Sashe 8
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigarsu dila ya ce ya ajiye bakansa daga waje don kada a ce shi maharbi ne. Suka shiga, sai dila ya komo da baya ya boye bakan yaron. Suka tarad da zaki a zaune, duk ga namomin daji sun kewaye shi, ana fadanci. Dila ya fadi, ya yi gaisuwa. Kura ta dubi yaron nan, ta ce, "Kai, ba ka gai da Sarki?" Auta ya ce, "Ke, me ya sha miki kai? Ke kika aiko ni?" Ya duka ya yi gaisuwa. Da suka zauna, zaki ya dubi dila, ya се, "Shi ne wannan da ya dame ku?" Kura ta amshe ta ce, "Shi ne, ranka ya dade. Kuzajje mai kaі kamar kodago!" Zaki ya ce ma Auta, "Kai samari, me ya sa ka ke kashe mana 'yan'uwa?"" Kafin ya amsa tambayar Sarki sai kura ta ce, "Ranka ya dade, raina mu dai ya yi, dubi jikinsa, dan nema, jemamme!" Auta ya durkusa, ya ce, "Ranka ya dade, shin kai ne Sarki, ko kuwa kura?" 26 Da zaki ya ji hàka, sai ya yi fushi da kura, ya ce. "Kada in sake jin kin yi magana a nan. Faďi jawabinka, samari." Auta ya sake durkusawa, ya ce, "Dattijan garimmu suka ce in zo in rika kashe ku, don mu ga idan abubuwan da kura ke fadi na labarinka gaskiya ne." Zaki ya ce, "Me kura ke faďi na labarina?" Auta ya ce, "Mu da nufimmu mu fid da Sarkimmu na mutane, don ba shi da hakuri, mu nada ka, ka yi mulkin dabbobi kuk da mutane baki daya, mu gama kammu mu bi ka, duk abin da ka ce mu yi, mu yi, abin da ba ka so mu bari. To, muna cikin wannan shawara sai ran nan kura ta shigo gari ta ce ka aiko ta, wai ba abin da ke tsakanimmu da kai sai kisa. Muka sake tambayarta, ta ce duk Sarakunan duniyan nan babu azzalumi irinka. Wai da an yi maka dan laifi kadan sai ka ce a kashe mutum. Saboda haka aka ce in rika kashe ku, mu gani ko ka sa a kashe ni. In ka sa an kashe ni, lalle maganar kura gaskiya ce. In kuwa ka yafe ni, kura ta zama makaryaciya." Zaki ya dubi kura, ya buga mata tsawa ya ce, "Wa ya aike ki ga mutane?" 27 Ta zabura, zawo na fita, ta ce, "Karya ya ke yi, ban taba shiga gari ba." Auta ya ce, "Wa ke maki karyar, zaki da kansa? Kin manta har muka ba ki kujera kika zauna, don girmamawar Sarki da kika се ya aiko ki?" Za ta yi magana zaki ya zabura, ya sa gaba ya banke ta, duk namun daji suka hau mata, mai yaga na yi, mai cizo na yi, har suka kashe ta. Zaki ya sallami yaron nan. Ya ba shi kaya mai yawa irin wanda su ke kwacewa daga fatake. Yaro ya yi godiya, ya ce zai je ya gaya wa mutanen gari abin da ya auku. Wannan shi ya sa ko yaushe in ka ga zaki a daji ka durkusa, ka ce, "Ranka ya dade," ba zai cuce ka ba. Musa ya duba haka, sai ya ga gari ya waye. Bai ko tsaya ba ya ji ko labarin ya kare, ko bai kare ba, sai ya yi tsaki, ya juya ya shiga gida. Yinin ran nan duk ya ki ko zuwa wurin aku, har magariba ta yi. Bayin Sarki suka ci abinci suka zauna hira, sai can barci ya kwashe su. Da Musa ya ji alamar bayi sun yi barci sai ya tasam ma wajen aku. Da hango shi sai aku ya bushe da dariya. Musa ya dube shi, ya ce,'Me ka ke wa dariya haka, kai kadai kamar mahaukaci?" Aku ya ce, "Ai ba ka san abin da aka yi ba jiya da dare. Shigarka ke da wuya, sai na ji bayin can naka na babban zaure suna hira, Sarkin Gida na yi musa tatsuniya. Da na ga ba na jin barci, ni kuma na tafi in taya su. Da Sarkin Gida ya kare tatsuniyoyinsa, ni kuma na ba su labarin. wani bakauye da wadansu 'yam birni." Musa ya ce, "Ashe Sarkin Gida tsofai-tsofai da shi nan, har ya iya tatsuniyoyi?" Labarin me ka tarar yana yi musu?" Aku ya ce, "Ba wani labari mai dadi ba ne, tun ina yaro na san shi. Kokawa da aka yi cikin labarin ne, in na tuna ta ke ba ni dariya." Musa ya ce, "Yaya suka yi?" Aku ya ce: 28 Labarin Sahoro Da Sahorama Wai akwai wani saurayi ne wanda a ke kira Sahoro. Kullum bá ya tabuka wani aiki sai ya kora akuyarsa, ya kai ta bakin rafi ta yi kiwo, da maraice ya kwanto ta. Nonon akuyan nan shi ne abincinsa, ko ya sayar ya sayi wani abu, ko ya sha hakanan. In akuyar ta yaye kuwa, sai ya sayar da ita, ya sayi wata mai da. To, ba abin da ya miskile shi sai kiwon akuyan nan. Kullum ya dawo gida sai ya ce, "Wash, ba shakka kiwon akuya ba aikin da ya sha kansa kan wahala! Haba, lokacin nan yanzu akwai abin da ya fi mutum ya sami inuwa mai sanyi, ya kishingida, ya yi ta barci? Amma ba dama, dole ne mutum ya bi ta, in ko ya ki, ta fada wata gona ta shirga barna a ci mutum tara, ko kuwa ta ki dawowa kura ta sami kalaci. Kai, ya kamata dai in tuna yadda zan sanyaya wa raina daga wannan azaba. Rai fa an ce dangin goro ne, ban iska ya ke so." Yana nan kullum yana zulumin wahalar kiwo, sai ran nan ya ce, "Ah! Na san dabara, ba abin da ya fi sai in auri Sahorama. Ga ta da akuya daya ita kuma tana kiwo, ka ga in na aure ta sai ta rika gamawa da tawa, ni ko in samu in rika taba dan kailula." Sai ya nemi Sahorama aure. Iyayenta suka ce, "Am ba ka. Dа ma da Tukura da Bako duk Umbutawa ne." Aka yi aure, ta tare, ta shiga hidimar kiwon awakinsu biyu. Don ba su da wani abinci sai wanda suka samu daga gare su. Sahoro ya yi ta shara barci a natse. Ba a dade ba kuma Sahoroma ta ce wa Sahoro, "Maigida, ni fa na gaji da wannan irin wahala, kudaje na cizona, ina tuntube. Don Allah, dubi jikina. Da na zo nan gidanka ina sheki, duk yanzu na fara kirci don cizon kudaje. Kai, ba na yarda in tsofad da kaina tun ina gabar kuruciya, sai mu sake dabara." Sahoro ya ce, "Wannan batu naki ba makankara. Ni ma fa na ga kin fara baki, ni ko dubi yadda na fara ajiye taiba. To, yaya zan yi da su?" Sahorama ta ce, "Sai mu ba Dabo, ya ba mu amiya guda, mu ajiye a bayan gida, in zuma ta shiga ta yi saka, mu rika diba muna 29 samun abinci. Ka ga ba ruwammu da kiwonsu, balle mu wahala." Sahoro ya ce, "Kai, ai ko kin samo dabara, ga shi kuma ko ba a faďi ba zuma ta fi nono dadi." Sai ya sa matar ta je ta yi magana da Dabo. Ya yarda da musayar, don ya ga da riba. Ya ba su amiya guda, suka yi ta samun zuma daga ciki suna sha. Suka sami wani gora suka cika, suka rataye. Sahoro dai in ya kwanta tun da dare, ba ya tashi sai rana ta take. Ya kan ce wai tashi da wuri shi kan hana gira tofo, kuma ya kan sa dundumi. Ran nan ya farka daga barci da rana tsaka, sai ya ga matarsa ta dauko goran zuman nan, za ta diba ta yi musu gari su sha. Sai haushi ya kama shi, ya ce, "Ku fa mata barnarku ta fi ku! Dubi goran zuman nan har ya kusa karewa. Watau zuman nan ta kare ne, har za ki fara dibar ta gora? Abin da na ga ya fi sai mu sayar da goran zuman nan mu sayi kaji da zakaru, su rika yi mana kwai suna kyankyashewa." Sahorama ta ce, "In ko haka ne sai mu sami wani yaro wanda zai rika zuba musu ruwa da hatsi. Ni dai ba na iya wannan jidali kullum kwanan duniya." Sahoro ya ce, "Lalle kiwon kaji wahala ne ja wur. Yaran yanzu kuwa kowa ya san su a kan ragwanci. Yanzu ko, ko mun yayo wani yaro don ya rika lura da kajin, in mun saya sai ki ga wasa ya dauke masa hankali, ba ya wani abin kirki." Sahorama ta ce, "Ko wane yaro muka dauko in ya ki yin aiki sai in dauki sandan nan" (ta sa hannu ta dauki wani guntun itace), "in sheme shi, tau a kai!" Sai ta kwantara wa gora ice, Gora ya fashe, 'yar zumar da su ke takama da ita ta tsiyaye. Sahoro ya ce, "Shi ke nan, ta faru ta kare, an yi wa mai dami 30 daya sata! Da kajin da za mu saya, da yaron da za mu dauko, duk ga su nan sun malale a kasa. Amma dai na isa barka, da sakainan nan da ta yi tsalle ba ta fada mini a kafa ba." Ya dubi matar, ya ce, "Sa hannu, kwashe wannan da ke gudu kasa kafin kasa ta shanye, don mu sami na farawa, kada yunwa ta sa in gintse barcina tun ban koshi da shi ba." Sahorama ta shiga sa hannu tana kwashe zuma, tana zuba dan abin da ta samu cikin wata kwarya, tana lashe rabi tana ba mijin labari tana cewa, "Abin nan fa da na yi yanzu amfanimmu zai yi nan gaba. Don na taba jin wata rana an gayyaci kunkuru wajen aure, don rashin saurinsa da ya tashi bai kai gidan ba sai bayan watanni. Da ya isa ya tarar ana sunan dan amaryar da ya zo bikinta ta haifa. Da aka gaya masa ya ce, "Ba kome, sauri shi ke haihuwar nawa!" Sahoro na kwance bisa gado yana kallonta, tana ta shan zuma da wayo, tana zuba masa surutun banza. Sai haushi ya kama shi, ya ce mata, "Wane labarin banza ki ke ba ni haka, ba kai ba gindi? Wayon a