Sashe 23
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya yiwo shiri ya dawo, ya се wa Musa, "Zan sake kwana nan gunka, yau lalle mu fita. Suka zauna suka yi ta hira. Da suka ji bayin nan sun yi shiru suka iske aku, Musa ya ce, "Zan tafi, ga shi har na sami 'yar rakiya kuma."" Aku ya duba ta taga sai ya ga hadari ya taso, yaşce wa Musa, "Haba, ko kuna hauka kwa fita yanzu cikin wannan ruwa?" Barakai ya ce, "Ai ba a fara ruwa ba, ma tafi hakanan." Aku ya yi ta jansu da 'yan tade-tade, har ruwa ya goce. Suka zauna suna jira a dauke. Aku ya dube su, ya ce, "Da zaman banza bari in gaya maku dan labari." Musa ya dubi Barakai, ya ce, "Ai ko kin san gaskiyarsa, ya fada mana dan gajere." 'Barakai ya сe, "Kуale shi, ba mu so. Kullum sai ka rika tsai da shi a kan surutun wofi, kai ba hadisi ka ke masa ba, kai ba labaran Annabawa ka ke gaya masa ba, balle a san kara shi ka ke yi." 92 Aku ya ce, "Abin da ya sa ba na ba da labaran Annabawa, tsoron jahilai na ke. Kun san yanzu akwai mutane da yawa wadanda su ba malamai ba na sosai, amma da sun ji mutum ya yi wata 'yar magana game da irin wadannan, sai ka ga suna neman daukar kafarsa, wai ya yi sabo. Amma fa im ba don gudun haka ba, labarin Annabawa, tun daga Annabi Adamu-tsira da aminci su tabbata a gare shi-har zuwa ga Shugaban Ma'aika, akwai wanda ban sani ba?" Musa ya ce, "To, in haka ne fara gaya mana labarin Annabi Sulaimanu, wanda aka ce ya mallaki mutane da aljannu har da tsuntsaye." Aku ya ce, "Wannan ai sananne ne har yanzu ba ka ji shi ba?" Musa ya ce, "I, na ji cikin dukan mutanen duniya babu wanda ya fi shi arziki." Aku ya ce, "Ai wannan daga baya ne. Domin sa'ad da aka nufe shi da annabci aka ce ya zabi dukan abin da ya kę so a ba shi. Shi ko ya ce tun da ya ke an ba shi mulkin jama'ar Allah, shi ba abin da ya fi so sai hikima, don ya san yadda zai rike su a kan adalci. To, tun da ya zabi wannan bai zabi dukiya ba, ko tsawon rai, ko girman duniya, Ubangiji ya ba shi hikima fiye da dukan sauran mutanen zamaninsa, ya kuma kara masa har da abubuwan nan da bai roka ba." Musa ya ce, "Haba, tun da na ke ban taba samun wanda ya bayyana mini asalin wannan al'amari ba, sai fa kai yau." Aku ya ce, "Ko labarin yadda ya yi hukunci tsakanin wadansu mata biyu ba ka taba ji ba?" Musa ya ce, "Wallahi ban taba ji ba. Wane irin hukunci ya yi?" Aku ya matso kusa da Musa, ya kishingida a bisa hannun rigarsa, ya fara: 93 Labarin Annabi Sulaimanu Wata rana Annabi Sulaimanu-tsira da aminci su tabbata gare shi-yana zaune, sai wadansu mata su biyu suka zo suka kawo kara a gabansa. Guda ta ce, "Ya Annabin Allah, da ni da wannan mace gida daya mu ke zaune. Na haifi da. Ana nan, bayan na haihu da kwana uku wannan mace kuma ta haihu. To, duk gidan ba kowa sai mu biyu kadai. Ran nan cikin dare ta kwanta bisa danta ba ta sani ba, har ya mutu. Sai ta tashi da tsakad daren, ta dauki dana ta mayar wajenta, ta dauko danta mataccen ta kawo gabana, ni ko duk ban sani ba. Sa'ad da na tashi da safe garin in ba dana mama sai na gan shi matacce. Da na duba da kyau, sai na ga ashe ba dana ba ne. Na gaya mata haka, ta ce karya na ke yi, maiaccen ne dana. Muka yi ta gardama. Da muka ga abin zai kaї ga barna, muka zo gare ka ka raba mana gardama, ya Shugaba." Waccan kuma ta ce, "A'a, karya ta ke yi, ya Shugabammu. Ni na riga ta haihuwa da kwana biyu, ran nan da dare ta taka nata ya muťu, ta zo ta musanya shi da nawa." Jama'ar da ke nan suka ce, "Kai, wannan shari'a ai ba ta warwaruwa, sai gobe ga Allah." Da Annabi Sulaimanu ya ji maganar matan nan sai ya sa aka dauko takobi aka zare, ya ce, "Tun da ya ke abin ya rikice haka, abu daya kadai za a yi a raba gardaman nan. Zan raba dan nan biyu ko wacenku ta dauki rabi, kowa ya huta, ku dangana har Allah ya sake ba ku wadansu." Da mace daya ta ji haka sai ta ce, "Don Allah kada a kashe shi. A ba ta, na yarda mata." Amma waccan ta ce, "A'a, daidai ne, ya Annabi. A dai raba shi, kowa ya huta." Da Annabi Sulaimanu ya ji haka sai ya ce, "Ku mika dan nan mai rai ga waccan da ta ce kada a kashe shi. Danta ne, ita ta haife shi."" Da Musa ya ji aku ya yi shiru sai ya ce, "A'a! Yaya aka san wannan ke da da?" Aku ya ce, "Haba, ba ka ga abin da a ke nufi ba? In da waccan ta haife shi ta ce a kashe shi tana kallo kiri-kiri?" Bai'tsaya su 94 Musa su sami damar fadin wani abu ba, sai ya ce, "Kafin ku kare tunanin wannan, tsaya ku ji yadda wani Sarki ya yi nasa hukuncin." 95 Ba Wahalalle Sai Mai Kwadayi Da aka yi wani Sarki mai son nishaďi. Ana nan wata rana zuciyarsa ta yi baki kirin, har ya kasa barci. Ya kira yaronsa ya ce masa, "Maza ka tafi wurin Waziri, ka ce ina kiransa." Yaro ya tafi ya gaya wa Waziri, suka zo tare, suka shiga wurin Sarki. Da suka shiga Sarki ya ce wa Waziri, "Yau zuciyata ta baci, har barci ya gagare ni. Ina so mu tafi mu zaga rafi, ko zuciyata ta yi sanyi." Waziri ya ce, "To, shi ya fi, ranka ya dade." Da fad'in haka sai yaron ya yi dariya. Sarki ya ce, "A'a! Mene ne? Ni ka ke wa dariya ko Waziri?" Ya ce, "Ranka ya dade, wane ni in yi maka dariya? Wani abu ne ya fado mini a rai wanda na gani jiya, shi na ke dariya." Sarki ya ce, "Wane irin abu ne?" Yaro ya се, "Ranka ya dade, jiya ina yawo a bakin kogi sai na iske wani mutum, mutane sun kewaye shi, yana ta ba su dariya." Sarki ya ce, "Maza ka tafi ka kirawo shi, ya zo ya yi mini abin da zai ba ni dariya, ko na samu zuciyata ta huce." Yaro ya tafi wurin mutumin, ya ce, "Sarki yana nemanka." Sai mutumin ya ce, "To, da kyau. Me ya sa Sarki ya ke kirana?"" Yaron ya ce, "Yau Sarki yana bakin ciki, yana so ka zo ka ba shi dariya, don zuciyarsa ta yi fari." Sai mutumin ya ce, "Mu je." Yaro ya ce, "To, sai mu yi sharadi, abin da Sarki ya ba ka duka a kasa shi uku, kai ka kwashi kashi daya, ni in kwashi kashi biyu. In ka yarda da haka zan kai ka, in ba ka yarda ba, yi zamanka, ni kuwa in koma in ce ba:ı gan ka ba." Sai ya ce, "To, shi ke nan, na yarda. Mu tafi." Yaro ya kai shi wurin Sarki, ya fita. Sarki ya ce wa mutumin, "Ina so ka yi mini abin da zai sa in yi dariya. In na yi, in yi maka kyauta, in ban yi ba in yi maka bulala." Mutumin ya yi ta yin abubuwa masu ban dariya, da labaru iri iri, har ya gaji. Sarki bai yi dariya ba. 96 Sarki ya ce, "Shi ke nan, ko akwai saura?" Mutumin ya ce, "Shi ke nan." Sarki ya ce, "Ga shi ban yi dariya ba. Kwanta in yi maka bulala." Mutumin ya matso, ya kwanta. Sarki ya tsala masa bulala da karfi. Sai ya yi ta kururuwa, ya ce, "Tsaya, ranka ya dade! Na karbi rabona, saura na yaronka. Domin mun sharada kome na samu in dauki kashi daya, shi kuwa biyu." Sarki ya kira yaronsa, ya ce, "Na ba wannan mutum rabonsa, sauran naka, matso kusa ka karba." Yaro ya matso kusa, yana tsammani zai sami kudi. Sarki ya tsala masa bulala da iyakacin karfinsa. Yaro ya kwala ihu. Sarki ya ce, "Tukuna, ai kashi daya kadai ka samu, saura daya." Yaro ya ce, "Ranka ya dade, kashi dayan nan ma ya ishe ni, na bar maka dayan." Da Sarki ya ji haka sai ya fashe da dariya, bakin cikinsa ya yaye. Ya kawo kyauta ya ba su, ya sallame su. Kafin aku ya kare wannan labari gari ya waye Barakai ya koma yana cizon hannu, yana neman hujjar da zai fada wa ubangidansa. Da zuwansa Waziri ya harare shi, ya ce, "Ban ji an gama aikin ba. Ina dalili?" Barakai ya ce, "Ruwa!" Waziri ya ce, "Ruwa? Wane iri? Ruwa da aka yi aka dauke tun kafin a yi kiran sallar fari?"" Barakai ya ce, "Watakila nan wajen gidanka aka dauke da wuri, wajen fada har rana ta fito ana ruwa." Waziri ya cika, ya kawo iya wuya, ya zabura ya danne shi ya shake, ya ce, "Fada mini gaskiya, in ba haka ba ko yanzu in kashe ka, mutumin banza, munafuki! Lalle kai ne ka tona asirin da muka kulla da Sarkin Sinari. Da ma ina shakkar haka." Da Barakai ya ji haka sai jikinsa ya dauki rawa, ya ce, "Na tuba Allah ya ba ka nasara, gaskiya zan gaya maka yanzu. Akun nan sihiri gare shi, in ya fara ba da labari, sai duk hankalin mutum ya rude, ya rasa abin da ya je yi. Muddin akun nan na numfashi ba yadda za a yi a fid da Musa daga gidan nan, ko kai ka je da kanka." Waziri ya ce, "Rufa mana baki nan da karyar banza!" Ya dauki bulala ya tsala masa har ya gudu. Waziri ya koma ya zauna, yana ciccika shi kadai, yana cewa, 97 "Ina Wazirin kasan nan duk tsawonta da fadinta, ga shi dan abu kadan ya rage da zan yi