Sashe 27
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
me a jikinsa za a san lalle ya yi ado, ba abin kushewa?" Musa ya ce, "Kai fa na san ka, wadansu tambayoyinka duk na ba'a ne. Kai ba ka kan gani da kanka ba? Ai ko tsuntsu ya san ba abin da ke kambama mutum irin ya sa wando mai zina, da jabba, da riga aska takwas a bisanta, kana ya sami-." Aku ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ai ma ado ya kare. Kada in tsai da kai, sai da dare." Musa ya ce, "Allah ya kai mu da alheri." Da dare ya yi, barci ya share Musa, sai can da asuba ya farka, ya tashi, ya shiga damaru, ya dauko mashi ya zo wajen aku, ya cе, "Madalla, ai kowa ya yi karyar dare gari ya waye! Ka ce labarin 111. Shaihu da na bayar jiya ko na goye ya san shi. To, ina son in ji naka wanda ba a sani ba." Aku ya kada fiffike, ya dukad da kai, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, yanzu ko ka ji." 112 Labarin Shaihu Dan Hodiyo da Wani Malami Wata rana wani malami daga gabas da ya ji labarin Shaihu sai ya yiwo wa Sakkwato tsinke, ya zo ya ga abin da a ke fadi da idanunsa, domin an ce gani ya kau da ji. Da ya kusa da Sakkwato ya yi shiri irin na alhazai, ya shiga kokuwa, ya tafi wajen Shaihu Mujaddadi, ya ce, "Ina da fatawa, ya Shugabana." Shaihu dan Hodiyo ya amsa, "Allah ya sanasshe mu!" Mutumin nan ya ce, "Ya Shugabana,. da me a ke miya a nan kasarku?" Shaihu ya ce, "Da kuka, da gishiri, da tosshi, da daddawa." Mutumin nan ya се, "То, ashe sun sha bamban da na kasarmu." Ya yi ban kwana da Shaihu, ya fita. Shaihu ya ci gaba da sha'anin da ya ke ciki na jihadi. Aka ci kasashe, aka ba wadansu tutoci, sai can bayan shekara biyu har an manta da wannan mutum da ya yi tambaya, sai mutumin nan ya dawo, ya sami irin kayan Hausawa, ya yi shiri yadda ba mai ganewa shi ya zo bara waccan. Ya tafi wajen Shaihu ya gaishe shi, ya ce, "Da me kuma?"" Da ya ke Shaihu dan Hodiyo al'amarin nasa ya yi nisa, ya tuna tambayar bara. Ya dubi mutumin nan, ya ce, "Idan da wadata a kan sa nama." Ko da bakon nan ya ji haka, sai ya fadi ya nemi Shaihu dan Hodiyo gafara, ya sallame shi ya koma garinsu. "Tsakaninka da Allah, Allah ya ba ka nasara, ka taba jin wannan irin labari na Shaihu Mujaddadi in ba yau ba?" Musa ya ce, "Gaskiya dai, ban taba ji ba. Shin don Allah ko kai ka kaga shi yanzu?" Aku ya kada kai, ya ce, "Haba, Allah ya ba ka nasara, wallahi ba yanzu na kera ta ba, ni ma haka na ji shi. Ko mutum na hauka, irin karairayin nan da a ke wa tatsuniyoyi a yi wa tarihi kamar na Shaihu Mujaddi dan Hodiyo? Haba, ai wargi wuri ya ke yi." Musa ya ce, "To, ko da ya ke haka, kana tsammani wannan ya fi wanda na gaya maka jiya ban mamaki?" Aku ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ai ba gardama na ke ja da 113 kai ba. Wadannan al'amura ne na waliyyai, idan aka yi zurfi ciki, sai a tasam ma yin sabo. Ba mu da wata ta cewa, sai Allah ya ba mu albarkacinsu, amin, amin, amin!" Musa ya ce, "Gaskiya ne, Allah dai ya kiyashe mu azabobin Jumma'ar da ba ta da Asabar, domin alfarmar Shugaban talikai!" Ya juya zai tafi. Aku ya ce, "Af, Allah ya ba ka nasara, kana ya sami me?" Musa ya waiwayo, ya ce, "Kana ya sami me fa?" Aku ya cе, "Tambaya na ke. Kana ya sami me?" Musa ya ce, "Me ka ke nufi da 'Kana ya sami ne?' Wa ka ke maganarsa? Wane abu zai samu? In kana tambayar wani abu ne ka faďi mu ji. Kai ba abin da ke dibarka sai samartaka. To, ni na aske." Aku ya duka, ya ce, "Allah ya huci zuciyarka, yallabai. Sauran tambayar da na yi maka jiya, da na so in gani in ka iya iyad da jawabin da ka fara ba ni, don ka ce tarihin da na bayar yanzu na Shaihu Mujaddadi ba shi da bam mamaki kamar wanda ka bayar jiya." Musa ya ce, "Wane tambaya ka yi mini jiya?" Aku ya bushe da dariya, ya ce, "Jiya-jiya har ka manta, ranka ya dade? Na tambaye ka shin sai mutum ya sa me da me a jikinsa za a san lalle ya yi ado, ba kushewa. To, ina ga wannan da aka yi da shekara biyu?" Musa ya dubi aku ya ce, "Hо dan nema! Kai dai ba ka barin ko ta kwana, duk inda mutum ya fito maka kana make kana kallonsa." Ya duba haka sai ya ga gari ya waye, ya harari aku, ya ce, "In don mugunta ka ke mini wannan abu, ba kome, Allah ya isa." Ya shige gida. Azahar na yi sai ga Sarki Abdurrahman ya aiko da dan bushara an ci nasara, gobe kuwa tun da safe ga shi nan tafe. Musa ya tambaya. "Ina Mahmudu? Ya warke? Dan busharan nan ya cе, "Ai da ma ba abin da ya same shi, gobe ka gan shi." Kafin Musa ya sami damar tambayarsa sai ya hau ya koma, don an ce kada ya zauna. Duk gari ya rude da gude-gude, ana ta murna, Waziri ko sai ka ce an yi masa mutuwa. Magariba na yi sai ya kira wadansu samari hudu daga cikin yaransa, ya gaya musu abin da a ke ciki duka, ya yi alkawari in 114 sun yi kokarin da suka kashe Musa daren nan na yau, ko da su murde wuyansa ne, shi ko ya ba su fam ashirin ashirin. Bayin nan suka ce, "Don wannan har wani aiki ne?" Suka shiga neman kayan ado irin na mata suna sawa. Aku kuwa da ya ke ya san haka zai faru, magariba na yi sai ya ce wa Musa, "Yallabai, yau bai kamata a yi barci ba, sai mu koma babban zaure, mu gamu da bayin nan a yi ta hira." Musa ya ce, "Ai ko hakanan ne," Aka kai kujera, Musa ya tafi ya kame bisa, bayi suka kewaye shi. Jimawa kadan aku ya biyo, ya duba ya ga bayin nan ba mai wani makami kusa da shi, sai ya ce, "Ashe ku duka mata ne, yaya za a bar ku kumu ku rika zama ba mai ko sanda? Halal kun manta da duniya." Bayi suka ga gaskiyarsa, kowa ya dauko takobinsa ya zare ya ajiye a gabansa, aka shiga hira. Can lisha sai ga bayin nan na Waziri su biyar, har da Barakai, suka shige gida sai ka ce mata, aku kadai ya gane maza ne. Suka sami wani zaure suka make, su ba su cikin gida, su kuwa ba su waje. Suna nan suna jiran Musa ya shigo, don su tarye shi nan su halaka shi, hira ta ki karewa. In aku ya ga za su dan dakata sai ya yi musu wani abin dariya. Suka yi ta yin haka har asuba ta yi. Da aku ya ga sun gaji da hira, wadannan sun fara gyangyadi, sai ya ce, "Bari in yi muku wani labari mai daďi." Musa ya ce, "Ai ko hakanan ne, ku tsaya ku ji fasaha wurin dan tsuntsun nan nawa." Wadanda ke jin barci suka murje idanunsu. Aku ya sami ruwa ya kora, ya yi kaki ya zubad da yawu, ya fara: 115 Sauri Ya Haifi Nawa An yi wani Sarki nan arewa wanda ke da dan auta da ba a taba ganin kyakkyawa irinsa ba. Da fari dai ga shi, shi bai cika kyamushewa ba, shi kuwa ba kakkaura ba hakanan. Wuyan nan nasa sai ka ce goran nono, idanunsa ko fari fat sai ka ce madara. Gashin kansa ma abin kallo ne, don sai ka ce mai ya ke shafa masa. In ko har ya yi dariya ka ga hakoran nan, wayyo Allah! Kafafunsa kuwaMusa ya ce wa aku, "Kai don Allah in za ka ba mu labari ka ba mu mu sha, in ko ba ka ba mu, ka kyale mu kowa ya san abin da ya kama." Aku ya ce, "A'aha! A bar ni in gyara labarina yadda zai yi daďi." Wata rana Sarkin nan ya hau duk da mutanensa, don ya kewaya kasarsa ya buga musu haraji. Suna cikin tafiya sai autansa ya janye wani baransa, suka rika ja da baya. Suna son a wuce su kama labarin duniya. Ko da suka ga rundunar Sarki ta bace, sai suka yi ta tadinsa suna kakkawa suna tafawa. Suna cikin haka sai suka isa wani dan kauye wanda Sarki ya wuce tuni. Da suka ga azahar ta yi sai suka sauka, don su yi salla. Baran nan ya tafi gidan mai garin ya gaya masa ga dan Sarki nan zai yi salla a garinsa. Da bayin nan na Waziri suka ga ga shi har asuba ta yi Musa bai ko motsa ba, balle su sami damar gama masa aiki, sai suka sake shawara, wani daga cikinsu ya zo ya durkusa gaban Musa kamar mace, ya ce, "Ana kira ciki." Musa na tsammani baiwarsa ce, sai ya ce, "Je ki, ina tafe," ya koma, Aku ya ci gaba da labarin da ya ke bayarwa, ya yi ta jansa, don kada ya kare gari bai waye ba Musa ya ce zai tashi. Da baran ya wuce, sai ga wata yarinya kamar 'yar Larabawa ta fito daga wani gida kusa da masallaci. Tana leko kai sai duk wurin ya haske, in ka dube ta sai ka yi tsammani ba ta cin abinci don ba alamar ciki. Jikin nan nata kuwa na rantse har da girmanka, yallabai, kamar in ka duba za ka ga bargo. Hancirta 116 ko sai ka ce ita ta yi wa kanta. In da ka dubi idanunta sai ka rantse da Allah ba ta kifitawa, Gashi koMusa ya ce, "Kai, ya isa hakanan. Ci gaba da labari, ka ji ana kirana gida." Aku ya ce, "Ina zuwa." Ya yi