← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 31

Sashe 26

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tafi, Shaihu na gaba, yana biye. A lokacin nan ko la'asar ta yi sakaliya. Da fitarsu kofar gari, sun dan taba tafiya kadan sai suka kai ga wani dan rafi, suka sa kafa suka tsallake, sai suka isa wani daji, Umaru Mu'alkamu ya duba, bai ga kome ba sai itatuwan goro ko'ina. Shaihu ya dube shi, ya ce, "Ka ce kana kawar goro, to, ga su nan, debi iyakar abin da ke isarka." Umaru Mu'alkamu ya shiga diba yana mamaki, ashe akwai dawan goro kusa da Sifawa ba a sani ba? Ya cika aljihunsa, ya се wa Shaihu dan Hodiyo, "Ai wannan ya ishe ni, Allah ya gafarta malam." Nan da nan suka tsallako dan rafin nan suka komo gida. Ana nan, bayan 'yan kwanaki kadan goron da Umaru Mu'alkamu ya debo tare da Shaihu ya kare. Da ya ga dai dawan goron nan ba nisa gare shi ba, sai ya tashi shi kadai ya kama hanyar da suka bi da Shaihu, yana sauri ya je ya debo kafin hantsi ya yi zafi. Ya yi ta tafiya, ya yi ta tafiya har rana ta take tsaka cur bai ga ko alamar ya kusa da wurin ba. Sai ya yanke kauna, ya juyo. Kafin kuma ya iso sai da la'asar ta yi sansanya. Da isowarsa bai zame ba sai wajen Shaihu. Suka gaisa, ya dubi Shaihu, ya ce, "Kai, yau na ga tasku!" Shaihu ya ce, "Me ya same ka haka, har ka ke yaba wahalar da ka sha?" Umaru Mu'alkamu ya ce, "Ai tashi na yi tun da safe, wai in tafi dawan nan na goro da muka je da kai shan iska kwanan baya 107 na debo, in sake karowa. Na yi tafiya har Allah ya gajishe ni, ban ga na kai ko dan rafin nan ba. Da na ga rana ta yi tsaka dai, sai na rufa wa kaina asiri na dawo. Ka ga tun sa'an nan isowata ke nan, ko ruwa ban biya gida na sha ba." Shaihu dan Hodiyo ya dube shi, ya yi murmushi ya ce, "Da ka san inda muka tafi fitarmu ran nan, da ba ka ce za ka bi ba. Ai cikin dawan Gwanja na kai ka ka samo goron." Umaru Mu'alkamu ya rike baki. Shaihu ya ce, "Ka ga dan rafin nan da muka sa kafa muka tsallake kafin mu shiga dawan goron?" Umaru Mu'alkamu ya ce, "Na gani." Shaihu ya ce, "Wannan ai kogin Kwara ne ka ga ya tsulance hakanan." Umaru Mu'alkamu bai sami ta cewa ba, sai ya kada kai kawai, ya ce, "Allah ya ba mu albarkacinku!" Da Musa ya ji haka sai ya ce, "Af, wannan ai ina tsammani ma shi na fara ji cikin mu'ujizozin Shaihu dan Hodiyo. In dai za ka ba ni wani labari, na yarda ka ba ni, amma na Shaihu wannan namu ne, sai mu ba wani, muddin dai an yi shi. Gama ko labarin jihadin da ya yi, da biranen da ya gina, da wadanda ya ba tutoci, duk a kaina su ke." Aku ya gyara fiffike, ya ce, "Ai ni ma hakanan, Allah ya ba ka nasara, ko da na ke tsuntsu sai dai in ba wani labarin Shaihu đan Hodiyo, ba wani ya ba ni ba." Da Musa ya ga aku ya tsunke da surutai yana yabon kansa, sai ya ce, "Tsaya! Mene ne na yabon kai? Yabon kai jahilci. Ni ba wani surutu na ja ka ba, balle ka cika mini kunne haka. Cikin labarin mu'ujizozin Shaihu dan Hodiyo yanzu zan gaya maka wanda ba ka sani ba, in kure ka. Ba na ma takalo labarin jihadi ko labarin asalinsa balle ka ce na yi zurfi shi ya sa ka kasa. Shiga kidaya,.sai na gaya maka uku wadanda ba ka sani ba, sa'an nan in shiga in yi azahar, na ji an yi kira." Aku ya ce, "To, ba sai ka fara ba mu ji? In dai lalle an yi shi, ai sai na gani." Musa ya ce, "Da fari ma ba ka san wannan ba. Wata rana, sa'an nan Shaihu dan Hodiyo na yaro, suna zaune a Dagel da shi da ubansa Hodiyo. Ran nan Hodiyo ya shiga ya yi alwala su yi azahar, sai ya kira Shaihu ya ce, "Zo in aike ka Murnona--" Aku ya yi farat ya karbe ya ce, "Wanda Shaihu ya tafi ya dauko littafi har ya dawo uban bai gama alwala ba? Shaihu ya yi alwala ya bi shi aka yi sallar da shi? Alhali kuwa daga Dagel zuwa Murnona zango guda ne ga mai kaya?" Musa ya ce, "Me ka ke faranniya haka don ka gane na fari? In ka san wani ka san wani ne?"" 108 Aku ya ce, "To, fadi mana mu ji, Allah ya ba ka nasara." Musa ya ce, "Wata rana Sarkin Gobir Wuro Nafata ya aika a kira Shaihu dan Hodiyo kamar abin girma-" Aku ya karbe ya ce, "-ashe ko nan ya sa an gina rami mai zurfi, ya kafa wukake da masu ciki, ya sa an rufe ramin da tabarma, don in Shaihu ya zo ya ce ya zauna nan ya faďa ciki ko? Shaihu kuwa ya zo ya zauna, bai fada ba. Sarkin Gobir ya daga wata bindiga da ke gare shi nan boye zai harbi Shaihu, bindigar ta fashe. Sarkin Gobir duk ya kokkone. In ko ba wannan mu'ujizar ba, wata ka ke nufi ka fadi mu ji, Allah ya ba ka nasara." Musa ya ce, "A'a! Ashe dan tsuntsun nan a yi da shi. Ya dubi aku, ya ce, "Ka san labarin Shaihu da madugu?" Aku ya ce, "Shaihu da madugu? Wane labari ne kuwa na Shaihu da madugu wanda ban sani ba? An ko yi shi? Allah ya ba ka nasara, sai ka faďi mu ji." Musa ya се: 109 Labarin Shaihu Dan Hodiyo Da Madugu Wata rana wani madugu yana dawowa daga Gwanja, ya iso Kwara ya shiga jirgi. Suna kan tafiya cikin jirgin nan, sai igiyoyin Kwara suka murda, jirgin ya yi nan tangan tangan, ya birkice. Sai madugun ya kama, "Shaihu dan Hodiyo, ka taimake mu! Shaihu dan Hodiyo, ka yi agaji! Ni dai kam wallahi in na kubuta daga wannan halaka, in na je Sakkwato sai na kai maka sadakar goro kwarya goma:" Yana fadin haka sai ya ga wani ya zo ya kama shi, ya fid da shi duk da kayansa. Ya duba ya ga kowane ne, sai ya ga ba kowa. To, a cikin wannan lokaci kuwa Shaihu Mujaddadi dan Hodiyo yana Sakkwato, yana ba da karatu, kuma yana wa'azi ga jama'a. Sai aka ga ya yi shiru. Can sai aka ga yana matsa hannun rigarsa, ruwa na zuba tsurururu. Jama'ar da ke nan suka nemi bayanin wannan al'amari daga gare shi. Shaihu ya ce, "Wani bawan Allah ne ya nemi taimakommu a Kwara da jirginsa ya kife. Allah ya nufa muka je muka taimake shi." Jama'a suka rike baki suna cewa, "Allah ya sa mu cikin ceton Annabinsa, ya ko ba mu albarkacinku, Mujaddadai!" Bayan an yi kusan wata biyu, ran nan sai ga madugun ya zo Sakkwato, ya debi goro kwarya uku ya tafi wajen Shaihu ya kai masa don ya cika alkawari, ya kuma nemi albarka. Bayan ya gaishe shi, ya gaya masa abin da ya faru duka ga jirginsu sa'ad da suna tsakiyar Kwara, da kuma yadda ya roke shi, ya zo ga taimakonsa, ya ga kamar wani ya zo ya fid da shi, amma da ya duba bai ga kowa ba. Shaihu dan Hodiyo ya tambaye shi wace rana ce wannan hadarin ya auku, kuma nawa ga wane wata ne. Madugu ya fadi ranar da watan, ya lissafa kuma ya fadi kwanan watan sa'ad da wannan al'amari ya auku. Da almajiran Shaihu su kuma suka lissafa, sai suka ga ya kama daidai da ranar da Shaihu Mujaddadi ya yi shiru cikin wa'azi yana matsar hannun rigarsa. Abin ya kara ba da mamaki. Madugu ya fitad da goro ya mika wa Shaihu, ya ce, "Ga abin 110 da na yi alkawari zam ba ka in Allah ya nufa na kubuta." Allah ya nufa na kubuta." Shaihu dan Hodiyo ya yi godiya, ya karba ya ajiye, ya yi murmushi ya dubi madugun, ya ce, "Ai ko ba ka cika alkawari sosai ba. Kwarya goma ka ce, ga shi ka kawo uku." Madugu ya rasa abin da zai ce don kunya, yatai gida ya ciko kwarya bakwai ya kawo wa Shaihu, ya fadi ya yi godiya, Shaihu ya karba, ya raba wa mutanen da ke nan sadaka. Musa ya dubi aku, ya ce, "Ka ji labari daya da ba ka sani ba cikin mu'ujizozin Shaihu Mujaddadi dan Hodiyo. Yanzu kana daya. In dai ga labarun Shaihu ne, in na fara na iya gaya maka goma ba ka sami wanda ka sani ba." Aku ya tuma nan ya tuma can, ya karkata kai, ya ce"Allah Sarki! Ai wannan labari na Shaihu ko na goye ya san shi, amma ka ga duk da haka sai da ka yi babban kuskure cikinsa. Shi ya sa ka ruda ni, na ji kamar ban sani ba." Musa ya сe, "To, ka fara ba? Kai dai wani ba ya yin abin kirki in ba kai ba. Wannan labari na ji shi ya fi sau kam, amma duk ban taba jin inda suka saba ba." Aku ya ce, "Saurara, Allah ya ba ka nasara, abin da na gaya maka duk na labarin Shaihu dan Hodiyo sai ka yarda, Madugu da ka ce ba madugu ba ne, farke ne. Ai ka ji batan da ka yi." Musa ya ce, "Wasalam! Ka ji ka ba? To, me ya raba dambe da fada?" Aku ya yi dariya, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, zage-zage." Sai Musa ya yi dariya, ya yi tsaki, ya ce, "Kai dai ba ka gajiya da surkulle. Ko mutum ya tashi yin hushi da kai sai ka ba shi dariya. Allah ya kai mu dare, kai ka gaya mini naka wanda ba mutum duka ya sani ba. In na bi taka yanzu, har lokaci ya wuce ban yi salla ba."" Aku ya kada fiffike, ya ce, "Allah ya kai mu. Amma ina da fatawa. Don Allah, Shugabana, shi sai mutum ya sa da me da
Chapter 26 · 0% Book details