Sashe 13
Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Haba ƴar aljannata wa ya ce miki haka, wallahi Saddiqa ce ta yi wa kicin ɗin dirar mikiya kawai sai ganinta na yi kamar an jefo ta" Ya faɗa murya ƙasa-ƙasa don ya ƙosa su yi sallama kar Saddiqar ta sake dawowa, saboda tun yadda ta sauya ɗazu da ya kusa kai hannunsa jikinta sai yake ɗan shayinta.
Sai ji ya yi ta ce"Ikon Allah na kwance ya faÉ—i, yanzu kai kuma mijin ta ce za ka zama ko mene ne wannan É—in, kai da kake da tsarin mace biyu amma kake tsoro to wallahi tun wuri ma in bacci kake ka falka amma tabbas akwai aiki ja a gabanka"
Cikin ƙarfin hali ya ce
"Ba fa tsoronta nake yi ba ai ni daga ganina kin san cikakken namiji ne mai kwarjini da haiba, na fi ƙarfin mace ta juya ni"
Ƙwafa ta yi sannan ta ce
"To a dai juri zuwa rafi don watarana tulu zai fashe" Bai biya ta ba don burinsa yanzu su yi sallama saboda ya koma É—akin, kar Saddiqa ta yi tunanin wani abu da ban saboda sai da ya ji dama fita waje ya yi idan ya gama wayar ya dawo.
Wani ƙaramin ƙyalle da ya gani ya ɗauka tare da wata ƙaramar roba, fitowa ya yi ya dawo falon, zaune ya same ta tana kurɓar shayin da take jin tamkar maɗaci ne take sha, gabaɗaya ranta a cunkushe yake ta kasa gane wane irin zaman aure take yi lallai ta yarda maza su ba ƙwarya ba ne bare a ƙwanƙwasa a ji. A yadda take kallon Aminunta bata ɗauka za ta samu wata kasawa ko gazawa daga gare shi ba, amma sai ga shi hakan ta faru a kwana kusa.
Ji ta yi ya ce
"Bari na tsiyayi ruwan nan" Ya faÉ—a yana É—aukan flacks É—in, a gefe É—aya yana satar kallonta ta wutsiyar ido amma sai ya ga kamar dai bata ki mai yake faÉ—a ba, duk da dai yanayinta bai nuna masa ta nuna wata alama da za ta alamta masa ta ji wayar da yake yi ba, amma dai ya fi zargin abin da ya faru tsakaminsu É—azu ne yake kai kawo a birnin zuciyarta.
Ɗan gefe ya matsa ya zauna ya shiga tsoma ƙyallan nan yana matsewa sai ya ɗora a hannunsa, kallon gefen ido ta masa tare da taɓe baki don ta fahimci babu wani ciwo a tare da shi. Tana gama shanye shayin ta ɗauki kofin da flacka ɗin ta mayar kicin. Ɗaki ta koma ta cire kayan jikinta ta ɗaura towel ta shiga bayi ta yi brush tare da yin wanka, fitowa ta yi ta ɗauki wata rigar bacci iya gwiwa ta sanya.
Jikinta ta feshi da turare ta ɗauki wayarta da take kan madubi, har za ta hau gadon kawai sai ta ga duk dattin ƙafar Aminu da kuma farin fulawa ya ɓata zanin gadon ƙyanƙyami irin nata sai ta ji ba za ta iya kwantawa ba, cirewa ta yi ta ɗakko wani ta shimfiɗa ta ɗauki freshner ɗinta da ta ji ta kusa ƙarewa ta fesa ta hau ka ta kwanta.
Wayar ta cigaba da dannawa ta hau whatsapp, gani saƙon ƙawarta Khady ta buɗe ta fara karantawa kamar haka.
"Gobe zan dawo" Tana daga kwancen sai da ta tashi zaune, sosai ta ji daɗin maganar dawowae ƙawar tata wacce bata gari aka yi bikinta ma tana can Niger dangin Babanta.
Amsa ta bata da cewa
"Da gaske kike ko wasa?"
Ita ma amsar ta maido mata don lokacin tana online.
"Wallahi da gaske"
Cike da zumuÉ—i ta ce
"Allah kawo ki lafiya" Sallama suka yi ta ajiye wayar ta ja bargo ta yi addu'a ta shafa bacci ya yi awon gaba da ita, don bata san shi Aminun yau ma ko kwanan falon zai yi ba, in ma a ina zai kwana shi ya sani saboda yanzu ta daina saka damuwarsa a ranta kar ta je ta cutu a banza tun da shi ba ta ita yake yi ba, wata ce a gabansa ba ta tata yake yi ba.
A ɓangaren Aminu kuwa tana shigewa ɗaki ya sauke wata ajiyar zuciya, bai san mai ya sa ba tun da ya yi yunƙurin marinta ya ga ɓacin rai ɓaro-ɓaro a fuskarta sai ya ji yana shayinta kaɗan.
A zuciyarsa ya ce
'Oh duniya mai juyi-juyi kwaɗo ya faɗa ruwan zafi yau ni Aminu ne nake jin fargaba a kan mace, sai ka ce wanda bakin uwa ya kama' Hannu ya sa ya ture robar da ya zuba ruwan zafin ya ajiye ƙyallan ya koma ya jingina da kujera, wayarsa ya fiddo ya yi shige-shige ya gama ya mayar da roba da ƙyallan.
Sai da ya mayar da wayar silent sannan ya je ya buɗe drower ɗinsa ya saka wayar saboda tsaro ba don tsoro ba, ya san ƴar aljannarsa za ta iya ƙara kiransa, duk da yana jin saukar numfashin Saddiqa alamar bacci ya yi awon gaba da ita.
Bayi ya shiga ya hau toilet ya rage nauyin cikinsa, bayan ya yi tsarki ya tashi ya mayar da murfin ya rufe ba tare da ya yi floshing ba. Tunowa da ya yi da abin da Saddiqa ta ce a kan bar mata kashi bai kora ba, sai ya yi floshin ɗin don yau so yake ya lallaɓa ya sauke buƙatarsa a kanta tun da dai jiya ma a falo a kujera ya kwana kamar wani gauro.
Yana fitowa ya haura gadon yanayin ƙamshin turaren da Saddiqa ta shafa da na freshner ya haɗe kan gadon, hanci ya ƙara buɗewa yana shaƙa, sai da ya kwanta ma ya ji ƙamshin duk ashe a jikin zanin gadon ma. Bargon ya ja ya shige ya rarumo Saddiqa da take cikin tsafta tana bacci cikin kwanciyae hankali. Cikin baccin ta tsinkayi muryarsa yana cewa
"Saddiqa ba dai har kin yi nisan zango ba" Wani irin hamami da ya ziyarci hancin ta daga warin bakinsa dai da kanta ya sara, a take zuciyarta ta tashi ta ji wani amai ya tasho mata, janye jikinta ta shiga yi shi kuma sai ƙara maƙalƙaleta yake kamar ƙadangare ya samu bango.
Fisge -fisge ta shiga yi don babu abin da ta fi buƙata yanzu sama da ta ganta a bayi, kokawa ce ta kaure a tsakanin ma'auratan biyu ita tana son ta je ta amayar da abin da ya taho mata, shi kuma duk tunaninsa gudunsa za ta yi saboda abin da ya faru tsakanin su, tana cikin kiciniyar ƙwatar kanta sai ya sake buɗe bakinsa ya ce
"Haba Saddiqa, ke yanzu saboda saɓani ya gifta tsakanimu sai ki hanani haƙƙina? Ko so kike mala'iku su tsine miki?" Kai kawai take jijjigawa alamar a'a don bata son ta buɗe bakinta amai ya zubo saboda maganar da yake ƙara hautsina cikinta warin bakin nasa yake, bata san adadin kwanakin da ya yi bai wanke bakin ba ga warin hammatar gumin jikinsa kaɗai ma ta sai tabbas ƘAZAMIN MIJI take aure.
Tana ta ture shi ta samu ta kuɓuta sau ya ce
"Na ga dai ban yi marin ba, kuma kowa yana kuskure ki tausaya mini a buƙace nake wallahi" Ya faɗa yana rungume ta. Ganin shi bai fahimci komai ba ta dage ƙarfinta ta tura shi baya, da sauri ta tashi tsaye a kan gadon tana shirin ta dira, sai ji ta yi ya saka hannu ya riƙo ƙasan rigar baccin nata. Hannu ɗaya ta saka ta toshe bakinta gudun kar aman ya zubo, ɗaya hannun kuma ta yi amfani da shi wajen yi masa zancen kurame alamar tana zuwa, sai sannan ya gane banɗaki take son shiga don ya ga tana masa nuni da jikinta hakan ya sa ya washe rinannun haƙoransa.
Har neman tuntuɓe take wajen yin gudu, takalmin ma a juye ta saka tana sauri tana shiga bayin ta shiga kelaya amai tamkar ƴaƴan hanjinta za su fito. Sai da ta gama ta wanke fuskarta tana cikin yin brush sai ganin mutum ta yi tsaye a bakin ƙofa yana kallonta kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai, bata ankara ba sai ji ta yi ya ce
"Haba Saddiqa wai ke kama sau nawa kike wanke baki a rana ne, a ce mutum ko fashin wanke baki ba ya yi kullum sai ya wanke, wankewar ma ba sau ɗaya ba sau biyu ba?" Ya faɗa yana riƙe da ƙugu.
Bata ce komai ba sai da ta gama brush ɗin don so take ta daina jin abin ƙarnin aman a bakinta, tana shirin ajiye brush ɗin ta ji ya ce
"Ina miki magana kin watsa yina Saddiqa, mace dai an santa da tattali da cancana abu amma ke baki iya komai ba sai almubazzaranci, ni bakin nan sai in kwana uku huɗu ban wanke ba, kuma ko da na tashi tatsar makilin ɗin ɗan kaɗan nake matsa, amma ke sai kin cika kan brush ɗinki da makilin gaskiya ya kamata ki iya tattali saboda rayuwa" Ajiyar zuciya ta sauke ta taho ta raɓa shi ta wuce ya biyo bayanta, tana zuwa ta zauna a bakin gado, zuwa ya yi ya tsaya a kanta yana hucin jin haushin ƙyaleshi ɗin da ta yi yana bambami, ita warin da take shaƙa daga jikinsa kaɗai aka barta da shi ba ƙaramin cutuwa take yi ba ta rasa sai yaushe zai fahimci cewa ƘAZANTA ba ƙaramin cutar da abokin tarayya take yi ba, amma haka ta danne zuciyarta ta ce
"Yanzu shi wankin bakin ma sai an tuhumi mutum? Kai yanzu tsakani da Allah daÉ—i ta maka kake ikirarin kwana huÉ—u biyar baka wanke baki ba? Har kake cewa wai tattali ne hakan?"
Hannunsa ya mayar baya jin tamkar ya kwaÉ—e ta sannan ya ce
"Yanzu daga magana sai cibi ya zama ƙari Saddiqa kike neman faɗa mini baƙar magana, su baki dai mene ne don ka yi fashin wankewa?" Tsabar takaici sai da ta kai zuciyarta nesa ta bashi amsa da faɗin
"Babu komai" Ganin kamar dai ranta a ɓace kuma ya lura kamar ma tana ɗan kauda kai sai ya sassauta murya ya ce