← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 31

Sashe 18

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana ci, sai ya yi tsammani gaurakin nan ke ba shi kyauta, don suna sonsa. Saboda haka, da ya ga alherin ya yi yawa, ran nan sai ya daga kansa ya dubi gauraki, ya ce, "Kai 'yan'uwana, na gode! Kullum dai na kan ga 'ya'yan bauren da ku ke sako mini. Abin naku ya yi yawa, wallahi har kunyar godiya na ke yi. Allah dai ya saka da alheri!" Da gauraki suka ji haka, suka duba suka gan shi, sai suka gane abin da ke aukuwa. Da har babbar za ta ce masa su ba a kan sonsu bauren ke zuwa gare shi ba, sai karamar ta hana ta. Ta dubi kunkuru ta ce, "Don mun ga kai ba ka iya hawowa, shi ya sa mu da Allah ya ba fiffike mu ke taimakonka. Don dan wannan abu kada ka sa wa kanka wani jin kunya ciki. Allah dai ya bar zumunci." Kunkuru ya ce, "Amin! Na ko yi godiya." Suka zauna kan haka. Da abu kamar wasa, har ya zama aminci na gaskiya. Gaurakin nan da sun zo da safe, ba abin da su ke fara yi sai sun tambayi kwanan kunkuru tukun. Suka zauna, ba su son abin da ya taba shi, shi kuma ba ya son abin da ya taba su. Ana nan, bayan kamar wata guda baure ya kare, gauraki suka koma neman kwadi da tana. Bayan kamar wata biyu kuma dan sauran ruwan rafin ya kafe. Wurin ya koma sai ka ce dadai duniya ruwa bai taba zama nan ba. Da gauraki suka ga haka, sai suka yi šhawarar su tashi su sake wuri, don ba su iya zama sai inda ke da danshi-danshi. Ran nan har za su wuce, sai karamar ta ce, "Ya kamata mu je mu sallami kunkuru, kada ya ga shiru hankalinsa ya tashi, ya yi zaton wani abu ne ya same mu." Suka tashi, suka tafi wajen kunkuru, suka gaya masa za su yi kaura. 71 Da kunkuru ya ji haka, sai ya ce, "Af, to, ai ba ku barina, sai mu tafi tare. Abin da ya yi Goje, ai shi ya yi Kaura. Ni ina na ke iya zama inda babu laima?" Da gauraki suka ji haka, sai suka ce, "Yaya za ka yi ka bi mu, alhali kuwa kai ba ka da fiffike?" Kunkuru ya ce, "Sai ku dauke ni, in kun ga kwa iya kokarin hakanan." Babbar gaurakar ta ce, "Wa ka ke zato cikimmu zai iya daukar kato kamarka? To, ce ma muna iyawa, ina za a kama, ga ka jiki duk kwarya?"" Karamar ta ce, "Bar shi, mu ji tasa, watakila yana da dabara, Kin san an ce mai rai ba ya rasa kokari." Kunkuru ya ce, "I, ina kuwa da wata 'yar gurguwar dabara, in kwa iya. Sai mu sami kara mai karfi kamar zira'i biyu, ni in cije tsakiyar, ku kuma kowace ta kama gefe guda dá baki. Kun ga da haka sai ku tashi da ni har inda za ku." Babbar ta ce, "Wannan dabarar ban ga za ta yiwu ba ga kamarka, mai surutu." Karamar ta ce, "A'a, in ya ce dai ya iya kyalewa, ai sai mu 72 daúke shi." Ta tashi, ta tafi ta samo karan dawa mai karfi, ta dauko, ta zo ta ajiye gaban kunkuru. Ta dube shi, ta ce, "To, don Allah in ka kama, ban da yawan magana." Kunkuru ya ce, "Haba, wannan ma sai an dankwafe ni kansa, sai ka ce yaro? in yi surutu mana, in ina so!" Gauraki suka ce, "To, madalla!" Suka kama kara suka tashi da kunkuru yana cije. Suna cikin tafiya, sai hanya ta daukè su ta bisan kasuwa. Suna kaiwa tsakiyar, sai mutane suka daga kai suka hange su, suka ce "Eho, eho, ku zo ku ga inda gauraki ke daukar kunkuru! Kai jama'a, abin mamaki ba ya karewa nan duniya!" Da kunkuru ya ji haka, sai ya fusata ya ce, "Kai, Allah ya tsine idandunan nan naku mutane, da ba su iya ganin abu su kyale." Bai gama fadin abin da ya ke nufi ba, sai da ya kawo ķasa kum. Duk da karfin kokon san nan, ya haure, bai ko motsa ba. Gauraki suka wuce abinsu suna bakin ciki, suna cewa "Wanda duk bai iya mulki da bakinsa ba, lalle yana tare da halaka." Musa ya saurara haka, sai ya ji wani daga cikin bayin nan na ta da 'yan'uwansa, gari ya waye. Ya bata fuska. Aku ya ce, "Ai ko yau ba ka yi zaman banza ba, don na yi maka gargaďi." Musa ya çe, "Gargado!" Aku ya shiga shashatad da shi, har ya 'ciwo kansa. Suka yini nan suna 'yan tade-tade. Da rana ta fadi, lokacin fitar Musa ta yi, sai ya taho ya ce wa aku, "Yau, don Allah ba ka kyale ni in wuce baki alaikum?" Aku ya ce, "Sai ka dawo." Musa ya ce, "Kai, yau wace rana ka kyale ni ba ka yi min wani surutu ba!" Ya sa mabudi ya bude zaure na farko ya taka zai shiga ya buda na biyu, aku ya biyo shi, ya ce "Yanzu wani babban abu ya fado mini a rai. Kwanaki na bä ka maganin karfe, na manta ban ba ka kau da bara ba. Ko kuwa ba ka so ka iya gociya?" Musa ya ce, "Ban iya gociya ba, in kau da baran na kusa ka kawo mini. Ba wanda ya ki taimako." Aku ya ce, "Wani kauci ne nan kusa, bari in fita in kawo maka." Ya fita fir ta taga. Musa ya ce, "In kana wa Allah, ka yi sauri!" Aku ya ce, "Shi babba." Ya tafi ya sami wani lambu, ya yi ta satar baure yana ci. Da ya koshi, ya ga kamar asalatu ta yi, ashe farin wata ne, ya debo ganyen bauren ya taho, ya ce wa Musa, 73 "Ga shi, ka sami saki ka dfinke shi da shi, ka gama cikin damarunka, ko ana ruwan kibau, ka tabbata ba dayar da za ta same ka. Amma da sharadi guda, ya kamata ka koyi gociya, domin kau da bara duk ba ta ci sai ana gamawa da 'yan zukezuke." Musa ya ce, "To, madalla." Ya bude zaure na biyu, aku ya dubi gabas yà gani ko asalatu ya yi, ya ga ashe bai yi ba, farin wata ne ya rudo shi ya dawo da wuri. Sai ya tashi da 'yan tsalletsalle yana bin Musa, ya tarad da shi har ya bude zaure na uku, ya ce, "Bari in gaya maka wani labari mai daďi. Wata rana akwai دو wadansu 'yam makaranta Musa ya ce, "Kai, tafi ka ba ni wuri! Ni na gaji da labarun nan naka." Ya bude zaure na hudu. Aku ya yi tsalle ya bi shi, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni dai wallahi kana kayatad da ni, tun da ba ka wuce maganar iyayenka ba. Dubi abin da Sarki ya gargade ka da ni, ka ga har Allah ya kawo mu rana wa ta jiya kana nan rike da abin nan da ya се." Musa ya waiwayo ya ce, "Rana wa ta jiya kadai, ranar yau fa?" Aku ya ce, "Ai kullum kana rike, da ma dai ai-." 74 Babban Mugun Abu Gun Da, Ya Yi Fushi Da Iyayensa Ina tsammani ban taba gaya maka ba, wata rana aka yi wa wadansu 'yam makaranta jarrabawa. Daga cikinsu akwai dan limamin garin, ana kiransa Ilu. Ba ya kula da aiki ko kaďan. Kullum in ana koya musu aiki, shi sai ya yi ta wasa. Saboda haka da aka yi jarrabawan nan bai ci kome ba. Sai ya sami sifiri. Malaminsa ya yi fushi kwarai da ya ga haka, ga yaro dam manyan mutane ya lalace. Saboda haka ya je ya gaya wa liman abin da dansa ke ciki, don kada nan gaba a kore shi, uban ya bata rai. Da aka gaya wa uban, sai ya kira shi wai ya yi masa fada ya kara kokari. Ya zazzage shi yana cewa in bai yi kokari ya yi karatu ba, ba shi da wani amfani, sai fa ya je ya yi tallan tsire. Yaro ya tashi yana ta hushi, wai uban ya ce in bai yi kokari ba, zai ba da shi ga mahauta ya je ya yi tallan tsire. Ya koma karamin zauren gidan, ya zauna. Yana nan yana ciccika, lokacin cin abinci ya yi, kanensa Ibrahim ya zo ya kira shi su je su ci. Sai Ilu ya dube shi da hushi, ya ce, "Je ka, ci! Ni ban ci." Ibrahim ya bushe da dariya, ya ce, "Kana tsammani wani ya kula don ba ka ci abinci ba? Je ka, huta." Ya tafi ya gaya wa iyayen. Liman ya ce, "Fushi ya ke yi, don na yi masa fada? To, kyale shi! Don cikinsa." Matar ta ce, "Ya da ta ki auren Sarkin Noma ba?" Ko da ya ke uwar ta ce haka, duk da wannan hankalinta na Wajen Ilu. Та kaikaici idon liman, ta tafi wajensa tana rarrashi, ya ki cin abinci. Ta yi ta yi, sai ya dube ta, ya ce, "Ina ruwanku da ni, ni da kuka ce ba ni da amfani sai ga masu tsire? Ina kokarina, don malam ya ki jinina ya zo ya ce ba na kokari. Na ko san duk ajin nan ba a samun yaro goma gabana." Sai uwar ta tashi, ta ce, "Bari mu je mu ajiye maka." "Me za ku ajiye mini? Ni ko kun ajiye, ba na ci. Me za ku yi da mai tallan tsire?" Da liman ya duba, bai ga matar ba, sai ya yi tsammani tana 75 wurin Ilu ne, saboda haka ya sa baki ya kira Ilu, ya ce, "taso ka ci abinci, kada ka yi sakarci." Ilu ya ce, "Ba sakarci na ke yi ba, karatu na ke yi. Kuma ni mai tallan tsire, yaya zan ci abinci da ku?" Liman ya ce, "Ho lalatacce, d'an banza, mai taurin kai! Allah wadan yaron zamani!" Ilu ya ce, "Na kuma zama dan banza, lalatacce, bayan da fari ga ni bawan mahauta?" Ibrahim ya dubi uban, ya ce, "Ya yi fushi ne, baba." Ashe Ilu ya ji, sai ya ce, "Kai kuma me ya sa bakinka
Chapter 18 · 0% Book details