Sashe 30
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
kan wannan nasiha. Sa'an nan Sarki ya tashi tsaye, ya ce wa jama'a, "To, mun ga inda wadannan tasu ta kwashe. Amma ina tambaya, shin don me a ke yin Waziri?" Jama'a suka ce, "Don ya rika taimakon Sarkin gari shawarа, yana kwabe abin da zai cuci jama'a, ba kamar wannan ja'iri ba. Allah ya kiyashe mu da halinka!" Sarki ya ce, "In don haka ne, na nada wannan aku Wazarina. Da shi zan rika shawara." Ya dubi mutane, ya ce, "Ko kuwa kun ga bai isa a yi shawara da shi ba, don yana tsuntsu?" Jama'a suka ce, "Wane irin isa? Wanda ya yi wadannan abubuwa a ce bai isa ba? Wannan tsuntsu ai baiwa ce Ubangiji ya nufe mu da ita, wa ke da ikon jayayya da nufin Allah? Mu dai wallahi mun so, mun so." a Sarki ya dubi dogarai ya ce, "A kama Waziri, a daure shi cikin jaka da ya bayar a sa Musa, a tafi da shi a jefa cikin kogi, yadda ya yi niyyar yi wa Musa. Ku kuwa Sarakunana da makada, a tafi kai Waziri Aku gidan Waziri, a fid da matansa na aure, sauran ko duk abin da ke gidan an ba shi." Sarki ya tashi ya shiga gida. Duk fada ta yamutse, wadansu suka nufi wajen da za a kashe Waziri, wadansu suka bi sabon Waziri, ana ta goce ganguna da kakaki. Aku kuwa yana bisa wata karaga ta zinariya, an sa laima, katta na dauke da shi. Sai makada ke ta binsa suna waka: Haba jama'amu, ku zo mu yi caffa, Gunsa Waziri, mazajen aiki. Masu rabo da yawa mai ba mu! Sannu da sirdi, tsuntsun kirki! Da ba don shi ba, masu fasaha, Da yanzu da muna Sinari. Ga wani sauna, don sakarci, Ya yi butulci, ya bashe shi. Ikon Allah wa zai ki shi? Kowas saba yai jahilci. Ka sai mana doki, baba Waziri, Muje mu gwada wa mutan Sinari. In ba donka ba, mai cika aiki, Da wani mun ga irin bautanshi. Masu fasaha, masu basira, Mai tauhidi, Sarkin ilmi! Ga ni a durkushe, na roke ka, Ya Allahu ka gafarce ni. 125 Aka kai aku gidan Waziri, ya debi dawaki uku daga cikin wadanda ya samu gidan Waziri, ya ba makada da suka rako shi. Ya sa bayi su yi ta gadinsa. Aka yi ta shagalin sarauta har kwana bakwai. Da aka natsa, Sarki ya sami matan aku guda hudu ya sai wa sabon Waziri. Duk inda Sarki ya ji wani na da aku, in mace ce, sai ya sayo ya kawo wa Wazirinsa, watau kwarakwarai. Ana nan, bayan 'yan kwanaki daya daga cikin matan nan na Waziri Aku ta yi kwai. Bayan kamar kwana ashirin ta kyankyashe wani dan aku namiji. Ya sa masa suna Fasih, ya sa wani bawa ya yi ta kiwonsa. Waziri Aku ya yi zamansa, yana tą muskakar sarauta. Ba уа shan ruwa sai da sukar, shinkafa ko ba ya cinta sai an dafa an sa gishiri da mai: 126