← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 31

Sashe 28

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta tsawaita shi: Dan Sarkin nan ya ta da kai, ya dube ta tun daga kasa har sama, sai ya ce a ransa, "An ce dan Adam duk bai cika goma ba, to, yau ga wadda ta kai goma sha biyu." Ya kara dubanta ya ce, "Yam mata, daga ina?" Ta ce, "Daga Waila Fadama. Mun zo biki ne nan jiya, yanzu kuwa da azaharin nan za mu koma." Dan Sarki ya yi mamaki, ya ce, "A Waila Fadama? Wane gida ki ke kuwa har ban sani ba?" Ta ce, "Nan gidan mai garin. Ai ni ce babbar 'yarsa. Ba na fita ne, daga biki sai salla, shi ya sa ba ka san ni ba. Amma ka ga, ni kuwa na san ka. Ko kai ma ba ka rasa jin labarin Nana Yauki ta Waila Fadama ba." Dan Sarki ya yi shiru, ya ce, "Wallahi kuwa, na ji ana labarinta." Та се, "To, ai ni ce." Da dan Sarkin ya ji haka sai ya takale ta da maganar aure, ya ga alamar lalle tana sonsa. Wancan mijin da za a ba ta wai dattijo ne mai gemu, ita kuwa ta ce ba ta auren mai gemu. Bayan sun shirya da ita a nan sai ta tafi. Ya dauki buta a masallaci ya yi alwala, ya shiga ya yi salla. Da yai sallama, ya yi addu'a ga Fiyayyen taliki ya nufa Allah ya sa ya auri wannan yarinya. Don dokin bukatar auren yarinyan nan har ya yi subul da baka ya ce wai in Allah ya nufa ya aure ta ya kashe kansa don murna. Bayan ya fito daga masallaci sai ya tarad da mai garin ya kawo masa sauka. Suka gaisa, ya hau, suka mika da baransa. Suka bi Sarki har suka iske su. Yana tafe yana ba baran nan labarin yarinyar. Da aka kare kewayar kasa aka koma gida. Sai dan Sarkin nan ya gaya wa Wazari yana son su neman masa 'yar Sarkin Waila Fadama da aure. Waziri ya gaya wa Sarki. Aka neman masa, aka ba shi. Aka yi biki aka kare. Bayan sun yi kamar shekara uku da auren, sai ran nan Nana ca ce tana son mijin ya raka ta ta gano gida. Dan Sarki ya gaya wa ubansa, uban ya yarda. Ya sa wani babban bawansa ya raka su, aka yi musu shiri, suka hau rakuma suka tafi. Suna cikin tafiya har suka kai garin da dan Sarkin ya fara ganin Nana, suka yi zancen aure, suka tsaya kusa da masallacin, don ya 117 yi alwala ya yi sallar azahar. Ko da ya shiga ya gama salla zai fara tasbaha, sai ya ji kamar daga bisa an ce masa, "Ina alkawarin da ka dauka, da ka ce in Allah ya nufa ka auri Nana za ka kashe kanka don murna da godiya ga Ubangiji?" Da dan Sarki ya ji haka, sai ya tuna da alkawarin nan da ya yi. Ya duba gabas, ya duba yamma, bai ga mai magana da shi ba, sai jikinša ya dauki rawa, ya yi salati, ya ce, "Lalle baki shi kan yanka wuya!" Sai ya zare takobi, nan ya fille kansa. Ya fadi ya mutu. Da aku ya kawo nan sai suka ji assalatu. Wani daga cikin bayin Waziri ya yi maza ya sake zuwa ya durkusa gaban Musa, ya ce, "Ana kiranka maza maza ciki." Musa ya ce, "Haba, su sai su dami mutum da kira. Ina kika ga zan iya tashi ban ji karshen wannan labari mai dadi ba? In wani abu a ke so, Sarkin Gida, je ka ka gani." Da bawan nan ya ga Sarkin Gida zai biyo shi sai ya ce, "A'a zauna abinka, Sarkin Gida, shi a ke nema. In ba ya zuwa, bari in je in gaya musu." Sai ya koma ya gaya wa 'yan'uwansa, suka yi waje da sauri, suna wa juna barka da Sarkin Gida bai biyo ba, da yau sun bakunci lahira. Suka tafi suka gaya wa Waziri abin da ya faru. Waziri ya ce ku koma su sake kokari, zai kara musu fam goma goma. Suka sake shiga irin ta maza, suka komo. Duk gari an tashi, har rana ta kunno, aku kuwa sai jan labarinsa, ya ke yi: Da Nana ta ga ya dade bai fito ba, sai ta ce wa bawan nan ya shiga ya gani wane irin dogon wurdi ya kama, har yanzu bai gama ba. Da shigarsa sai ya tarad da shi kwance male-male cikin jini, ba kai, ga tokobi can gefe yashe. Ya dafe kai, ya yi salati, ya се, "Yanzu in na fita na fadi abin da ya faru, lalle za a ce ni na kashe shi, Ban ga wata hanya ba sai in kashe kaina nan tare da shi, in an ga haka a san lalle sai da na yi kokarina har na kasa, abin ya faru haka." Sai ya dauki takobin nan ya fille kansa. Ya fadi gefe daya ya mutu. Nana tana waje tana jira. Shiru shiru, ba ta ga wani ya fito ba, ta ce, "Kai, yau fa ga inda na yi ma'aikin kibiya. Abin nan lafiya dai?" Ta kara hakuri dai har la'asar ta yi sakaliya, sa'an nan ta cе, "Ko da mata ba sa shiga masallaci, lalle ni in je in ga abin da ya auku." Sai ta sauka, ta kutsa kai cikin masallaci. Da shigarta sai ta ga mijinta da bawansa duk ba kawuna. Ta ja da baya, ta yi nan ta yi 118 nan, ta fadi ta yi ta kuka. Da ta ga dai kuka ba ya magani, sai ta dauki takobi, ta ce, "Bari ni ma dai in kashe kaina, in huta da wannan bakin ciki, raina dai ba shi da amfani gare ni muddin mijin nan nawa ba ya numfashi." Ta cira takobi za ta sare kanta, sai ta ji an ce, "Tsaya. Dauki kawunansu ki lillika musu, duk sai su tashi." Ta duba gabas, ta duba yamma, ba ta ga wanda ya yi mata magana ba. Sai ta tashi da rawar jiki, ta dauki kawunan ta lillika jikunansu. Ashe cikin dokin ta ga mijinta ya tashi har ta kidima ta dauki kan dan Sarki ta lika wa jikin bawan, ta dauki kan bawa ta lika wa jikin dan Sarki. Sai suka tashi, dan Sarki da kan bawa, bawa da kan dan Sarki! Kowane da mikewarsa sai ya rungume ta, ya ce matarsa ce. To, jama'a, wa kuka gani ke da mata? Bayi suka tashi da gardama haya haya, haya haya, wadansu na 119 cewa mata ta kan dan Sarki ce, wadansu na cewa a'a, mata ta gangar jiki ce. Suna cikin gardamar, ga bayin Waziri tsaye bakin zaure, ba wanda ya san abin da su ke jira sai aku. Sai aka ji tambura Sarki ya tinkaro. Kafin a yi haka, kofar fada ta fara daukar 'yam bushara. Bayin Waziri da suka ga ba dama, suka koma suka gaya wa Waziri, ya yi ta cizon hannu don bakin ciki. Jim kadan Sarki ya kawo, Mahmudu na gaba maroka sun daho shi, sai kirari a ke masa, ana yi masa waka. Mahmudu, jimre ka dau himma, Sai an gwada za a san babba. Zama ga daki na raggo ne. Wan Musa, taso mu je gaba. Mai son fada, duk ya zo nana, Gun Mahmudu, yanzu ya bar wasa. Sinari bana sun tabo wahala, Wan Musa Allah ya jaya ma! Sakaci da tsoro ka yashe su, Duniyag ga ba tai mai wauta. Sinari sun tuba, sun bi ka, Sarkinsu ya zo, ka gafarta. Kyaun saurayi duk ya dau mashi, Don shi da mata a bambanta. Ayyururui! Mutane, mu dau guda, Mahmudu da mai kamar baba. Allah ka dube mu kai rahama,. Allah ka dube mu kai rahama. Allah ka dube mu kai rahama, Ka ji kan mahaifa, mu ce amin! Da suka iso duk gari aka dauki alo alo. Musa ya tafi ya taryi Mahmudu a kofar gida, ya rungume shi, suka yi ta murna. Ya tambaye shi kwana nawa ya yi yana jiyya, ya ce shi ko kaya ba ta taba sukarsa ba tun fitarsa, balle ya yi jiyya. Musa ya yi ta mamaki. Ya tambaye shi batun takardar da ya sha yiwowa, ya се shi bai aiko kowa ba. Musa ya tafi dauko takarda, ya tarar ba ko daya, ashe duk aku ya kwashe su ya boye. Waziri ya zo yana 'yan dararraku, wai shi yana murna. Da aka natsa, aku ya ce wa Musa, "Na ji kana neman takardun da Mahmudu ya aiko maka sa'ad da su ke wajen yaki, ai suna nan na ajiye maka." Ya tafi ya dauko ya kawo musu, suka yi ta karantawa suna tu'ajjibi, suka boye takardun suka kyale. Da gari ya waye, sai suka dauki takardun nan suka kai wa 120 Sarki. Ya duba, ya ce, "Wańnan ai hannun Waziri ne." Mahmudu ya ce, "Hannun Waziri! Karanta ta ka ji." Sarki ya karanta takarda, sai ya rike baki, ya ce, "Me ya ke nufi da wadannan?" Ya juya ga Musa ya tambaye shi yadda aka fara, har aka aiko masa da wadannan takardu. Musa ya ce shi bai san abin da a ke ciki ba, tsammani ya ke Mahmudu ke aiko da su. Ya kwashe abin da aka fara aikowa, da dukan abubuwan da suka auku, da yadda aku ya yi ta rudinsa da labaru har bai sami fita ba, duk ya fada wa Sarki. Da Sarki ya ji haka, ya ce, "Ba shakka akwai magana. A kira aku." Nan da nan aka zo da shi, Sarki ya tambaye shi. Aku ya zauna ya kwashe yadda aka yi duka har da abin da suka yi da Waziri sa'ad da ya aiko a je da shi, da labarin bayin nan da a ke aikowa suna yiwo shirin mata suna zuwa, da abin da ya faru daren da Sarki zai dawo, har ya są suka komo cikin bayin da aka bari tsaro ya rika ba su labari don kada su yi barci, da yadda ya yi ta fama da Musa don kada ya fita, duk ya fadi. Da Sarki ya ji wannan abu, sai hawaye suka zubo masa don tausayin aku, ya dauke shi ya rungume, yana cewa, Yaya za mu yi mu fito wa wannan al'amari?"
Chapter 28 · 0% Book details