← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 44

Sashe 35

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya Aminu in É—akko maka shantos idan ka je gida ka fesa a kanka" Da sauri ya juya ta tahonda gudu ta saka sakata a É—akin, ya tsaya yana ta masifa yana cewa kar ta kuskura su haÉ—a hanya, ya rasa mai ya sa Fatima take masa haka ko do ta ga ita take binsa daga shi sai ita.

Kasuwa ya wuce.

Da yamma Umma ta shirya ta biya ta gidan ƙawarta suka wuce gidan Aminun. Sun shiga ɗakin Saddiqa inda ta gaishe su cikin mutunci, ta kawo musu ruwa mai sanyi sai dai waina ta yi kuma ta cinye babu hakan ya sa bata kawo musu abinci ba. Bayan sun gaisa Umma suka shiga tambayarta ba'asin abin da ya faru, kai Saddiqa ta sunkuyar tana jin wani ɗaci a zuciyarta ji take tamkar ta roƙi Umma cewa ta sanya Aminu ya sawwaqe mata, saboda ta lura Aminu ba mijin aure bane, indai za su cigaba da zama a haka tabbas za take cutuwa, duba da yadda yake ƙazamin nan, dama ita yanzu daɗin da take ji bai wuce cewa komawa ɗakin amaryarsa ba ƙaramin daɗi ta ji ba saboda haɗa makwanci da Aminu akwai damuwa.

Umma ce ta ce

"Saddiqa da amincewar ki Aminu ya ɗauki kwanaki ya ba Zulaiha? Bayan nata kwanakin bakwai sun ƙare matsayinta na amarya kuma budurwa" Shiru Saddiqa ta yi don ta tasa abin cewa saboda na farko dai kwanan nan umarni ne aka bata ba a shawarce ta ba, ta wani ɓangaren kuma za ta iya cewa taimakonta aka yj don ita da, da hali ma da ta ƙauracewa Aminu har abada!. To mai ma za ta ce? Mutumin da ya yi amarya ko ya haɗa su ya gabatar da ita a wajen amaryar ba matsayinta na uwar gidansa ba, sai a kicin ta ga amaryar, sannan ya yi watsi da duk wasu buƙatunta hatta abin cikinta ya nuna bai shirya haifarsa yanzu, to ita wace irin magana za ta yi a kan Aminu? Ta ce mai, ita yanzu kishin Aminun ma bata ji sai wanda ba a rasa ba ga matarsa marar kamun kai duba da yadda jiya ta zo ɗakinta ta yi wa Aminu ihun kwarto a cikin gidansa a ɗakinta, kawai saboda tana ganin satar kwana ya mata.

Ƙawar Umma ce ta kalle Saddiqa da tausayawa ta ce

"Saddiqa ana tambayarki amma kin kasa bada amsa?" Ta faÉ—a tana kallon yadda fuskar Saddiqar ta bayyana asirin zuciyarta, amma duk da haka sai suka tsaya sauraron jin ta bakinta, cikin muryarta mai sanyi cike da ladabi ta ce

"Umma da amincewa ta ya ƙara mata kwanan, shi ya sa jiyan ma na ce na ƙara musu sati biyu" Ta faɗa idanunta suna kawo ruwa amma ta danne bata basu damar zubowa ba, tana tuna irin so da ƙaunar da zuciyarta ta yi wa Aminu amma yanzu ya dishashe komai, da a ce bata zo gidansa ta samu halayen da bata yi zaton samunsa da su, da babu yadda za a yi ta bari a nisanta da shi, duk yadda za ta yi sai ta ƙwato mijinta amma ita yanzu neman kai ma take da shi, so take a barta ta ji da cikin jikinta da take ɗawainiya da shi.

Kallonta Umma ta yi ta ce

"Saddiqa kowa ya kalli fuskarki ya san ƙarya kike, a yadda hasashena ya nuna Aminu ya ba amaryar kwanakin naki ne ba da amincewarki ba kuma wannan tozarci ne a ce namiji ya karɓi kwananaka ya ba kishiyarka" Ƙawar Ummar ce ta ce

"Alamomi masu yawa sun yi nuni da hakan, amma Aminu bai kyauta ba" Umma ta ce

"Zai zo ya same ni sai an rama miki kwanakin ki da aka ƙwace, ma'ana idan kika karɓi girki gobe sai kin yi kwanakin da ta yi a cikin naki sannan miji zai koma bakinta" Da sauri Saddiqa ta ɗago kai tana kallon Umma ta ce

"Umma wallahi na bar mata ba sai na rama ba, idan suka yi wata gudan sai mu fara rabon kwan... Umma ce ta y saurin katse ta da cewa

"Saddiqa me kike ƙoƙarin yi ne? Mijinki kamar kina neman kai da shi? Ya za a yi mace ta barwa kishiyarta har sati uku kamar wani shirin wasan kwaikwayo ko littafin hausa? Hakan fa tozarci ne da jan raini a wajen kishiya, za ta ga baki isa a gidan mijinki ba" Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata ba tare da ya shirya zubowarsu ba ta ce

"Umma ni alfarmar da nake nema a wajenki, don Allah Umma ki faɗawa Aminu yake yin tsafta" Ta faɗa tana mai jin nauyin furucin sai dai babu yadda za ta yi hakan ya zama dole ne domin yanzu mafita take nema a kan ƙazantar Aminu, ta tsani warin jikinsa ta duniya tana baƙin cikin shaƙar warin bakinsa, mai za a yi da ƘAZAMIN MIJI babu wanda zai gane halin da take ciki sai matar da ita ma mijinta ya kasance ƘAZAMIN MIJI.

Shiru Umma ta yi don ta rasa bakin magana, sai ta ji tana jin nauyin Saddiqa, tana tuno yadda ta ga kwarkwata a cikin kansa da yadda jikinsa yake tashin wari, ita ce mahaifiyar Aminu ita ce za ta bayar da shaidar cewa Aminu ƘAZAMI ne na ajin ƙarshe. Cikin lallashi ta kalli Saddiqa ta ce

"Saddiqa na san kina haƙuri sai dai in ce ki ƙara haƙuri a kan haƙuri, sannan ko yau da Aminu ya je na kwashe tsowon lokaci ina masa faɗa da nasiha a kan ya gyara halayensa, amma yanzu ma zan ƙara nannaga masa, na san akwai damuwa amma ki yi haƙuri watarana sai labari, amma ina roƙon ki arziƙi ki yi haƙuri mijinki ya dawo ɗakin ki yau" Ba za ta iya cewa Umma a'a hakan ya sa ta ce

"To Umma babu komai na amince" Ta faɗa tana sadda kai. Ƙawar Umma ta ce

"Allah miki albarka, ya sa hanyar shigarki aljanna ne auran, Allah ƙara miki haƙuri, domin haƙuri shi ne matakin cimma nasara a rayuwa" Da amin Umma da Saddiqa suka amsa kafin suka mata sallama suka fita, ɓangaren Sumayya suka shiga, tana zaune da ɗaurin ƙirji tana shan take, Ruma ma tana shan raken ruwan raken duk sai zuba yake ya gama ɓata mata gaban rigar, duk ta ɓata ɗakin dama daga gani babu shara ga kayayyaki nan zube a ƙasa da kan kujera.

Shigowar su Umma ne ta É—akko hijabi a kan kujerar wani da ya gama shan uban datti, kana iya ganin datti a fuskar hijabin. Zaunawa ta yi ta shiga gaishe da su, É—akin sai tashin warin jikin Sumayyar yake.

Bayan sun ɗan taɓa hira, Umma ta ba Ruma biskit da alewar da ta kawo mata, haka suka wuce ɓangaren Amina ma suka gaisa suka ba su Albani nasu biskit da alewar, suna fitowa suka nufi ɗakin Zulaiha.

Zaune take a tsakiyar É—aki, jikinta da rigar buba ta yadi kanta babu É—ankwaki, duk ta cukurkuÉ—a shi duk ya tashi tsaye da alama ma susa take yi. Bayan sun zauna ta gaishe da su, Umma tana lura da ita yadda bayan ta saka hule a kan mata amma ta cigaba da susa, sai sosawa take a kai- a kai, Umma kallon tsaf ta mata a zuciyarta ta ce

'Tsakanin ke da Aminun a samu wanda ya kwasawa wani kwarkwatar don ita ma alamomi sun nuna hakan. Umma ce ta yi gyara murya ta ce

"Zulaiha Aminu ya faɗa minj saɓanin da aka samu a gidan nan, shi ne na ce bari in zo in bincika in ji" Tun kafin Umma ta rufe bakinta Zulaiha ta ce

"Umma shi ne bashi da gaskiya, bayan ya bani sati biyu amma na kama shi yau ya munafurce mi Umma turmi da taɓarya na tarar da shi da matarsa" Ta faɗa babu jin nauyin Umma ko wani ladabi

Umma ta ce

"Amma ai kwanan Saddiqa ne, ita mun je min mata magana kuma komai ya wuce, don haka yanzu ki bari yau Aminu ya koma can idan ta yi kwana biyu sai ya dawo bakin ki" Kallonsu take tarrr da wankakkun idanunta ta ce

"Haba dai Umma abin har da zaɓunta, ai maganar fari ita sarki yake karɓa, kuma ko jiya ita matar tasa da bakinta ta ce ta ƙara masa sati biyu, don haka yanzu kuwa sai na yi ƙarasa kwana ukun sannan na ƙarasa sati biyun, ai baki shi yake yanka wuya" Baki sakkak suke kallonta saj da ƙawar Umma ta ce

"Haba ke kuwa ana yin sulhu kuma kya ke wannan maganar, ko ba komai wannan ai surukarki ce" Shiru ta yi tana haÉ—e gira alamar maganar bata shige ta ba, tashi ta yi ta je kicin ta É—akko jallof É—in wake da shinkafa a plate ta rufe da wani plate É—in sai cokula biyu da pure watar biyu, ta kawo.

Bayaj fitar ta sun jinjina rashin ta ido irin na Zulaiha, don kar ta zargi wani abu suka buɗe abincin, tana gefe tana danna waya, su duka suka yi cokali ɗaya, guntse da abincin suke a bakinsu, don waken bai dahu ba, ita ma shinkafar kamar ta jiƙu ga wani gashiri, kallon juna suka yi dakyar suka haɗiye, Umma tana ƙara ɗakko cokali na biyu sai ga gashi dogo a ciki.

Da sauri Umma ta ajiye tana ɗaukan plate ɗin ta rufe tare da ɗaukan pure water ta shiga sha, ita ma ƙawar Ummar ruwan ta sha, Zulaiha ta ɗago tana kallon plate ɗin da suka rufe ta ce

"A ƙaro muku ne Umma?" Da sauri ƙawar Umma ta ce

"Ah Alhamdulillahi, ai da yake kafin mu fito mun ci abinci" Ba ta taɓe a ɓoye ta tashi ta kinkimi plate ɗin ta ajiye a kicin sai gata ta dawo, daidai nan Aminu ya shigo da sallama. Jir da warin gumi ga jikin nan butu-butu da fulawa. Gaishe da su Umma ya yi, nan Umma suka ƙara musu nasiha da kuma tabbatar da cewa Saddiqa ce za ta karɓi girki, Aminu sai washe baki yake yana tuno yau zai yi kwanan wuri mai tsafta ga kuma tsaftatacciya Saddiqa a gefe, tabbas ya yi kewar ɗumin jikinta da fatarta mai laushi da santsi tamkat kifi tarwaɗa.
Chapter 35 · 0% Book details