce. Ya kai kofar gari ke nan, sai ya ga wani matacce an dauko shi, za a kai shi a rufe, wadansu na ta kuka. Wawa ya tsaya yana dubansu. Tausayi ya kama shi, ya matsa wajen wata tsohuwa, ya ce mata, "Wane ne wannan ya riga mu gidan gaskiya?" Tsohuwa ba ta ji Hausa ba, sai ta dube shi, ta ce, "Ni ban ji ba."" Wawa da ya ji haka sai ya dafe kai, ya ce, "Allah mai girma! Ka san kowa samun nan na duniya ya ruda, ya shiga uku. Don Allah dubi abin da Ni-ban-ji-ba ya tara. Ga shi yanzu ya zama sai labari, kamar dadai duniya ba a halicce shi ba! Cikin duk abin nan da ya tara, dubi dan kyallen da za a kai shi da shi. Tun da ya ke al'amarin nan haka ya ke, to, ni yanzu me ya ruda ni har da na rabo da gida don rashin wadar zuci? Ga shi Allah bai hana mini abin da zan ci ba. Watau ba dai abin da ya fid da ni gida sai in sami abin alfahari in kara sabo. Mhm, Allah ya kiyashe mu da aikin Shaidan! Na gode Allah da ya kawo ni nan na sami gargadi daga al'amarin Ni-ban-ji-ba. Ba sauran abin da ya fi, sai in koma garimmu, in dangana da abin da Allah ke ba ni wajen 'yar gonata. Da ma an ce, "Gani ga wani ya isa tsoron Allah." Musa ya tashi, har ya bude zauren farko, sai ya ji bayi sun farka. Sai ya kuta, ya koma. Da Waziri ya ga kwana biyu sun wuce, kowace safiya bayin 23 nan da ya sa suka dawo sai su ce ba wanda ya ko leko zauren, har abin ya dame shi, ya ce, "A'a! Da ko na yi tsammanin zai fito, yaya haka! Amma ba kome, kada ku fasa aikinku, na san dabara." Ya kira wata tsohuwar baiwarsa, ya bayyana mata abin da ya ke so duka game da Musa, ya ce mata in ta yi kokarin ta taimake shi har ta sa Musa ya fito waje, zai ba ta fam goma, ya kuma 'yanta ta. Ya kawo sule goma, ya fara ba ta ta lasa. Tsohuwa ta ce, "Ta kwana gidan Sauki." Magariba na yi, sai ta shiga gidan Sarki da kayan talla, ta kaikaici idon mutane ta yahuto Musa waje guda, ta ce, "Mahmudu ya aiko ni, ya ce a gaya maka wai kai haka za ka yarda ka lalace cikin mata? Ya ce a gaya maka fa duniya ba ta auren raggo." Musa ya matsa kusa da tsohuwa, ya ce, "Don Allah iya, yana can yana ta yaki ko?" Tsohuwa ta ce, "Haba! Yanzu sansanimmu akwai wanda a ke magana irin Mahmudu? Ni ma fa can na ke sansani, mu ke yi musu abinci. Mahmudu ya shaku da ni, ya aiko ni gare ka." Musa ya ce, "Koma maza ki gaya masa, gobe in Allah ya so ya gan ni." Tsohuwa ta koma. Da dare ya yi, Musa ya saurara ya ji barci ya kwashe bayin nan, sai ya shigo damaru, ya zo wurin aku, ya ce, "Ka ji Mahmudu na can sansani yana ta abin kirki, ni za ka sa in lalace nan cikin mata." Aku ya ce, "Yallabai, ina ruwana? Ni ban hana ka ba. Yaya barde kamarka zai ce za shi wurin yaki a hana shi? Tun da ya ke niyyarka ka yi abin da zai faranta wa tsohonka rai ne, ai kowane 24 hadari ka shiga Allah ya fisshe ka, yadda ya fid da Auta dan Sarkin noma daga namun jeji." Musa ya ce, "Wane rigima ta kai shi ga fadawa hannun namun jeji?" Aku ya karba: 25 Labarin Auta Dan Sarkin Noma Da Namun Jeji Wata rana wani manomi ya ce wa dansa Auta kullum ya san yadda zai yi ya harbo musu abin da za su yi miya. Auta yа сe. "To." Kowace rana sai ya je daji, yau in ya harbo zomo, gobe ya harbo batsiya ko gada. Kullum haka har ran nan bai samo ba, uban ya yi ta yi masa fada har ya ba shi kashi. Yana cikin haka, ran nan har namomin daji suka gaji da kisa, suka kai kara gun zaki, Sarkinsu. Zaki ya ce, "To, yaya za mu yi? Kun sani fa Allah abin tsoro ne, mutum ma abin tsoro ne." Sai kura ta ce, "Ai, ranka ya dade, babu wata dabara sai mu yi kokari mu kawo maka yaron nan, kai kuwa ka yi abin da ka ga dama da shi." Sauran dabbobi suka ce, "Ai kuwa haka ne, abin da kura ta ce shi ne gaskiya." Suka sallami Sarki, suka watse. Ran nan yaron yana yawon harbi sai ya ci karo da dila ya ja baka zai harbe shi, sai dila ya ce, "Tsaya! Na ce ko abinci ka ke so? Zo in kai ka inda za ka hųta da wahala." Auta yana tsammani gaskiya ne. Ya bi shi, suka mika har wani katon kogo inda zakin nan ya ke mulki. Da
Chapter 7 · 0% Book details