Sashe 11
Magana Jiri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai a banza, yadda ya tashi halaka Sarkin Zairana." Musa ya waigo, ya ce, "Ina ne Zairana kuma? Zulumin mene ne haka ya sami Sarkin, har ya tashi halaka?" Aku ya ce, "Yallabai, me ka mai da zulumi ne?" 39 Labarin Sarkin Zairana Da Sarkin Bokaye Gara Akwai wani Sarki a Zairana wanda Allah ya nufa da kiba, abin har ba iyaka. Idan ka gan shi sai ka ce giwa, in ya zauna ba yadda zai yi ya ga cibiyarsa, dokin duniyan nan duk ba mai iya daukarsa. In ya tashi daga zauren gidansa zai shiga, mutum ya yi tafiyar loko biyu Sarkin nan bai isa ba. Sarki fa duk abin duniya ya dame shi bisa ga wannan kiba, shi kuwa ba abin ya ki cin abinci ba ya mutu. Saboda haka ya tara bokayen kasarsa, ya ce su yi kokari su samam masa maganin da zai sha ya rage kiba. Bokayen suka shiga aikinsu. Kowa sai ya sassako wannan itace, ya gino wannan sauya, ya kai wa Sarki. Ya yi ta sha, amma a banza. Maimakon ya ragu sai karuwa ya ke kullum safe, sai ka ce ma maganin ya kara kiba su ke ba shi. Da Sarki ya ga haka sai ransa ya kara baci, ya yi kamar ya kashe kansa don haushi. Ga duniya Allah ya ba shi, kiba ta hana shi jin dadin cinta. Yana nan haka sai ya ji labarin wani boka wanda a ke kira Gara Mai Aburkuma. Sarki ya aika aka kira shi, ya bayyana masa bakin cikinsa. Ya ce in ya warkad da shi kuwa zai yi masa kyauta har ya kasa godiya. Gara ya се, "Tо, Allah ya taimake mu. Amma in ka yarda,. ranka ya dade, ina so a ba ni kwana uku in je in shawarci Aburkuma, Inna uwa ma ba da mama, abin da muka yi da ita duka zan zo in gaya maka." Sarki ya ce, "To, je ka, na ba ka iznin kwana uku, amma kada ka wuce haka." Gara ya yi ban kwana, ya tafi. Ya yi ta tunanin inda zai fito wa Sarki ya yaudare shi. Ya san dai, in ba wautar Sarki ba, wane boka ne zai iya ta da hukuncin Allah? Bayan kwana uku sai Gara ya komo wajen Sarki, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, na dawo." Sarki ya ce, "To, ina labari?" Gara ya ce, "Allah ya daukake ka, ai sai a bar kaza cikin gashinta, al'amarin ya tayar mini da hankali."" 40 Sarki ya ce, "Me ka gani, na ce. Fada mini mana in ji." Gara ya ce, "Allah ya ja zamaninka, ai ba na iya fadin abin da Inna ta gaya mini. Saboda bakin cikin al'amarin, jiya, na rantse har da rawaninka, ban yi barci ba. Abin da na gani ya fi sai a bar wata wahalar neman magani, a tasam ma istingifari." Sarki ya fusata, ya ce, "Yau ga zancen banza. Na ce ka gaya mini abin da ka gani, ka tsaya kana kewaye-kewaye." Gara ya ce, "Allah ya yi wa Sarki rahama, Inna ta ce saura kwana arba'in ka riga mu gidan gaskiya." Sarki ya fusata, ya ce a kama shi a daure. Dogarawa suka cafe shi. Gara ya ce, "Da ma abin da na ke gudu ke nan da gaya maka gaskiya." Aka dai iza keyarsa zuwa gidan kurkuku. Sarki ya shiga zulumin abin nan da Gara ya fadi, ya ce, "Na san Gara fa shahararre ne bisa ga al'amari da aljannu. Ba abin da ya fi dai sai a rika kidaya kwanakina da ya fadi. In sun cika arba'in na ga ban mutu ba, na san Gara karya ya ke yi. In kuwa na ga bayan kwana talatin da takwas, ko talatin da tara, na fara 'yar mashasshara na san ni tawa ta kare."" Wannan zulumin da ke ran Sarki fa ya sa ya tsunke. Ko abinci ba ya iya cin abin kirki, balle ma ya faranta ransa da wadansu kawace-kawacen duniya. Saboda haka kullum sai ramewa ya ke don zulumi. Duk mutane suka rasa kansa suka rasa gindinsa. Bayan kwana talatin da wannan magana sai tashin hankalin nan ya yi masa yawa, har ya sa kansa ya rika ciwo. Rana ta talatin da tara da ya ji ciwon kan na karuwa, sai ya kira dansa ya danka masa mabuďin taskoki, ya yi ta yi masa wasiya, yana gargadinsa yana cewa su tasu ta kare. Yaro bai san abin da ya ke nufi ba, tsammani ya ke don ya fara tsufa ne ya ke so ya nuna masa al'amuran mulki. Ana nan dai kwana arba'in suka cika, Sarki na jiran mutuwa, bai ga ya mutu ba. Kwanaki dai suka kai kwana arba'in da biyar, Sarki bai ga ya mutu ba. Sai ya áika aka zo da Gara daga gidan sarka, ya се, "Ка сеe bayan kwana arba'in zan mutu, ga shi yau kwana arba'in da biyar da maganar, ban mutu ba." Gara ya ce, "Da ma maganin ka rage kiba ka tambaye ni, to, karyan nan da na yi na ce'saura kwana arba'in ka mutu ita ce maganin. Ka tambayi kowa nan garin ka ji in ba ka rage kiba ba."" Da Sarki ya ji haka, sai hankalinsa ya kwanta, ya bushe da dariya, mutane suka yi kyakkewa baki daya, suka ce, "Lalle Gara ya isa dan duniya." Gara ya ce wa Sarki, "Ba abin dariya ba ne, sai ka ba ni abin da ka alkawarta." 41 Sarki ya sa aka yi ta kawo masa riguna da zannuwa da wanduna, ya kuma ce duk mai kaunarsa ya yi wa Gara kyauta. Mutane suka yi ta zuba masa kudi, tun yana godiya har ya fashe da kuka don murna. Sarki ya sallame shi, ya kwashe kayan da aka ba shi duk, ya tafi. Kullum in an ta da labari, sai Sarki ya yi ta yi wa kansa dariya in ya tuna abin da ya yi daren da kwanan nan arba'in za su cika, da ya yi ta yawo tsakar gida shi kadai, ya kai gwauro ya kai mari, yana ta salati ga Fiyayyen talikai. Aku na kare wannan labari, sai Musa ya ji zakara na ta cara, gari ya waye. Ya rasa abin da zai ce wa aku ya huce, sai ya shiga gida, ya yini ran nan bai ce wa kowa kome ba. Magariba na yi, sai ga 'yar tsohuwan nan ta dawo, Waziri ya aiko ta da takarda wai daga Mahmudu, ta kawo wa Musa. Musa ya karba ya karanta, ya cе, "Allah wadan dan abin nan da ke hana ni fita." Tsohuwa ta ce, "Yanzu haka, yallabai, duk karkaran nan da mace da namiji ba ka jin wani abu sai Mahmudu. 'Yam mata ma yanzu ba su da wata waka sai ta Mahmudu." Musa ya ce, "Har waka 'yam mata suka yi masa? Don Allah, in kin iya, rera mu ji." 'Yar tsohuwa ta karkace kai, don iya kissa ta fara wakan nan, ba da ko ta taba jinta ba: Jama'a ku zo ga kallon Mahmudu, Wanda ya wuce wargi. Ya fi karfin sai gobe, Ya wuce mai wargi. Shi ne ya kori Sinarawa, Har ya kashe musu Sarki. Ya fi karfin sai gobeе, Ya wuce mai wargi. Mahmudu wa ga Musa, mazaje, Da sunka kawo karfi. Ya ki wargi dattijo, Ba ya son mai wargi. Zaman gida na raggo, Sai dan da ke gudun mai karfi. Dan Sarkin da ke cikin mata, 42 Shi da su ana nan daidai. Ya fi wargi, Mahmudu, Ba ya son mai wargi. Da Musa ya ji wannan waka sai idandunansa suka jujjuye. Tsohuwa ta tashi, ta tafi wurin Waziri ta gaya masa. Waziri ya yi mata kyauta. Da asubahin farko, Musa ya yi damara, ya dauki wata babarbara, ya tafi wajen aku, ya ce, "Zan tafi, ko ka yardá, k ba ka yarda ba." Aku ya duka, ya ce, "Yallabai, ina da ikon hana ka? In dai ka fita, ka sami dan kwabo ka yi sadaka. Allah ya ba da sa'a!" Musa ya ce, "To." Ya juya zai fita, aku ya ce, "Af, yallabai, ko za ka dakata kadan in fita ta taga in samo maka wani maganin karfe da na gada daga kakana? Ka san fa mazaje ba a tasam musu ba shiri." Musa ya ce, "Gaskiyarka. Yi maza ka debo, amma kada ka tsaya." Aku ya fita ta taga, ya sami wata itaciya ya haye, ya yi zamansa. Can da ya ga asalatu ta kusa, ya debo ganyen itaciyar, bai san ma ko wace irin itaciya ba ce. Ya taso fir ya kawo wa Musa. Musa ya karba, ya се, "Amma kuwa ka tsai da ni."" Aku ya ce, "Ba ka san iyakar inda na tafi ba ne, da ba ka zarge ni kan dadewa ba. Ka sa a dafa maka, ka yi wanka da shi, ba dai karfe ba, sai wani abu." Musa ya ce, "Ka ji asalatu ta yi." Aku ya cе, "Bа kome ka tafi gobe, zuwa da wuri ai ya fi zuwa da wuri wuri. Kafin a kare kiran salla bari in gaya maka wani dan labari guntu." 43 Labarin Kyanwa Da Bera Akwai wata itaciyar kuka a bayan wani gari. A gindin itaciyan nan akwai wani bera, a cikin kogonta kuma ashe akwai wani muzuru na kwana. Kukar kuwa cikin gonar wani mutum ta ke. Kullum dare sai muzurun ya fito ya je ya yi ta wa mutumin nan barna. Da mutumin ya ga haka, sai ya samo wata raga ya yi tarko, don ya kama kome ke shiga ke yi masa barna. Allah ko ya ba shi sa'a. Da asalatu ran nan muzurun ya ga beran, ya zabura zai kashe, sai ya fada cikin tarkon, ya yi ya yi ya fita, ya kasa. Bera kuwa da ya waiga ya ga tarko ya kame muzurun, sai ya yi rawa yana murna. Yana nan yana murna, ya duba haka cikin kara kusa da raminsa, sai ga wani maciji nan yana jira ya rabo da muzuru ya hadiye shi. Ya duba sama don ya hau, sai ya ga shirwa na kewaya, tana jira ya motsa ta fyauce shi. Bera ya tsaya, ya rasa inda za shi. Abu ya zama masa gaba siyaki baya damisa. Yana nan sai ya tuna