← Book details Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 31

Sashe 4

Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ji wani abu, ha ha ha! Duk suka waiga firgigi, sai suka ji daga cikin keji an ce, "Ai ga ta nan. Da ma na gaya maka, ka tashi kashe ni, kai ne ba ka sani ba, ba irin magana kamar tamu a ke rainawa ba." Sarki bai sami ta cewa ba. Aku ya ce, "Ko yanzu in ka bi shawarata allah ya kyauta, ba wani abin da zai bata maka rai. Sarki ya dubi aku da fushi, ya ce, "Ka rufa mana baki nan! Wata shawara gare ka?" Musa ya sa baki ya ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara, matambayi ai ba ya bata, ya fadi mu ji." Sarki ya ce, 'To, fadi, in ko shawarar taka ba ta fita ba, ina murde maka wuya, kowa ya huta." Aku ya ce, "Yanzu Sarkin Sinari ya kusa kawowa kadarkon Kimba, nufinsa ya biyo ta tsakanin dutsen Kimba da na 7 Ubandawaki ya kewayo ta gabas ya fada wa birni ta inda ba a tsammaninsa." Sarki ya ce, "Cikin 'yan gari ma akwai wani mahalukin da ya san wannan hanya, balle Sarkin Sinari?" Aku ya ce, "Kai dai ka ji abin da zan gaya maka. Yanzu maza ka koma gida ka aika da 'yan kwarbai su tsare makurdin nan da ke tsakanin dutsen Kimba da na Ubandawaki. Kome yawan rundunarsa, ko mutum goma masu karfin zuciya sa iya mai da shi baya a wannan wuri, kafin ya kewayo ma ka shirya uwar yaki." Sarki ya yi tsaki. Musa ya ce, "Dan akun nan ya san abin da ba mu sani ba, sai a bi shawararsa mu gani." Ko-da-ya-ke abin nan da aku ya fadi Sarki na jinsa kamar tatsuniya ce, duk da haka tun da Musa ya sa baki sai ya hau, suka koma gida, ya zabi 'yan kwarbai guda dari ya aika da su inda aku ya misalta masa. Ya kuma ta da manzanni ya aika da su kudu da arewa, gabas da yamma, a gaya wa mutane su yiwo harama su zo maza da shirin yaki. Makera kuma suka shiga gyara makamai. Ana nan bayan kamar kwana biyar sai ga wani daga cikin 'yan kwarban da Sarki ya aika ya zo a sukwane da bushara, ya ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara, ai wannan dabara da ka yi ta fita. Shekaranjiya da hantsi muna nan mun yi kwanto inda ka ce mana, sai muka hangi kura ta toshe sama, sai tsinin masu kawai ka ke gani suna wal wal wal. Ga masu dawaki da dakarai bilahaddin, muka hanga har iyakar ganimmu, ba mu ga karshensu ba. Muna nan dai sai da muka bari goshin yaki ya kawo dab da mu, sa'an nan muka yi ta sako musu kibau kamar ruwan sama. Na gaba suka juya da baya suka gamu da wadanda ke biye, abin ya cude, ga 'yar hanya karama, dawaki suka yi ta zallo suna fada wa junansu. Mu ko dai sai zuba musu kibau mu ke, na bisa na ta sullubowa kasa, dawaki na tattake su. Cikin na gaban nan sai dai dai suka sami komawa wajen uwar yaki. Jim kadan kuma sai ga wadansu suka taso wai za su yi mana sukuwar salla. Ba dama, don hanyar ta cika matsatsi tsakanin duwatsu. Muka yi musu yadda muka yi wa na farko. Aka yi ta aiko wadansu, muna yi musu hakanan, har la'asar ta yi. Da suka ga ba dama suka koma, suka bar gawawwakin 'yan'uwansu nan, abin sai wanda ya gani!" Ko da Sarki ya ji haka, sai ya yi kamar ya ce kaka don murna. Ya shiga ya gaya wa aku, ya yi ta gode masa, ya yi kamar ya dauke shi ya hadiye shi. Nan take ya dauko jaka biyu ya ba Balarabe, kuďin aku. Ya kawo ingarma taka hau ya ba shi, ya kara masa da bayi bakwai, ya ba shi kyankyandi goma sha biyu na tufafi, ya sallame shi ya tafi. 8 Cikin daren nan sai ga Barakai ya komo ya gaya wa Waziri abin da ya faru, ya ce, "Mu ke kan gaba, sai kawai muka ga ana ta zubo mana kibau, har aka sami dokina ban sani ba, sai na ga kawai mun zube. Ni ko da na ga haka sai na kwanta karkashinsa kamar na mutu. Na yini nan ba motsi, ana ta yaki bisa kaina. Da dare ya yi tsaka, na ji sun yi shiru, sai na sulale na dawo." Waziri ya yi masa barka, ya ce, "In ji ba a gane kai ne ba?" Barakai ya ce, "Na tabbata ba wanda ya gane ni." Waziri ya се, "То, madalla. Amma ina mamakin yadda Sarki ya gane ta nan za su bullo." Barakai ya ce, "Ni ma hakanan. Bakina dai ban yi da kowa ba." Waziri ya ce, "Lalle mutanen Sinari akwai munafukai. Amma ba kome, gobe ma rana ce." Bayan kamar kwana uku gayyar yaki ta taru, gari ya cika da dawaki da dakaru har ya amaye, kauyukan rabe da birni ba wanda bai cika ba. Da Sarki ya ga duk an hallara, tun da sassafe sai ya kira Waziri ya bar shi tsaron gari. 9 Waziri ya duka, ya ce, "Na ko karbi amanan nan taka da hannun dama." Yana 'yan koke-koken munafunci. Sarki ya tashi ya shiga gida, ya kira wadansu bayinsa amintattu guda goma sha biyar, ya bar su tsaron gidan, ya ce su lura kada su Musa su fita waje sai sa'ad da Allah ya dawo da su lafiya. Ya kuma tafi ya kira su Musa wajen aku, ya ce musu, "In kun kuskura kuka fita wajen gidan nan bayan ba ni nan, ban yarda muku ba. Kuma kome za ku yi ban yarda muku ku yi shi ba, sai kun zo kun shawarci akun nan. Abin da ya ce muku kuwa, ko da kuna tsammani kan kuskure ne, kada ku ketare shi." Yara suka fashe da kuka suna cewa, "Baba, mun ji abin da ka ce duka, ma ko bi." Sarki ya juya wajen aku, ya ce, "Kai kuma, ga amana nan, in ka ci amanata, to, Allah ya isa." Aku ya ce, "Hakanan ne, ranka ya dade. In Allah ya so kuwa, ka tarad da abin da ka ke so." Sarki ya ce, "To, madalla." Zai tashi ya ce, "Af, jiya kuwa na ga wani da wata macen aku, na saya don in gama ku tare, ta rika debe maka kewa." Ya aika aka kawo ta, aka gama su. Aku ya yi godiya, suka yi sallama da Sarki. Walaha na yi, aka buga tamburan tafiya. Sarki ya taka ya hau, sai Waziri ya zo ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ko ka sha'afa ne? Ka yi alkawari duk yakin da ya fara aukuwa da Mahmudu za a." Sarki ya kawo iya wuya, ga bakin cikin rabuwa da iyali, ga kuma wata maganar banza. Sai ya sa baki ya kira Mahmudu ya ce, "Ga doki nan, hau mu tafi, da kai za a." Mahmudu ya dare doki. Musa ya ce, "Ni ma zan tafi!" Sarki ya ce. "Ba na zuwa da kai." Musa ya fashe da kuka, ya cę ba ya rabuwa da Mahmudu. Sarki ya daka masa tsawa ya koma gida, ya kira Sarkin gida da bayin nan da aka bari tsaro, ya ce, "Ku lura kada ku bar Musa ya ko leko waje, in wani abu ya same shi ina yanka ku!" Suka shiga da shi. Runduna ta dunguma, aka taryi inda Sarkin Sinari zai fito. Da Waziri ya ga an raba Musa da Mahmudu, ga shi kuma Sarki ba ya nan, sai ya tafi gida ya yi ta murna, yana tsalle-tsalle. Ya shiga tunane-tunanen abin da zai yi ya halaka Musa kafin Sarki ya dawo. Domin in ya samu ya kashe Musa, kome ya faru wurin yaki shi ke bisa. In Sarkin Sinari ya ci nasara, bukata ta biya, in ko Sarki Abdurrahman ma ya ci, duk daya, don ko ba jima ko ba dade shi ne zai gaje shi. Da ya ga kurar yaki ta bace, sai ya kira wadansu katti hudu cikin bayinsa wadanda ya amince da su, ya ce yana da wata 10 bukata, wanda duk ya biya masa ita zai 'yanta shi. Bayin nan suka dauka gaba daya, "Fadi, yanzu ka ga aiki da cikawa!" Waziri ya ce, "Ina so ku kashe mini Musa. Yana nan cikin gidan Sarki an kulle shi, an sa duk bayin gidan su tsare shi." Bayin nan suka ce, "Af, in haka ne yaya za mu yi mu kashe shi?" Waziri ya ce, "In dai kun kasa kunne kwa ji, aiki a ke so ba surutu ba. Yanzu duk hankalinsa yana ga Mahmudu dan'uwansa. Na san lalle in kafa ta dauke, yadda aka yi duk saı ya yi kokarin da ya fito don ya bi shi. Sai ku nemi buhu, in dare ya yi ku tafi kofar gidan Sarki, ku sami wuri ku make. Da kun gan shi ku kama shi, ku rufe bakinsa, ku tura shi cikin buhu ku daure, ku je da shi kogi ku jefa." Bayi suka ce, "An gama." Musa ya yini ran nan sukuku. Mutane suna tsammani uban ya ke tunawa, saboda haka ba su koma ta kansa ba. Da magariba ta yi Sarkin Gida ya kulle kofofi duka, ya miko wa Musa mabudi ta taga, yadda Sarki ya ce ya rika yi kullum. Ya koma zaure wajen bayin nan da aka bari, suka yi ta hira har kusan asuba, sa'an nan barci ya kwashe su. Duk abin nan kuwa Musa bai yi barci ba, yana jira bayin nan su yi, ya je ya gaya wa aku ya bar shi ya fita ya bi su Mahmudu. Da ya ji sun yi barci, sai ya shirya, ya dauki mabudan nan, ya shiga damaru, ya dauki garkuwa da mashi, ya nufi wurin aku. Sai ya tarad da aku namijin, watau wanda aka fara saye mai sihiri, yana barci. Sai ya ce, "Af, tun da wannan ke barci bari in tambayi matar, da Bako da Tukura ai duk Umbutawa ne." Ya tsaya gaban macen aku, ya ce, "Na zo in gaya muku ne don ku sani, za ni bin Mahmudu, duk abin da zai same shi ya same mu tare." Da akun nan
Chapter 4 · 0% Book details