← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 31

Sashe 21

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na amsawa baki daya. In ya fadi ta farko, su kuma su fadi ta biyu, suna cewa: Ku zo ga daula wa zai ki, Alo alo, mu ci daďi! Kowa ya bari ta gota shi, Alo alo, mu ci daďi! Tuwo, nama, sai mun koshi, Alo alo, mu ci daďi! Nono da zuma ba mai zari, Alo alo, mu ci daďi! Siliki ran Salla ba datti, Alo alo, mu ci daďi! Zagi, mari, mun huta shi, Alo alo, mu ci daďi! Aikin wahala duk ba ma yi, Alo alo, mu ci daďi! Alo alo, mu ci daďi! Alo alo, mu ci daďi! Mutane ba su san abin da suka yi da Sarki ba, suna tsammani wasa Sarkin Busa ke yi da 'ya'yansu, sai suka tsaya suna daáriya, su ga ikon Allah. Amma da suka ga ya nufi kogi duk sai ransu ya baci, suna tsammani zai fada ne. Da Sarkin Busa ya fita bayan gari, sai ya tasam ma wani tsauni nan kusa da gari. Sarki da mutanensa na tsaye na kallonsu. Sarki ya ce a ransa, "Na san dai yaran nan ba su iya hawa wannan tsauni, na ga yadda zai yi da su." Ko da Sarkin Busa ya isa gindin tsaunin, sai mutane suka ga tsauni ya bude. Sarkin Busa ya kutsa ciki, duk yaran nan suka duru bayansa. Da suka shige duka, saura daya da aka bari can baya yana d'ingishi, sai tsauni ya rufe. Mutane suka yi ta kuka saboda batan 'ya'yansu. A cikin yaran nan akwai 'ya'yan Sarki su hudu, su ko ke nan gare shi, duk suka bace. 85 Inda Allah ya kyauta wa Sarki da ya ke mutane ba su san rashin tsaida maganarsa ta sa wannan abu ya faru gare su ba. Da sun sani nan take su ke halaka shi duk da zuriyarsa. To, ga shi kuma duk nasa sun bace, balle a ce wani makirci aka kulla da shi. Da uban yaron nan mai dingishi ya ga abin da ya faru, sai ya ruga ya jawo dansa, yana murna. Aka tambayi yaro me ya sa su ke bin mutumin nan? Yaro ya ce, "Ai mun ji yana cewa mu biyo shi, duk abin dadi na duniya ya ba mu. Ya ce akwai tabkin zuma, da nono, mu yi ta sha. Ga nama soyayye da dafaffe, wai inda zai nuna mana shinkafa ba a maganarta. Ni yanzu, duk bakin ciki na ke yi da aka bar ni baya. Yanzu suna can suna cin dadinsu, ni ina nan." Beran nan guda kuwa da ya haye, sai ya tafi ya iske wadansu beraye can, ba irin wadannan na bala'i ba. Ya rika ba su labari, yana cewa, "Ba ku sani ba, na yi daron cin dadi. A can ketaren rafi wani mai busa ya tara mu zai nuna mana inda daddawa ta ke banza, ga nama, ga mai, ga abinci iri iri, ba mai hana ka ci. Ya ce wajen nan da zai nuna mana ba a taba sanin akwai wani abu wai shi kare ba balle kyanwa, karamar alhaki. Zan isa, saura kadan, sai na ji na fada cikin ruwa. Yanzu 'yan'uwana na can sun yi kiba ni rashin sa'a ya sa ni na tabe!" Saura suka yi ta cewa, "Allah ya sa wata rana mai busan nan ya zo nan kasar, ya tafi da mu mu ma!" Sarki ya baza mutane cikin duniya, ko a sami labarin ya bulla wani wuri da 'ya'yansu. Aka yi nema, ko labari. Suka gaji suka dangana. Manyan gari suka ce, "Kai, ba ku sani ba fa, Sarkin nan ke da duk wannan gashin tsiya. Tun da aka halicci duniya kun taba ko jin inda irin wadannan al'amura suka faru?"" Saura suka ce, "A'a, lalle in ba tasam masa muka yi ba, har mu kuma zai sa a halaka mu." Sai suka taru suka tafi gidan, suka kunna masa wuta. Mai gari ya fito da gudu, suka bi shi da jifa, suka kore shi garin, ya fita tsirara. Iyalinsa kuwa suka fid da su, kowace ta nufi gidansu. Suka kwashe dukiyar da ya tara, da akwatunan kudi da ya jibge. Suka kona gidan, don kada sabon Sarkin da za su yi ya kwashi ciwon wancan na tsiya. Ka ji abin da ke aukuwa ga mai yin alkawari ba ya cikawa. Musa ya duba ya ga wuri ya yi haske, ashe har rana ta fito ba su sani ba. Sai ya ce wa aku, "Na ji abin da ke aukuwa ga mai alkawari ba ya cikawa. To, me 86 ke faruwa ga irinku masu hana a cika alkawari? Bai tsaya garin jiran amsa ba, sai ya shiga gida a fusace. Da azahar ta yi Waziri ya kira tsohuwan nán ya yi mata kwando goma na zagi, don har yanzu ta kasa dabarar da za ta yi tfito da Musa. Tsohuwan nan ta ce, "Kullum ina kokari, wani dan aku gare shi mai tsai da shi da labaru ko yaushe har gari ya waye." Waziri ya tashi ya mangare ta, ya ce, "Tun da ba ki da wata dabarar da za ki wayace dan tsuntsu, tafi, yau na sa wani." Sai ya kira bawansa Barakai, wannan da ya aika wajen Sarkin Sinari kwanan baya, ya gaya masa abin da ya ke so, da kuma yadda aku ke hana Musa zuwa da labaru. Barakai ya yi shiri irin na mata, ya tafi gidan Sarki, ya tarad da Musa inda tsohuwan nan ta yi masa kwatanci. Ya yi masa maganar Mahmudu na can rai ga Allah, ya ce wai Mahmudu ya сe a gaya masa, tun da ba ya kaurfar zuwa su gana, shi ma ko lahira kada Allah ya gama su. Musa ya fashe da kúka, ya ce, "Kullum ina so in tafi, dan akun-nan ke tsaishe ni da labari. Ga ko Sarki ya ce in na yi wani abu ba da na shawarce shi ba, bai yarda mini ba duniya da lahira." Barakai ya ce, "Don dai wannan dan tsuntsu, yau ka tafi. Nan zan kwana, da mun ji bayin nan sun yi barci mu je tare ka sallami akun, in hana shi ya tsai da kai." Musa ya ce, "Da kin kyauta.". (Don yana tsammani mace ce.) Suka zauna nan, har barci ya share bayin da ke zaure. Suka tashi suka nufi wajen aku. Ko da aku ya hango su tafe su biyu, sai ya gane Barakai namiji ne, ba mace ba ce. Saboda haka, kafin su iso su yi masa wata magana, ya riga su ya ce, "Don Allah, yallabai, yau ka tafi. Ni ba na iya ba ka wani labari. Duk inda ka ke son zuwa, ka tafi." Barakai ya dubi aku, ya ce, "Ko ba ka ce ba, da ma yau ba mu son wani labari naka." Aku ya langabe kai kurum, sai tausayi ya kama Musa, ya ce masa, "Me ya same ka yau?" Aku ya ce, "Tunani na ke yi." Da ya ke Musa ba ya son ya yi wa akun nan abin da zai motsa masa rai, sai ya tambaye shi tunanin da ya ke yi. Aku ya ce, "Ina tunanin abin da ya faru ga wani masassaki ne, wanda ya yi kokari ya tara fiye da abin da Allah ya ba shi." Musa ya ce, "Wannan masassaki ýa ja wa kansa halaka." Aku ya ce, "Da. ma ka ji abin da ya same shi, ai da ka san lalaçewar ba ta da iyaka." Bai tsaya a ko ce ya fadi ba, sai ya fara: 87 Kowa Ya Yi Kokarin Ya Sami Fiye Da Abin Da Allah Ya Nufe Shi Da Shi, Ya Ja Wa Kansa Lalacewa Domin wai akwai wani masassaki a Katako, yana da 'yarsa mai shekara biyar da haihuwa, sunanta Halima. Ko da ya ke an sanyaro a kan son tambayar kome ya ji ko ya gani, duk da haka son tambaye-tambayen Halima sun wuce kima. Wata rana da safe uban na zaune na sassakar wata kujera, sai Halima ta shigo, ta ce masa, "Baba, inna ta ga mussa ta ce mata kyanwa, ashe ba ta san sunanta ba, ko ta sani ke nan?" Kafin uban ya bayyana mata da mussa da kyanwa duk daya ne, sai ta sake masa wata tambaya, ta ce, "Baba, kawu ya ce wai akwai giwa na yawo nan sama, ita ce ke yin fitsari da damina muna cewa ruwan sama, gaskiya ne?" Uban ya fashe da dariya, zai bayyana mata ba gaskiya ba ne, sai ta ce, "Baba, wai kai ma inna ce ta haife ka?" Uban ya ga za ta hana shi aiki da surutu, sai ya ce mata, "Fita waje can, ki yi wasa da yara, sai in na kare ki dawo." Sai ta tashi ta ruga. Tana fita, sai ta ji yara na bin wani wada, suna cewa, "Malam Dogo, Malam Dogo! Halima kuwa ko wane karambani ya ja ta, da ganinsa sai ta tsaya daga kofar zaurensu, ta ce, "Malam Dogo, Malam Dogo, ka zo, baba na kira." Malam Dogo da ya ji haka sai ya nufo zauren. Halima ko ta ruga zaure wajen ubanta, ta rungume shi tana kuka. Tsammaninta wani dan sanho da wadan ke rataye a bayansa duk ba kome ciki sai 'yan yara kamarta. Malam Dogo ya zo, ya durkusa gaban masassaki, ya ce, "Ga ni, 'yar matan nan tawa ta ce kana kirana."" Masassaki ya kawo sadakar abinci da goro da kwabo, ya ba shi, ya ce, "Tun da Halima ta kira ka, ai lalle in sallame ka." Malam Dogo ya yi godiya, ya bude sanho ya fitad da wata 'yar nakiya da aka ba shi sadaka, ya mika mata, ta ki karba, don ita ce gamuwarsu ta fari. Daga ran nan kullum kuma in zai wuce sai yar biyo ta zauren -gidan, in ya ga Halima a waje ya ba ta dan wani abin da ya samo sadaka. Tun tana gudu, yau da gobe har ta saba da shi, ta rika tsayawa tana karba. Da ya gan ta dai sai ya zauna, ta hau bisa kafarsa suna wasa. In ta fara irin 'yan tambayoyin nan nata na yara, sai shi kuma ya rika ba ta amsa irin yadda ya kamata. In ta tambaye shi, "Me ke cikin sanhonka?" Sai ya amsa mata,
Chapter 21 · 0% Book details