Sashe 2
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Magana Jari Ce Littafi Na Farko Magana Jari Ce 1 Yaro Ba Da Kudi A Gaya Maka! Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E., C.O.N. -Kámfanin Littafai Na Nijeriya Ta Arewa ZARIA. Mallaka (M Kamfanin Gaskiya Zaria 1945 Ba a yarda a kwafi wannan Littafi ba, dukkansa ko sashinsa don bugawa ko sa wa a kowace irin na'ura, sai an samu izini a rubuce. An Fara Bugawa 1937, An sake Bugawa Sau 17, daga 1954 - 1985. Gyaran Farko 1993, 1997. 1998 An Shirya a Kamfanin Littafai Na Nijeriya Ta Arewa Lambar Gidan Waya 412, Kamfanin Gaskiya, Zaria. ISBN: 978-169-057-7 An Buga Shi a Kamfanin Gaskiya, Zaria Labarun Da Ke Ciki Gabatarwa Shafi Labarin Sahoro Da Sahorama Magana Jari Ce Labarin Wani Bororo Da Dan Zaki Banza Ta Kori Wofi Sauna Kira Mana Shashasha, In Ka Ga Sakarai Ku Taho Tare Labarin Auta Dan Sarkin Noma Da Naman Jeji Labarin Wani Bakauye Da Wadansu 'Yan Birni 1 13 18 22 26 29 32 Labarin Wani Aku Da Matar Ubangidansa 37 Labarin Sarkin Zairana Da Sarkin Bokaye Gara Labarin Kyanwa Da Bera 40 44 Labarin Wani Jaki Da Sa 49 Yadda Muka Yi Da Ubangijina Ojo 53 In Ajali Ya Yi Kira, Ko Babu Ciwo A Je 57 Labarin Wadansu Abokai Su Uku 61 Munafuncin Dodo, Yakan Ci Mai Shi 65 Abin Da Mutum Ya Shuka Shi Zai Girba, In Hairan Hairan, In Sharran Sharran 68 Fara Koyon Mulki Da Baki, Kafin Ka Koyi Mulki Da Hannu 71 Babban Mugun Abu Gun Da Ya Yi Hushi Da Iyayensa 75 Banza Girman Mahaukaci, Karamin Mai Wayo Ya Fi Shi 79 Labarin Sarkin Busa 62 Kowa Ya Yi Kokarin Ya Sami Fiye Da Abin Da Allah Ya Nufe Shi Da Shi, Ya Ja Wa Kansa Lalacewa Labarin Annabi Sulaimanu Ba Wahalalle Sai Mai Kwadayi Saurin Fushi Shi Ke Kawo Da Na Sani Raina Kama Ka Ga Gayya Labarin Shaihu Mujaddadi Dan Hodiyo Da Umaru Mu'Alkamu Labarin Shaihu Dan Hodiyo Da Madugu Labarin Shaihu Dan Hodiyo Da Wani Malami Sauri Ya Haifi Nawa 88 94 96 99 103 107 110 113 116 GABATARWA Wannan littafi, Magana Jari Ce, 1, yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin zaßo shi kuwa ya rubuta wadannan littattafai shi ne ya shiga wata gasa ta rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko 'Ruwan Bagaja'. An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin Kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta 'Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen kaga labari mai ma'ana ya sa Dr. R. M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya. Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta wasu littattafan. A can ya rubuta 'Karamin Sani kukumi' cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar farko ta Arewa. Shi ne ma ya rada mata suna 'Gaskiya Ta Fi Kwabo' aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939. Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin 'Yakin Duniya Na Biyu' watau 'Yakin Hitila' da ya ba suna 'Tafiya Mabudin Ilmi'. Wannan littafi ya ba da labarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa ta Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943. Wani mashahurin littafi kuma da ya rubuta shi ne 'Tarihin Annabi da na Halifofi' wanda aka fara buga shi a shekara 1957 lokacin nan yana shugaban Hukumar Daukar Ma'aikata ta Nijeriya ta Arewa. Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka fara nadawa Kwamishinan Jin Kararakin Jama'a a shekara 1974 a Jihar Kaduna, lokacin ana kiranta Arewa ta Tsakiya. Ya rasu yana da shekara 70 a duniya ranar Juma'a 19 ga watan Yuni, 1981. Alhaji Abubakar Imam ya rika cewa wannan aiki da ya yi, na talifin 'Magana Jari Ce' ya yi masa amfani ainun. Ya kan ce wannan aiki shi ne ya ba shi damar zama tare da mashahurin Baturen nan na talifin Hausa, Dr. R. M. East, O.B.E. Ya ce daga gare shi. ne ya koyi duk dan abin da ya koya na game da talifi. Abin mamaki, shi kuma wannan Bature, Dr. East O.B.E., a wajen 'Mukaddamar' da ya yi da Turanci tun farkon buga 'Magana Jari Ce', ga abin da ya ce: 'Muna godiya ga En'e ta Katsina, saboda taimakonsu, da hangen nesa da suka yi, har suka yarda, suka ba mu aron Malam Abubakar Imam. Suka yarda, ya bar aikinsa, na koyad da Turanci a Midil ta Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi wata shida domin ya taimake mu, mu sami wadannan littattafai a cikin harshensa. 'Iyakar abin da mu ma'aikatan wannan ofis muka yi, na game da talifin wadannan littattafai, shi ne aiki irin na ofis, na shirya al'amuran, yadda suka kai har aka buga su. Ban da wannan sai kuma taimakonsa da muka yi na tattara masa littattafai iri iri, don ko zai kwaikwayi wani samfur. Sai fa,kuma wajen shiryawa bayan da ya rubuta. 'Kai, in dai'har muna da wani abin da za mu yi kirari mun yi, game da talifin wadannan littattafai, to, babban abin kirarimmu kawai, shi ne yadda muka yi har muka binciko wannan malamin talifi'. 1982 N.N.P.C. Magana Jari Ce A wani gari a kasashen gabas an yi wani babban Sarki wanda a ke kira Abdurrahman dan Alhaji. Rabonka da samun ko labarin mai arziki irinsa tun Dankaruna, mutum ko gidansa ya shiga ya ga yadda aka kawata shi, ya ga kuma irin kayayyakin da ke ciki, sai ya rike baki kawai, don abin ya fi gaban mamaki. Zaurukan gidan nan kuwa-kai! In ma mutum ya ce zai tsaya ya bayyana arzikin Sarki Abdurrahman ga wadanda ba su san abin da a ke kira duniya ba, sai su yi tsammani shara ta yake yi. Amma duk yawan arzikin Sarkin nan sai ya zama na banza, don ba shi da 'ya'ya, ba shi da kane, ba shi da wa. 'Ya daya kadai gare shi, an ko yi mata aure, Saboda haka Sarkin nan ya zama ba wani wanda zai gani ransa ya yi fari cikin fadan nan tasa duka. Ya ga in ya mutu duk dukiyan nan sai a raba a ba matarsa da 'yarsa kadai, abin da ya rage a sa baitulmali. Kuma sarautarsa sai wanda Allah ya ba ya ci. In ya tuna da wannan, duk sai ni'imomin duniyan nan da Allah ya ba shi su yi masa baki kirin. Ana nan ran nan sai 'yan nan tasa ta haifi da namiji, aka yi shagali, aka sa wa yaron Maiımudu. To, amma ko da ya ke Sarki ya yi murna kwarai da ya sami jika, duk da haka murnarsa ragaggiya ce domin dan mace ba ya gado, balle har a ce ya yi sarautaа. Yana nan cikin wannan bakin ciki, sai ran nan wani shaihun malami ya zo ya ce masa, "Na yi mafarki jiya, an gaya mini da za ka tara malamai arba'in su yi ta yi maka addu'a har kwana arba'in, in Allah ya so za ka haihu." Sarki ya yi murna da wannan mafarki, ya dauko kudi da riguna zai ba malamin nan. Malamin ya ce shi ba kuďi suka kawo shi ba, ya zo ne ya isad da umurni, ya yi sallàma, ya tafi. Ranar ba ta sake juyowa ba sai da Sarki ya sa aka tara masa 1 manyan malamai guda arba'in na kasarsa, ya gaya musu abin da ya ke so. Suka ce, "To, Allah ya karbi rokonmu!" Mutane suka ce amin. Suka yi shiri, suka shiga masallaci, suka duka. Ubangiji ya nufe su da katari, ya karbi rokonsu. Kwanan nan arba'in ba su cika ba sai da matar Sarki ta sami ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji, wanda kyaunsa ba shi da iyaka. Shagalin da aka yi cikin kasan nan, da farin cikin Sarki bisa ga wannan al'amari, ku da kanku kun san ba shi yiwuwa a bayyana shi cikin wannan dan karamin littafi. Aka dai, rada wa yaron nan suna Musa. Watau tsakaninsu da jikan Sarki abin bai ko yi shekara ba. Sarki kuwa ya dauki ransa ya kallafa bisa kan yaron nan. A ma tsaya a kwantanta son da Sarki ke wa dan nan nasa, abin ya zama kauyanci ke nan. Kwanci tashi, bayan shekara biyu aka yaye yaron. Sarki kuma ya aika aka kawo jikan nan nasa Mahmudu, aka yaye su gaba daya, don su rika wasa tare. Suka tashi sai ka ce tagwaye, ba abin da ke raba su. Da duk abin nan burin Waziri, tun da Sarkin nan ba shi da da namiji, in ya mutu shi ya ci sarauta. Yana alla-alla Sarki ya mutu bai haihu ba, sai Allah ya kaddara haihuwar wannan yaro. Tun ran da Waziri ya ji gudar haihuwar Musa, zuciyarsa ta yi baki kirin, daga ran nan ya zama ko mai suna Musa ba ya so ya gani, ya shiga kulle-kulle kullum na yadda zai yi ya kashe Musa, ko kuwa ya sa ya bi uwa duniya, abin ya gagara. Har yara suka yi kamar shekara goma sha biyar biyar, ko ina Sarkin nan za shi da su ya ke zuwa. Ana nan ran nan, ina ya Allah babu ya Allah sai Waziri ya sami wata dabara, ya ce a ransa, 'Alhamdu lillahi, ko-da-ya-ke ba yadda za a yi in sami Musa wani wuri shi kadai ba tare da Sarki ba, balle in san abin da zan yi masa, ai in na yi kokarin da na raba Musa da Mahmudu, kome ya yi kyau. Domin yadda suka shaku haka, lalle in aka raba su hankalin Musa zai tashi, ta wannan hanya zan san yadda 2 zan yi in sa shi ya sulale da dare ya bi dan'uwansa." Sai ya yi dariya, ya buga kafa a kasa. Kashegari, ko da ya tafi