Sashe 10
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haushi kuwa ya kama shi, ya ce a ransa, "Kai, ba na dai yarda in yi asara a wofi don lalataccen nan!" Sai ya dubi dam birni, ya ce, "Ashe ka koma mutum kuma?" Dam birni ya yi biris da shi. Sai bakauye ya tasam masa ya kama shi, ya sa masa akumari, ya ce wai zai hau ya tafi da shi ya yi kwarami. Dam birni da yana tsammani da wasa ya ke, sai ya ga ya yi wuf ya haye kafadarsa. Ga shi ya fi dam birnin karfi, ya kuma fi shi iya kokawa, ya yi ya yi ya ka da shi, ya kasa. Mutane suka cika wuri su ga.ikon Allah. Bakauye ko bai kula da su ba, sai df1, dl, d'l, ya ke yi, yana has! kur! wai shi ya hau jaki, yana ta ba shi dudduge a ciki, yana duka. 34 Da dam birni ya ji ba dama, sai ya kwanta. Bakauye ya haye cikinsa yana duka, wai ya tashi su tafi, yana cewa, "Ai fa ko a janye sai na kai ka gida, ka daukam mini taki, ba na yarda in yi asara. Ka sha ka zagi uwarka, ta mai da kai jaki, na saya ban sani ba, ta koma ta gafarta maka ka koma mutum, na dauki asara, na sake ka. Ranar Talata kuma, da na zo cin kasuwa, na tarar ka sake yin wani abu ta mai da kai kuma jaki, wani ya saya. Ga shi yau kuma ina ga ta gafarta maka, ka koma mutum. Ka sa kuma wancan mutumin da ya saye ka ya yi asara kamata." Ya dubi mutanen da ke kewaye, ya ce, "Don Allah, jama'a, gaskiya fa kun ga wannan na yiwuwa? Kura da shan bugu, gardi da karbe kaya? Ai ka san ba abin da zai hana ni yin kwarami da shi, ko kuwa ya fanshi kansa:" Sai ya sake hau masa da bugu, wai ya tashi su tafi dai kauyensu. Suna cikin haka sai ga wani Dogari, ya kwashe su ya kai ga Alkali. Alkali ya tambayi bakauye yadda aka yi, duk ya kwashe ya fadi, bai rage kome ba. Da mutane suka ji haka, suka ce me za su yi ba dariya ba? Alkali ya tambayi dam birni in hakanan ne. Dam birni ya ce faufau shi bai ko taba ganin bakauyen ba, sai yau. Alkali da ma ya san halin irin mutanen nasa sa aika. Sai ya sa Dogarai su tambaye shi sai ya faďi gaskiya. Da masu fushi da fushin wani suka same shi, ya ji zafi, sai ya ce, "Wayyo Allah, ku tsaya, ku tsaya!" Suka dakata. Ya kwashe maganar bakauye, ya ce duk hakanan ne, mutane suka yi ta al'ajibi. Alkali ya sa ya biya bakauye kuďin jakinsa sule goma sha daya da taro, yadda bakauye ya ce ya saya. Ka san abu hannun barawo, shi fa dam birnin nan sule shida da sisi ya sayar da shi wannan kasuwar da ta wuce. Alkali ya sa aka daure dan birni. Bakauye ko aka ba shi kudinsa, ya tafi. Bakauye dai bakauye ne. Duk abin nan gogan naka har ya tafi bai san wayo ba dam birnin nan ya yi masa ya sace jakinsa. Shi har yanzu tsammani ya ke dai rikida ya yi. Musa ya yunkura zai fita, sai ya ji magana a babban zaure, wadansu daga cikin bayin sauro ya dame su, sun kasa barci. Suka farka suka yi ta taďi har gari ya waye. Musa ya koma gida yana jin haushi. Da shigarsa gida ka san ba abin da ke cikin idonsa sai barci, don duk cikin 'yan kwanakin nan bai runtsa ba. Ko da ya kwanta bai farka ba sai can zuwa la'asar, ya tashi ya yi salla, yana nan har 35 magariba ta yi, aka ci abinci. Bayi suka duka hira. Da Musa ya ji bayi sun yi barci, ya tashi ya shigo damaru, ya ce wa aku, "Don Allah yau kada ka tsai da ni, sallame ni in tafi. Kai, Allah ya kiyashe mu! Ban taba ganin tsuntsu mai surutunka ba." Aku ya tuma nan ya tuma nan, ya ce, "Ba kai kadai ba, Allah ya ba ka nasara, kowa na ganin surutummu, amma in kun lura da mu ba mu surutu a banza. Ko dai mu ba da gargadi, ko kuwa don rashin munafuncimmu mu bayyana asirin da muka gani ana kullawa za a cuci jama'ar Annabi. Don haka yanzu duk inda muka fi rashin fada shi ne wurin mata. Tsaya ma ka ji yadda wani aku ya yi da wata mace, don ka san dai al'amarimmu muna yi don Allah ne, ba don mutane su yaba ba." 36 Labarin Wani Aku Da Matar Ubangidansa Wata rana wani tajiri za shi fatauci, sai ya bar matarsa a gida. Yana kuma da wani aku. Suna nan tare, sai matar ta rika fita yawo, don ta ga mijin ba ya nan. Barorin gida da suka ga abin ya dame su, ba su da damar su yi magana, kada matan nan ta sare su wajen mai gidan in ya komo. Saboda haka suka zura mata ido. Ana nan ran nan sai mai gida ya dawo. Ka san al'amarin duniya ba shi boyuwa, sai wani ya tsegunta masa abin da matarsa ta yi ta aikatawa bayan ba shi nan. Da mai gidan nan ya ji haka, sai ya kira matar, ya same ta ya yi ta zagi. Ya dauki sanda kuma ya ba ta kashi. Da matan nan ta ga haka sai ta yi yaji, aka komo da ita. Ta ce a ranta, "Ba wanda ya fadi abin nan sai aku." Ka san mu, Allah ya ba ka nasara, bakin jini gare mu kwarai, tun ba game da mata ba. Suna cewa mun faye tsegumi. Saboda haka, ta bari mai gida ya tafi kasuwa, sai ta kama aku, ta fige shi da rai, ta wurga shi waje ta taga, ta ce, "Daga gare ni ka bar tsegumi!" Allah ya sa aku bai mutu ba, ya tsallaka har ya kai wani hurumi ya sami kabari ya shige, ya yi ta jiyya. Da mai gidan nan ko ya dawo, sai matar ta ce wai bayan fitarsa kadan kyanwa ta cinye aku. Ko da ya ji haka sai ya san karya ta ke yi, kashe shi ta yi, don tana tsammani shi ya gaya masa tana fita da ba shi nan. Saboda haka ya fusata kwarai da gaske, .ya same ta da duka kamar ba zai bar ta da rai ba. Ya kore ta daga gidan, ta tafi wajen hurumin nan tana kuka. Ashe aku na nan kusa da ita cikin wani kabari, yana ji. Sai ya ce mata. "Yi shiru, bari kuka, in Allah ya so kya koma dakinki. Amma akwai sharadi guda, sai ki je ki aske kanki sarai, sa'an nan ki dawo nan, gobe zan taimake ki ki koma." Matan nan ta duba, ba ta ga kowa ba. Abinka da mace, sai ta yi tsammanin, wani matacce ne ke yi mata magana. Nan da nan ta tafi gidan iyayenta, ta sa aka aske mata kai kwal. Da gari ya waye, maraice ya yi ta nuho wajen hurumi, kai na kalli sai ka ce na namiji. 37 Da isowarta sai ta tafi wajen kabarin. Abinka da jahila, ta durkusa, ta ce, "Na asko." Sai aku ya ce, "To, kin san dalilin da ya sa na ce ki aske kanki, domin kin zalunci wani dan tsuntsu, kika targe shi a kan abin da bai ji ba bai gani ba, har kika fige shi da ransa, kika wurgo shi bayan gida. A wannan na yi miki sauki, na ce ki aske gashin kanki kawai, amma in kin kuskura kika sake yi wa wani tsuntsu haka, ki kuka da kanki. Amma akun nan da kika kashe zai komo duniya, yadda zan mai da ke dakinki, shi kuma zan mai da shi gare ki. To, ki lura da shi da kyau, ki sa mijinki ya ajiye yaro guda mai hankali wanda zai rika lura da shi, a rika ba shi ruwa da sukari. Kuma ki tsawata wa yara su bar kiransa aku kuturu." Matan nan ta kara dukawa, ta ce, "Na ji." Da za ta tashi sai aku ya ce, "Da saura. Yau kin ga sha biyu ga watan Safar. To, ko wace shekara sha biyu ga watan Safar ki aske kanki, don ya rika tuna miki aku dai da ki ke ganinsa banzabanza ba banza ba ne. Amanar Allah ce ya sa a hannunku 'yan Adam, ya fi kyau kuwa ku lura da ita da kyau. Watan duk da ya zo ba ki aske kanki ba, yadda na gaya miki yanzu, ki tabbata ba ki shekara. Shi ke nan, gobe kya koma in sha Allahu. Tafi gida abinki. Amma ki kiyaye gargadin nan da na yi miki, ki kuwa yi kirki, ki bi mijinki sau da hannu. Allah ya gama mu da alheri & Darassalamu!" Mace ta koma gidansu. Aku ya tashi yana tsalle, har ya kai gidan tajirin nan, ya ce masa, "Ka san ni?" Tajirin ya dubi aku ba gashi, ya ce, "Yaya zan yi in san ka, ban taba ganinka ba?" Aku ya ce, "Ba ka taba ganina ba? Ai ni ne akunka wanda kyanwa ta cinye." Tajiri ya ce, "Tun da kyanwa ta cinye ka, yaya kuma aka fara har ka yi rai? Da ma dai ba kyanwa ta ci ka ba akwai yadda aka yi." Aku ya ce, "Daga cikin kyanwar aka nufa in fito, don in shaida maka duk abin da matarka ta fadi na batun kyanwa ta cinye ni gaskiya ne. Kada ka zarge ta. Amma in kana sona, zan kara dakatawa kuma wurinka, in yi gashi in koma kamar da, har Allah ya kari kwanana gaba daya. Amma sai ka mai da matarka, ka yafe mata, ku yi zaman lafiya." Mai gida ya ce, "To." Ya aika matar ta dawo, ya gafarta mata, suka sake zamansu. Daga ran nan ta zama mazar kirki, duk gari ba wadda a ke so sai ita a kan kirki. Musa ya tashi zai fita, aku ya dube shi, a ce, "Wallahi, yallabai, ba ka ga yadda ka rame ba. Maza ka ta i kada zulumi ya 38 halaka mana