← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 31

Sashe 6

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ita, da ba ya magana biyu. In dai na yiwo mata na dawo, na yi maka don amfanina ke nan kawai wajenku." Dan zaki ya ce, "Zancen banza. Mece ce kura, har ka ce sai ka 15 yi mata gida za ka yi mini?" Ya taso wa Bororo, ya sa dagi ya keta masa dan warki. Bororo ya dubi warkinsa sabo ful, an yi masa karantsaye, sai ya kume, ya dai hade bacin ransa, ya ce, "Tun da ka ce kana so, manyan dawa, ai sai a tsaya a yi maka tukun." Dan zaki ya ce, "Dole. Ashe ana tsoron Inna, in ji 'ya'yan mayya." Bororo ya tsuguna ya shirya tsabgunan, ya yi tsaikon daki mai karfi tsakar wadansu itatuwa. Ya bi tsaikon nan ya daure tam da itatuwan nan, sa'an nan ya samo ciyawa himi guda ya tara, ya samo kirare tuli ya tsiba gefe daya, kamar mai shirin gashin tukwane. Da ya tara su duk, ya yi ta diba, yana jitawa bisa tsaikon nan. Ya bar'yar kofa wadda za ta isa dan zaki ya shiga. Da ya gama aminta shi, ya durkusa gaban dan zaki, ya ce, "Shiga mu gani in ya yi daidai da kai." Dan zal:i ya shiga cikin bukka, nan da nan Bororo ya mai da itatuwa, ya kulle, ya buga kyastu, ya kewaye bukka da wuta. Da hayaki ya murtuke, dan zaki ya kasa numfashi, sai ya yi neman fitowa, ya kasa. Da ya ji ya matsu, sai ya yi kara ya сe, "Kai Kuzajje, wannan daki naka ya faye kunci, kuma iskar ciki ba ta shakuwa. Fid da ni." Bororo ya ce, "Haba, me ka ce? Kara fadi in ji? Ka makara. Ni ne mutum wanda ka ke fartar kasa ka ke cewa sai kun gamu. Kafin ka fara shan alwashi, da ya kamata ka tambayi iyayenka, ka ji yadda mu ke murtuku da su." Da dan zaki ya ji wuta ta kama ba ba ba, ya ce, "Na tuba, don Allah ka fid da ni!?" Bororo ya ce, "Haba, da ma ka dangana. Alkalami ya bushe." Dan zaki ya cinye wuta kurmus. Bororo ya kama hanyarsa ya yi gaba. Wanda ya raina maganar na gaba gare shi, ya yi abin da ya ga dama, kome ya same shi babu kaito. Musa ya ce, "Me na ke ji haka kamar kiran salla?" Aku ya saurara, ya ce, "Kiran salla ne kuwa! Kai, wannan ladani ya yi sauri. Har asalatu ta yi?" Musa ya tashi ya shige, bai ce masa kome ba, don ya ga ba damar fita, duk mutane sun farka. Musa ya yini ran nan yana ta cizon hannu, bai sami fita ba har dare ya yi. Ya zauna yana allaalla bayin nan su yi barci, suka ki, sai can asuba. Da ya ji sun yi. 16 barci suna minshari, sai ya tashi ya taho wurin aku neman iznin tafiya. Aku ya ce, "Yallabai, ina ni ina hana ka abin da ka ke so? Alhali ko ma abin da a ke so ne ga dukan dam Musulmi, zumunci. Sai ka yi hanzari, ka ga alfijir ya keto." Musa ya juya zai fita, aku ya ce, "Yallabai, sai ka dauki fitila. Jiya na ji an koro wadansu barayi daga gidan Kakaki, na ji 'Yan Gadi na cewa kowa suka gani ba fitila sa kama shi." Musa ya ce, "Yaya aka yi ban ji ko kuwwa ba, ga shi kuwa ban runtsa ba?" Aku ya ce, "Hankalinka ne ba ya nan, da ka sha dariya. Wani barawo ne ya shiga taskar Kakaki, ya shinfida bargo yana shirin daure kayayyakin da ya sata, sai wani barawon kuma ya fado dakin, bai san wannan gudan ya riga shi ba. Yana sawo kafa ciki, sai wannan barawon da ya fara zuwa ya yi tsammani Kakaki ne mai gidan. Saboda haka ya yiwo kofa da gudu. Shi kuma wannan da ya zo yanzu, da ya ji an nufo inda ya ke, sai ya yi tsammanin shi aka biyo, shi kuma ya yi baya ya zura a guje. Banza ta kori wofi, yadda 'Yan Gadi suka yi da suka kori barayi daga gonar Madaki." Musa ya ce, "Jiya har sata biyu aka yi? Sun ga Sarki ba ya nan!" Aku ya ce, "A'a, nasu dabam ne." 17 Banza Ta Kori Wofi Wata shekara aka yi tsananin yunwa a wani gari, har abinci ya zama ba mai ganinsa sai mai dalili. Talakawa da matsiyata ba su da wani abinci sai rogo, rogon ma bai wadata ba. Saboda haka wadanda ba su da ko dalilin samun rogon sai suka rika zuwa gonakin rogo da tsakad dare suna satowa. Ana nan cikin wannan hali, sai wadansu mutum uku suka yi shawarar su tafi gonar Madaki su sato rogo. Suka dauki kwanduna, da dare ya raba suka nufi can. Daya daga cikinsu ana kiransa Kodago-a-taka-a-kare, guda kuma ana ce masa Kadanmai-ban-haushi, daya kuwa sunansa Kazunzumi-a-gan-ka-аraina. Da shigarsu sai suka yi wa juna rada suka ce ya fi kyau su ci tukun, sai sun koshi sa'an nan su diba, gobe su kai kasuwa su sayar. Saboda haka suka debo, suka sami wuri suka zauna suna ci. Kodago ya dubi saura, ya ce, "Kai, ai ko rogon mutumin nan duk zako ne." Kadan ya ce, "Haba, ai zakin ba magana a ke yi ba, in ka sa baki sai ka ji kamar sukar." Kazunzumi ya ce, "Ai Allah ya buda mana kofar arziki." Tun suna raďa har dadi ya sa suka koma magana sosai, kamar suna cikin gidajensu. Da suka koshi suka yi ta tuga suna cika kwanduna. Ka san dare in ya yi tsaka, da an yi 'yar magana ko da sannu sannu ce, sai ka ji ta da nisa. Saboda haka waďansu 'Yan Gadi suka jiyo su, suka lababo, suka tasam musu suna cewa, "Kada su kai! Biyo nan, harbar su! Kowa ka gani, kashe shi!" Sai suka yi ta bara da ka, suna harba kibiya cul cul. Wadannan 'Yan Gadin wadansu sakarkarun kauyawa ne, sabon shiga. Da jin yadda suka tasam ma barayin nan da hauka haka, ka san gaulaye ne, tashin kauye. Ka san in da 'Yan Gadi ne na sosai, Allah ya ba ka nasara, sai su lababa da ya ke ana duhu, su kama su a hannu ba su sani ba. To, ka ga yadda suka bata al'amarin. Ko da barayin nan suka ji haka fa, sai suka kwashe 'yan 18 kayansu suka runtuma da gudu. 'Yan Gadi kuma suka dafo su suna cewa, "Kada su kai!" Ko da ya ke ana duhu, har ba mai ganin kowa, duk da haka 'Yan Gadin nan na ta kurari, suna bin motsin barayin. Barayin nan suka yi ta gudu kamar ransu zai fita. Suna cikin gudu dai, sai Kodago ya yi wa saura rada ya ce, "Kai, ni fa na gaji, ya kamata mu yar da kwandunan rogon nan, mu yi ta kammu."" Kadan ya ce, "Ni ma da abin da na ke shiri in gaya muku ke nan." Da Kazunzumi ya ji haka, sai ya ce, "Kada ku yi saurin karaya. Ku dai dan jure kadan, ku ga tawa dabarar." Sai ya fadi rica, ya ce, "Wayyo Allah, ya kashe ni! Ashe, harbin nan da na ce an yi mini, sai yanzu dafin ya narke. Ku ji kaina, 'yan'uwa, ku yi mini rai." Ya rada wa sauran abin da za su ce. Sai suka ce, "Tashi don Allah, mu isa gida, watakila ka sami makari, in ka sha ka amaye shi." Kazunzumi ya ce, "Ni tawa ta kare. Ina maganar tashi?" Kodago ya ce, "Lallabo dai, in fa ka mutu ai lalle mu je Gidan Sarki da su, su gaya masa dalilin da ya sa suka kashe ka, don mun debi saiwar rogo za mu ci, kada mu mutu da yunwa." Kazunzumi ya marairaice ya ce, "To, mu tafi in gani, in na iya." Ko da barayin nan suka ji wannan makircin, sai suka kara mai. Da 'Yan Gadin nan suka ji haka, sai guda ya dubi dan'uwan, ya ce, "Ka ji abin da suka fadi?" Dan'uwan ya ce, "Ai na ji." Shi kuma ya dubi na ukun, ya се, "Kai ka ji abin da suka.ce?" Na ukun kuma ya ce, "Na ji mana, ai kome ya same su halas ne. Mu matsa, ko sun yar da abin da suka sato, mu gani." Suka dai yi ta bin su. Da Kazunzumi ya ji suna tafe sai ya sake faduwa, ya ce, "Wayyo, ni kaina! Da dai na ce ko zan kokarta in kai gida, don in sami inda za a lura da ni, kada in kumbura kafin safe. Amma na ji dafin ya ci karfina. Ku ku yi ta kanku, ku kyale ni, ashe da ma kasa ke kirana. In kun isa ku ba mata da iyalina hakuri, su tuna dukan mai rai mamaci ne."" Da'Yan Gadi suka ji haka, sai suka cirje, suna saurare. Ya sake cewa, "Ku lura da wasicin da zan yi. Ku shaida na ce a ba da sadakar sule talatin daga cikin kudina da na bari. Kuma ku na ba ku amanar 'ya'yana, ku lura da su da kyau, kada su sangarce. Ni tawa ta kare." Ya yi kalmar shahada. Da'Yan Gadin nan suka ji haka sai wannan ya dubi wannan, wannan ya dubi wannan. Kodago da Kadan kuwa sai suka yi ta tafa hannu, suna 19 sallallami, suna cewa, "Kada ka gakamar ka yi mutuwar kare, ka ji. Yadda aka kashe ka duk wanda ya yiwo harbin nan ta same ka shi ma sai Sarki ya sa an tsire shi, in gari ya waye. Ai cewa aka yi su kama barayi, ba a ce musu su kashe ba. Duk mu tsaya, in ya so in za su kashe mu ne su kashe mu duka, tun da dai suka raba mu da dan'uwammu. In ko suka kashe mu, ai lalle sur ma a kashe su, don mu ma Musulmi ne, ba kafirai ba." Da 'Yan Gadin nan suka ji haka fa, sai suka yi tsammani sun kashe mutumin nan ne. Saboda haka suka fara shawarar su gudu, kada a gan su. Suna cikin shawarar inda za su bi, sai suka ji barawon nan na kwance, ya fara kakarin mutuwa, yana shakuwa kikaf kikaf. Can
Chapter 6 · 0% Book details