← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 31

Sashe 29

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aku ya ce, "Duk wadanda a ke aikowa, ko ina suka shiga, in na gan su na gane su. Bari in kewaya wajen gidan Waziri in na ga daya daga cikinsu a kira shi ya zo, in an matsa masa ya fadi abin da suka yi niyya. Da zan sami ganin wata tsohuwa da ta fara zuwa, da ta fi bayyana abin sosai." Sai wani bawa ya sa shi a wuya, suka yi ta yawo unguwar Waziri, da wadansu katta uku kuma suna biye. Suna kawowa kofar wata 'yar rusasshiyar bukka, sai aku ya leka cikin bukkar, ya ce, "Ga ta!" Kattan nan da ke biye suka kutsa kai ciki, suka jawo ta, suka iza keyarta har gaban Sarki. Da Musa ya gan ta ya ce, "I, lalle ko ita ce, wannan aku abin nasa sai a yi shiru." Sarki ya tambaye ta abin da Waziri ya tashi kullawa game da Musa. Tsohuwa ta gigice, ta ce, "Iye, na'am! Allah ya ba ka nasara, wallahi tilasta ni ya yi." Mahmudu ya mike, ya dube ta ya kashe ta da mari, ya cе, "Sarki ke tambayarki, ki gaya masa abin da aka tilasta ki yi." Tsohuwa ta durkusa, ta fede wa Sarki biri har wutsiya. Da Sarki ya ji haka sai ya aika duk dogarawansa suka zo ya ce, "Ku jeku kamo mini Waziri!" Dogarawa suka ruga. To, ashe tun sa'ad da aka kama tsohuwań nan wani ya tafi wurin Waziri, ya ce, "Ranka ya dade, na ga wadansu bayin Sarki guda uku da wani aku sun zo sun kama tsohuwar baiwarka ta nan bayan gida, ko lafiya?" 121 Da Waziri ya ji haka, sai ya ce, "Lafiya mana." Bai sake wata magana ba, sai ya shiga gida, ya sa aka daura masa sirdi, ko rawani bai tsaya nema ba, balle bara. Sai ya hau, ya sulale ta bayan gida ya fita gari, ba wanda ya gan shi. Da dogarwa suka zo, suka fada cikin gida suka tarad da Jakadiya, suka ce, "Ina Waziri?" Jakadiya ta ce, "Lafiya, har cikin gida ba sallama?" Dogarawa suka iza ta, suka ce, "Je ki, ki yi mana iso." Jakadiya ta shiga cikin gida. Jim kadan ta fito, ta ce, "Ai ba ya nan." Dogarawa suna tsammani karya ta ke yi suka bazu cikin gida, wadansu suka tsare kofar zaure. Da suka yi nema ba su same shi ba, suka kama duk bayin gidan suka kai wa Sarki, suka ce ba su ga Waziri ba. Sarki ya ce, "Ya gudu ne." Ya sa 'Yan Doka su hau su bazu ko'ina, duk inda suka same shi su kamo shi. Aku ya dubi bayin nan na Waziri da aka zo da su, ya се, "Ranka ya dade, ga ko shaidu da suka san abin da aka yi." Sarki ya ce, "Ka san su?" Aku ya ce, "Na san bakwai daga cikinsu, har ma ga wanda aka aika gun Sarkin Sinari." Sarki ya ce, "To, nuna mini su." Aku ya tashi ya ce wa wani dogari, "Da wannan da wannan, kai su nan. Wadannan, ku ku komo nan. Kai, wancan da ke noke kai, komo cikin wadannan." Ya dubi Sarki, ya ce, "Ga su. Wadannan, su aka ce su boye nan kofar gida in Musa ya fito su kashe shi. Wadannan, su suka wo shirin mata suka zo shekaranjiya, daren da za ka dawo. Wannan ko," (ya nuna Barakai) "shi ne babban munafukin, shi aka fara aika wurin. Sarkin Sinari ya nuna musu hanya. Shi kuma ne ya, shigo cikin gida bayan tsohuwan nan." Da bayin nan suka ji haka sai suka dauka. "Wallahi, karya ya ke yi. Allah ya ba ka nasara, mun rantse har da rawaninka ba mu taba shigowa nan ba." Sarki ya dubi dogarawa, ya ce, "Ku tambaye su." Dogarawa suka same su da duka, suna ihu. Sai Barakai ya се, "Ni zan fadi gaskiya, na sai da raina don ubangijina ya yaba, ban sami kome ba sai duka, nan kuma in zo haka?" Sai ya kwashe duk al'amarin ya gaya wa Sarki. Sauran da suka ga ba dama, su ma suka faďi gaskiya. Sarki ya sa aka daure su cikin gidansa. Aka kwana biyu, rana ta uku da azahar sai ga 'Yan Doka sun zo da Waziri, sun kamo shi can kan iyaka, ya kusa ketare kasa, ya nufi Sinari. Da aka zaunad da shi gaban Sarki, sai ya bata fuska, ya tashi da fada ya dubi Sarki yana cewa, "Na mene ne za a aika 122 'Yan Doka su kama ni, ban ci kayan kowa ba?" Sarki ya tashi da mamaki, yana tafa hannu yana cewa, "A'a! Ashe kamo ka suka yi?" Waziri ya harari 'Yan Doka, ya ce, "Kamo ni suka yi mana." Sarki ya ce, "Ni ban ce su kamo ka ba, cewa na yi su kira ka, in ji ko lafiya, don tun shekaranjiya waccan rabona da ganinka. Da Waziri ya ji maganar lumana sai ya ce a ransa, "A'a! Ashe da ma asirina bai tonu ba na ke son tona kaina a wofi. Da ma na san Sarkin nan gabo ne, ba ya gane kome. Kuma ko ma ba wawa ba ne, irin makircina ai ba mutum duka zai gane shi ba." Sai ya ce, "Af, ashe Shamakina bai gaya maka ba?" Ai na tafi ganin wata goggona ce da aka aiko mini ba ta lafiya. Amma dai, Allah ya ba ka nasara, 'Yan Dokan nan sun karya mini irli." Sarki ya ce, "Sai ka yi hakuri da su. Da ma ina gaya maka sakarkaru ne, kai ke cewa suna da kirki." Waziri ya harari 'Yan Doka, ya ce, "Na rantse har da girmanka, ba na iya yafe musu, tun da suka ci zarafina haka. Su duk sai a daure su yanzu. Ko mahaukaci ai ya san abin da ya kamata. Sarki ya ce, "Ai kai ne da mulki, sai ka yi abin da ka ga dama da su. Amma bari in tambaye ka abin da ya sa na kira ka tukun. Tun da na dawo ban sami damar tambayarka wani abu ba game da gidana da na bar maka amana." Waziri ya ce a ransa. "A'a! Ka ji tsohon banza da wata irin tambaya." Sai ya dube shi, ya ce, "Ka tarad da wani abin tashin hankali ne? Ai ni ban yi wasa da gidan nan ba, da kaina na ke fitowa da tsakad dare in kewaya." Sarki ya ce, "Na san haka. Amma wadansu takardu ne aku ya nuna mini wadanda ban gane kansu ba." Ya dubi aku, ya се, "Je ka, kawo su." Aku ya tashi ya kawo su, ya zube gaban Sarki. Da Waziri ya ga takardun nan, sai cikinsa ya ba da kulululu. Ya dauke su yana budawa, yana dariya, yana cewa, "Wani ne ke kwaikwayon hannuna. In ka bibiya ma shegen akun nan ne. Amma, Allah ya ba ka nasara, ya kamata a tsawata masa, in zai yi wasa, ya rika yi da tsarar-rakinsa su ungulu da jemage!" Ya fashe da dariya, wai shi gwanin ba'a. Ya daga kai ya dubi Sarki, ya ga shi bai yi dariya ba. Ya dubi Musa, ya ga shi ma hakanan. Ya juya ga Mahmudu, ya ga kowa kinne. Aku ko ma, sai wasansa ya ke yi da kwayar gyada, kamar bai ko ji abin da a ke fadi ba. Sai idonsa ya raina fata. Sarki ya dubi Sarkin Dogarai, ya ce, "A zo da mutanen nan." Dogarawa suka duru da gudu cikin gidan Sarki, suka fito da 123 bayin nan na Waziri, kowanensu an bankare shi. Da Waziri ya gan su sai gabansa ya fadi. Ya gyara zama, ya duba gabas ya duba yamma, ya ga kowa ya kura masa ido. Sarki ya dube shi, ya ce, "Ka san wadannan?" Waziri ya ce, "Allah ya ba ka nasara, na tuba, na bi Allah, na bi ka!" Sarki ya ce, "Me ka yi mini na tuba? Cewa na yi ka san su?" Waziri ya ce, "Ka ji kaina, ka yafe ni, ba don halina ba!" Mutanen gari da aka tara suka yi ta duban Waziri, ba su san abin da a ke ciki ba. Mahmudu ya tashi, ya kashe Waziri da mari, ya ce, "Sarki ke tambayarka, ka san su, ka dame shi da magiyar banza!" Waziri ya dubi Barakai, ya ce, "Kai ne amintaccen bawana, don Allah bayyana musu sosai, su san ba ni da laifi cikin wannan al'amarin." Barakai уa сe, "A'a! Ba ka da laifi? To, wa ke da shi?" Makirin banza!" Ya gusa gaba, ya daga murya ya fadi duk makirce-makircen da Waziri ya kulla game da Sarkin Sinari, da game da Musa, bai rage kome ba. Da mutane suka ji haka sai suka yi salati, suka taso wa Waziri gaba daya kamar za su cinye shi danye, sai da dogarawa suka shiga tsakani. Sarki ya ce musu, "Ku dakata tukuna, ai ba a kare ba." Shi kuma ya kwashe labarin yadda aku ne ya yi ta kokari ya kubutad da su daga zama bayin Sarkin Sinari. Ya kuma gaya musu yadda ya hana Musa ya fita waje, don ya gane abin da Waziri ke kullawa. Da mutane suka ji haka sai ya ga kowanensu ya yi ta tafa hannu, suka dubi aku, suka dubi Waziri. Sai suka fara dibar kura za su yi masa ature, sai da Sarki ya tsawata. Da suka dakata ya sake dubansu, ya ce, "To, jama'a, ku dubi laifin nan na Waziri. Wanda ya aikata haka me ya kamata a yi masa?"" Jama'a suka dauka gaba daya, "Sai a tsire shi! Da shi ai halaka mu ya tashi yi, don Allah ya ki nufinsa. Da ma ba mai kaunarsa garin, don mugun halinsa." Sarki ya ce, "Na ji tasa. To, wadannan mutanen ko fa?" Jama'a suka ce, "Su ma sai a tsire su, abin da ya ci Doma ai ba ya barin Awai." Musa ya ce, "A'a, tun da dai Allah ya ki aniyarsu, ya gama fuskokimmu da Mahmudu lafiya, ga shi kuma Sarki ya ciwo nasara, sai a yafe su." Sarki ya ce, "Gaskiya ne, Musa. A kwance su." Aka sake su, suka zo suka fadi gaban Sarki suka yi godiya, don da sun tabbata 124 za a kashe su. Mutane suka yi mamakin Sarki a
Chapter 29 · 0% Book details