← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 31

Sashe 3

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajen fadanci aka fara 'yan tade-taden duniya, sai ya takalo maganar yaki, ya ce, "Mu dai mun saki jiki da duniya yanzu, ba mu shirin kome." Sarki ya ce, "Me ya kawo wannan magana, Waziri? Muna cikin sulhu haka, me ruwammu da wani shirin mayaka?" Waziri ya ce, "Ai ka san ba a san abin da sauran kasashe ke ciki ba. Gwamma ko mu zauna da shiri, don ba a fafa gora ranar tafiya." Sarki ya ce, "Wane shiri ya fi wanda mu ke da shi yanzu? Ga Sarkin Yaki, ga Barde, ga Madawaki, cikinsu kowane ya yi kukan kura sai a ba shi hanya." Waziri ya ce, "Wadannan ai duk sun tsufa, ga Sarkin Yaki yanzu a kalla ya ba saba'in baya. Wanda ya ke haka, tun da Allah ya nufe shi da samun magaji, ya kamata ya huta. Dabarata sai Mahmudu ya koma gidansu, ubansa ya rika koya masa al'amuran yaki." Musa da ke nan sai ya tsolma baki ya ce, "In dai don a dauke Mahmudu ne, a bar ni ni kadai, ni ban yarda ba, sai dai mu je a koya mana tare." Waziri ya kau da kai ya kuta, ya ce, "Ina ruwanka da koyon yaki, kai da za ka sa a je a yi maka?" Musa ya ce, "Ni dai ban yarda mu rabu ba." Sarki ya ce, "Tun da Musa bai yarda ba, dabararka ba ta yi ba ke nan, Waziri." Waziri ya bata fuska, zai fara wata magana sai ga wani ya zo ya fadi gaban Sarki, ya ce, "Ga Wazirin Sarkin Sinari ya zo da wadansu manyan garinsu, ya ce a yi masa iso." Sarki ya ce ya shigo. Da ya shigo ya yi gaisuwa, ya mika masa takarda. Magatakarda ya karba ya buda, sai ya ga an rubuta: 3 "Takarda ta fito daga Sarkin Muminai, Sarkin Sinari, Abdul'azizi, dan Shaihu Muhtar, zuwa ga masoyinsa amininsa Sarki Abdurrahman, gaisuwa mai yawa, da so, da yarda, da aminci. Amma bayan haka ina so in karfafa zumuntan nan da ke tsakanimmu, saboda haka na ba dana Musu 'yarka Sinaratu, in sun kara girma a yi biki. Sai mu shirya a gama su tun muna da rai. Haza wasalamu.” Da Sarki ya ji abin da takardan nan ke ciki sai ya tashi da fada, ya fizge takarda daga hannun Magatakarda ya kyakke ta. Ya tashi ya kama gemun Wazirin Sinari, ya jefad da shi gefe guda. Sarakunansa suka shiga tsakani, suna "Hucewa mai duniya! Rashin hankali ne na yara." Sarki ya сe, "Ko Musa ya lalace ya auri Sinaratu? Me aka yi aka yi Sarkin Sinari, balle 'yarsa Sinaratu?" Ya dubi mutanensa, ya ce, "Ku yi ta dukansu sai sun bar kasata! Wazirin Sinari ya ruga, ya haye dokinsa, mutanensa suka dafi bayansa. 'Yam birni suka bi su eho, eho. Fada duk ta rude, fadawa suka yi ta duban juna. Liman ya ce, "Allah ya ba ka nasara, abin nan da aka yi, a aika lafiya dai?" Sarki ya ce, "Me ya firgita ka? Don dai mai garin Sinari ko cewa na yi a mare shi, ya yi magana?" Barde ya ce, "Ai Sarkin Sinari yanzu ganin kansa ya ke daidai da kowa. Ban yi tsammanin abin nan da aka yi masa zai kyale ba." Sarki ya ce, "Kai ma ka karai ne, kamar Liman?" Waziri ya ce, "Ba karaya ba ce, ai gaskiya c abin da na ke fadi yanzu na kan ba mu da shirin kome." Mutane suka ce, "Gaskiyarka, Wazir, ga Sarkin Yaki yau 4 kwanansa kamar ashirin ke nan sai a kwantar a tayar, ba shi ko da magaji." Sarki ya kara fusata, ya ce, "Ba shi da magaji? Watau kun shiga maganar tsohon banzan nan? In dai maganar Mahmudu ku ke wa mita, na dauki alkawari, ko bai iya kome ba, duk yakin da ya fara tashi nan gaba, shi zai zama jagaba." Aka gama fadanci aka vatse, suka tafi suna zunden Waziri. Waziri ya koma gida da fushi, ya kama shawarwarin abin da zai yi wa Sarki ya huce haushinsa. Daren nan ya kasa barci, ya kulla wannan ya kwance, har asuba. Da gari ya waye sai ya rubuta takarda zuwa wajen Sarkin Sinari, ya ce, "Kada wani bu ya ba ka tsoro da Sarki Abdurrahman, shirim ne ba inuwa. Muddin ka dauki alkawarin za ka naďa ni Sarkin garin nan, ni ko na san yadda zan yi in taimake ka ka ci kasar. Domin duk mutanen kasar sai abin da na ce musu. Da farko sai ku dauri niyya maza ku zo kafin su shirya. Ku biyo ta kadarkon Kimba, don ta wannan hanyar har ka shigo birni kowa bai sani ba. Ku taho tare da wannan yaro ya nuna muku hanya, domin ko ban da shi nan kasar ba wanda ya san wannan hanya." Sai ya ba wani amintaccen bawansa, wai shi Barakai, ya gaya masa yadda zai yi, ya sallame shi. Sarki Abdurrahman kuwa bai sake komawa ta kan Sarkin Sinari ba. Ana nan ran nan ya sa aka daura wa dawaki sirada, ya hau tare da yaran nan suka tafi shan iska, har suka kai wata fadama, suka sauka suna hutawa, sai ga wani Balarabe dauke da aku cikin keji. Ko da Musa ya daga ido ya gan shi sai ya ce, "Alo, alo, ga aku a saya mana!" Nan da nan wani bawan Sarki da aka je da shi ya kira Balaraben nan, ya tambaye shi kuďin akun. Balarabe ya ce, "In ba jaka guda ba, ba na sayad da shi." Da bawan nan ya ji haka sai ya ce, "A'a! Da Sarkin za ka yi ba'a? Kana tsammani Sarki ya tambaye ka karin magana ce?" Da bawan nan ya fusata Sarki haka, sai ya cika ya ce a kama Balaraben nan. Bayin da aka zo da su suka tasam masa kamar za su cinye shi danye, da shi da tsuntsunsa duka. Da dai tsuntsun nan ya ga haka, sai ya kada fifike, ya се, "Allah ya ba ka nasara, kada ka yi hushi bisa ga gaskiyar ubangijina. Ni ma a jaka gudan nan da ya fadi a ganina ya karya mini daraja ne. Kamata ai bai kamata a sallama ni jaka guda kadai ba." Sai sarki ya ce wa bayi su tsaya. Ya dubi dan tsuntsu, ya ce, "Kai kuwa dan tsuntsun nan mene ne dalilinka na wannan cika baki haka?" 5 Sai aku ya dukad da kai, ya ce, "Akwai kuwa, Allah ya ja zamaninka, takamar da na ke yi ba don saboda kyaun jikina kaďai na ke yi ba, ba ko don saboda dadin bakin nan da Allah ya ba ni ba, amma saboda baiwa wadda Ubangijimmu ya yi mini ta wajen iya duba. Har yanzu ta kai ni fagen ina iya ba da labarin abin da za a yi nan gaba, balle ma a tambaye ni wanda aka yi ya wuce. Kuma a cikin bokanci, sanin da Allah ya ba ni ba shi da iyaka. In kuma labaruruka ka ke son ji, ko na aljannu, ko na barayi, ko na Sarakuna, in ka saye ni in ya so ma kada ka sake batad da kuďinka a banza garin sayen Alfulaila, ko wadansu littattafai na Turawa wadanda ba su da wani labari daga na tafiye-tafiyen gano kasashe, sai fa na tarihe-tarihe da na lissafelissafe, da na kiwace-kiwacen lafiya, masu gundurad da mutane. In kuma karuwa ka ke nema wurin arziki, in ka saye ni bukata ta biya." Sarki ya ce, "Ta wajen suruntun naka na wofi?" Aku ya ce, "Surutu ba abin rainawa ba ne. Magana ai jari ce." Da yaran nan suka ji ya iya ba da labarai, da ma abin da su ke so ke nan, sai suka yi ta tsalle-tsalle suna murna. Sarki ya rike baki yana mamakin wannan tsuntsu. Sarki ya ce wa aku, "Tsaya mene ne na wannan irin fafarniya? Yabon kai jahilci. In kana da hikima, gaya mini yau shekarun Musa nawa?" Sauran mutanen da suka zo tare da Sarki suka fashe da dariya, suka ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara, ka ko kashe mana bakinsa! Ya fadi mu ji, kan ba karya ba." Aku ya dubi Musa, ya ce, "Yau shekarunsa goma sha hudu da wata biyar da kwana uku." Mutane suka ce, "A'a! Ai ko, Allah ya ba ka nasara, gaskiyarsa!" Sarki ya ce, "Kai, ji ya yi wajen wadansu ana fadi. Labarin Musa yanzu ina ne bai kai ba?" Ya sake ce wa aku, "To, mun ji ka rike wannan da ka ji mutane ke fadfi, amma wace rana ce aka haife shi?" Aku ya sake duban Musa, ya ce, "Ranar Jumma'a da la'asar." Sarki ya ce, "A'a! Ai ko gaskiyarsa." Ya dubi aku, ya ce, "Da ya ke kana da hikima, sai ka gaya mini me za: fara aukuwa gare shi?" Aku ya ce, "Ba za ka so ka ji wannan al'amari ba, don zai bata maka rai kwarai. Ya fi kyau a bar kaza cikin gashinta." Sarki dai ya nace sai ya gaya masa, in ya ki kuwa yanzu ya sa a hura wuta a babbaka shi da rai. Da aku ya ga Sarki ya fusata sai ya ce, "a yi mini gafara bisa ga abin nan da zan fadi. Musa zai zama snad.n cuce-cuce, da 6 raunuka, kai har da halakar rayukan mutane kamar dubu na kasan nan. Wannan al'amari kuwa ba da daďewa ba zai auku. Da ma kana ganewa, ka sake shiri tun da wuri." Da Sarki ya ji haka sai ya hasala, don aku ya ce dansa zai zama sanadin mace-mace. Ya dauki kejin ya jefar. Ya tashi zai je ya take dan tsuntsun nan ya mutu. Bayi kuma suka zaburam ma Balarabe, duk wurin ya harmutse. Sai kwaram suka ji kuwwa. Su waiga haka, sai ga wani mai doki sukwane, ya zo ba ko sirdi, duk jikinsa jina-jina, abin ba kyaun gani. Ya fadi gaban Sarki, ya ce, "Wayyo Allah! Wayyo Allah! Ka yi mana agaji! Ai ga Sarkin Sinari can ya shigo kasarka da yaki, 'yan garuruwammu na nan kan iyakar arewa duk sun zama toka. Na rantse har da girmanka, ni kadai na tsere!" Sarki da mutanensa duk suka yi sako, kowa na duban dan'uwansa. Sai kawai daga bayansu suka
Chapter 3 · 0% Book details