← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 44

Sashe 8

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana jin fitar sa har ƙaran rufe ƙofar da ya yi ta ƙofar gidan hakan ya nuna ficewa ma ya yi daga gidan. Komawa kan gadon ta yi ta kwanta bata san lokacin da wani kuka ya ƙwace mata ba, dama al'adar ta ce matsawar ranta ya ɓaci wani lokacin sai ta yi kuka in ba haka ba bata samun sassauci a zuciyar ta.

Ta jima tana kukan sai da ta ji zuciyarta fess sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya. Tun tana saka ran dawowar sa amma shiru babu shi har ƙarfe goma ta gota amma bai dawo ba.

Har sha ɗaya saura idon ta biyu, daga nan bata san lokacin da bacci ya ɗauke ta ba. Can cikin bacci ta yi juyi ta falka sai kuwa abin da ya faru ya faɗo mata da sauri ta tashi tana ƙarewa wajen da Aminu yake kwance kallo ganin babu shi babu alamar sa. Mamaki ne ya ɗarsu a zuciyar ta tana tunanin shin bai dawo ba ko dai bayi ya shiga?.

Sakkowa ta yi daga gadon bayan ta duba wayar ta ta ga ƙarfe uku da kwata, wutar ɗakin dama a kunne ta bar ta don haka bayin ta nufa ta ɗan ƙwanƙwasa jin shiru ta tura ƙofar amma sai ta ga wayam tsoro da mamaki suka ƙara rufe ta ko ƙofar bata rufe ba ta juya da sauri nufi wayar ta lambar sa ta kamo ta shiga kiran sa don kawai sai ta ji hankalin ta ya tashi don tuni ta manta da abin da ya mata, wataƙila ko son da take masa ne ya danne laifin nasa ko dai ruɗun da take ciki ne ya mantar da ita komai.

Sai da ta kira sau uku wayar tana shiga amma ba a É—auka ba. Har ta yanke shawarar ta daina kira tun da ba a É—auka ba sai ta ji ba za ta iya ba hakan ya sanya ta sake kira sai da ta yi sau biyu nan ma babu amsa.

Bata yi tunanin kiran É—aya daga cikin yayun nasa a waya ta sanar da su ba sai kawai ta yanke hukuncin ta je part É—in É—aya daga cikin su ta sanar da shi kar wani abu ya biyo baya a ce da gangan ne bata faÉ—a ba cewa bai dawo gida ba.

Tana fitowa falon da yake a kunne ta bar wutar falon amma sai ta ga a kashe don ko ta ɗakin bata kashe ba lokacin da za ta kwanta tun da ta san bai dawo ba, ganin ta falon a kashe sai ta yi mamaki matuƙa.

Kunnawa ta yi haske ya gauraye falon kamar an ce ta waiwaya sai kuwa ta gan shi kwance saman doguwar kujera yana bacci hankalin sa kwance. Baki sake take kallon sa ganin ya shigo da wani sabon salo wai kiran sallah da usur.

Bata tashe sa ba sai kawai ta kashe fitilar ta koma ɗakin har za ta kwanta sai ta yi alwala ta yi sallah raka'a biyu ta yi addu'a ta koma ta kwanta a ranta tana mamakin wannan sauyin da ya shigo rayuwar su tun da tsawon lokacin nan basu taɓa raba makwanci da shi ba, amma yau ga shi ya raba musu makwanci.

Da asuba ta tashi ta yi alwala ta tafi falon ta shiga tashinsa ita ma da bata gajiya.

"Mai zan miki ne wai da kike katse mini bacci?" Ya tamabaya a ƙufule.

"Sallah aka kira"

"Za a saka mu kabari É—aya da ke ne? Ba kin ne kin faÉ—awa su Yaya Sule ba na sallah ba to yanzu ma sai ki je ki ce gani nan kwance ban yi sallah ba sai su zo da bulala ko?"

"A'a" Ta ce cikin sanyi murya tana jinjina irin yadda yake mata magana cikin hargagi kamar dai ba wannan Aminun da yake son ta ba yake nuna babu mai raba su sai mutuwa babu wanda zai shiga tsakanin su, yana faɗa mata idan sun yi aure za su huta ba za su taɓa yin faɗa ba ba zai taɓa ɓata mata rai ba ba zai taɓa mata kishiya ba da ita kaɗai zai rayu.

Amma ga shi tun ba a je ko ina ba ayyukansa suna ƙaryata maganar sa, na farko dai ya ce ba zai mata kishiya ba sai ga shi tun auren bai je ko ina ba ta kama shi yana kallon hoton mace, sannan ga shi a jiya ya shuka mata kalmomin rashin mutunci tare da gasa mata baƙaƙen maganganu.

"Tun da kowa kabarin sa da ban ki je ki ji da naki kabarin" Maganar sa ta katse mata tunani, yana gama faɗar hakan ya juya mata baya ya kwanta. Jiki babu ƙwari ta juya ta koma bedroom ɗin tana tunanin wane irin miji ta aura? Shin jiya da ya fita ya yi sallar magriba da isha'in ne ko kuwa haka ya gama bulayi ya dawo ya kwanta? In kuwa haka ne ai da sake ta yaya za take zaune da miji ba ya sallah ga baƙar ƙazanta.

Tun da ta yi sujada take addu'ar Allah ya kawo mata mafita a cikin lamarin tun da ta ga abu kamar wasa amma ƙaramar magana tana shirin zama babba.

Sai da ta gama karatu gari ya ɗan yi haske sannan ta kwanta. Bacci ya yi awon gaba da ita. Sai wajen ƙarfe tara ta tashi. Ta yi mamakin baccin da ta yi tana hamma ta sakko daga gadon amma tana zuwa falo ta ga Aminu kwance wannan karon ba bacci yake ba idanun sa biyu amma yana danna waya.

Ƙafarsa ta kalla ta ga babu alamar an saka ruwa alamar an yi sallah. Tsabar takaici bata masa magana ba ta koma ta shiga bayi ta yi brush ta wanke fuskar ta tana kallon brush ɗin Aminu har ya fara ƴar ƙura alamar ma ko ta kansa ba a bi.

Kicin ta shiga ta kwaɓa fulawa ta shiga soya musu waina. Sai da ta kammala ta tafasa ruwan shayi ta ɗakko ta taho. ta ajiye abin mamaki sai ta ji ƙaran zubar ruwa a bayi alamar ana wanka. Matsawa ta yi gaban bayin ta ƙara kunne ta ji da gaske wankan yake, hannu ta ɗaga sama tana yi wa Allah godiya, tana tunanin an samu sauyi tun da ga shi ana wanka don ta ji ƙaran dirza soso.

Falo ta dawo ta zauna tana jin daɗi a ranta tana fatan Allah sa maganganun da aka faɗa masa ne suka shige shi. Wayar sa da take kan kujera ce ta fara haske leƙawa ta yi sai kuwa ta ga kira ne yake shigowa da alama wayar a silent take shi ya sa ba a jin ƙaran.

"Ƴar aljanna" Sunan da ta gani yana yawo kenan a saman wayar, hannun ta har karkarwa yake tana mamakin a iya wannan ɗan lokacin da aka ɗauka da yin auren su wace ce wata ƴar aljanna wato saboda matsayin ta har an kira ta ƴar aljanna.

Kallon hanyar bedroom ɗin ta yi sannan ta kasa kunne tana jiyo ƙaran ruwan. Tana shirin ɗaukan wayar ta gudu kicin ta ci mutuncin ta a kan tana kiran mijin ta a cikin gida sai kawai kiran ya katse bata gama dawowa daga mamaki ba sai message ta ga ya shigo hannun ta har karkarwa yake ta buɗe.

"Ya ina kiranka ka ƙi ɗauka, kai da ka ce mini ƙarfe goma za ka zo yau ko wajen sana'a ba za ka je ba" Ganin wannan saƙon ya mugun ɗaga mata hankali tana cikin wanann yanayin ta ji ƙaran buɗe ƙofar bayi alamar ya fito daga banɗakin, message ɗin ta goge.

Da sauri ta tashi daga kujerar ta koma gaban kayan abincin da ta ajiye musu.

'Kenan wannan dalilin ne ya sa ya yi wanka wato wajen wata zai je?' Ta faÉ—a a zuciyarta.

Shi kuma dama kamar an ce masa ga abun da yake wakana a falon ya taho yana zuwa ya É—auki wayar ko kallon inda take bai yi ba da harara ta bi shi a ranta tana cewa

'Aikin banza bata san ƙazami bane kai da bata ɓatawa kanta lokaci ba' Ta ce a zuciyar ta. Jim kaɗan zuciyarta ta ce ta leƙe ɗakin ko dai chatting suke tana zuwa ta same shi yana sallah, wai sai lokacin wannan yake sallar asuba.

Falo ta dawo can sai ga shi ya fito sanye da wata shaddar sa da ta wanke masa ta goge, da a ce bata san inda zai je ba da ta ce ya birge ta, yau amma tuno da abin da Æ´ar aljanna ta ce sai ta ji tana jin haushinsa.

"Ina kwana "Ta gaishe shi ciki-ciki.

"Lafiya" Ya amsa a taƙaice.

Ganin ya nufi ƙofa da alamar fita zai yi ta buɗe baki ta ce

"Ya na ga ka kama hanyar fita ina jiranka mu karya?"

"Ki karya kawai ni na makara a wajen sana'a ta" Ya ce ba tare da ya kalle ta ba kafin ta ce wani abu har ya fita.

Tasowa ta yi ta biyo bayansa ta ce

"Wannan ne shirin zuwa wajen sana'a?"

"Kamar ya?" Ya furta yana haÉ—e rai.

"Na ga ai ka yi kwalliya kuma ba haka ka saba ba in za ka je wajen kasuwa ba ko dai wani waje za ka je da ban? Kai da ka ce wajen sana'a ba wajen saka kaya wankakke ba ne amma yau har gogagge ka sanya"

"Tuhuma ta kike yi ne? Ni da kayana sai ana tambayata don na saka ba ke kike damuna kullum a kan in ke saka kaya ba"

"Amma da nake cewa ka saka ai baka taɓa sakawa ba sai yau?"

"Haka na ga dama'" Ya ce yana juyawa ya bar ta tsaye da tuƙuƙin baƙin ciki.

ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE?

KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST?
Chapter 8 · 0% Book details