Sashe 32
Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakan ya sa bata hana shi ba, kuma bata nuna damuwar kwalliyar da ya ci ba, har da ɗakko wani turare da ta saya mai bala'in ƙamshi ta fesa masa sosai, wai bata son ya je wajen abokai a raina shi.
Yana fita ya dokawa Salaha waya ya ce yana hanya. Suna cikin hira da Salaha tana ta yaba ƙamshin turaren, zuwa can sai ta ce ya ara mata wayarsa za ta tura wata waƙa da ta ji ranar nan ana kiransa da ita, hankali kwance ya miƙa mata, tana cikin danne -danne sai wayar ta ɗauki ƙar gani ya yi Salaha ta zaro idanu sai ta ce
"Me zan gani wane suna ne wannan?" Ta tambaya tana tashi tsaye, gabansa ne ya buga da ƙarfi yana jin wani tashin hankali don ya san ba zai rasa nasa ba da kiran Amina ba ne ya shigo wanda ya yj saved na sunan da MY WIFE, cikin karkarwa hannu ya miƙa hannun yana cewa
"Wane suna kuma? Bani in gani, tana aika masa wani kallon tuhuma ta miƙa masa wayar, sunan da ya gani ne ya sa hankalinsa tashi, ya fara tunanin amsar da zai bata...
*ZULAIHA*
Ɗakin ta koma ta ɗauko fitila, ko tsoro bata ji ta fito daga ɗakin ta shiga baza idanu amma babu kowa, ƙwafa ta yi ta kama hanyar ɗakin Saddiqa duk da bata taɓa shiga ɗakin ba wannan ne karon farko amma yau ya zame mata dole ta je tun da a nata ganin ai neman kadararta za ta je, wato mijinta.
Tana zuwa ƙofar ɗakin ta ganta a rufe, amma tun daga hanyar take duba sawun Aminu, ko takalmi babu, kuma ta ga sawun nasa ya yanke ne daga lokacin da ta zo ƙofar ɗakin Saddiqa sai ta nemi sawun ta rasa.
A can cikin ɗakin kuwa Saddiqa, jin Aminu ya rungume ta, ta shiga kiciniyar ƙwace kanta daga gare shi, saboda yadda warin jikinsa ya gama cika mata hanci ba abin da ta fi buƙata illa ya sake ta, ko ta shaƙi wata iskar mai daɗi wacce ba gurɓatacciya ba irin ta jikinsa. Shi kuma jin tana son raba jikinta da nasa, sai ya bada ƙaimi wajen yi mata wani irin riƙo, cikin murya raɗa-raɗa ya buɗe bakinsa mai warin da ya sa ta fara jin kanta ya fara juyawa ya ce
"Saddiqa ni ne Aminunki fa, ki saki jikinki yau na zo na share miki hawayenki na kewata, na san tabbas! Kin yi kewar mijinki da É—umin jikinsa" Yana faÉ—ar hakan ta ji amai ya taho mata jin aman yana barazanar zubowa sai ta shiga girgiza masa kai.
Bai damu da yanayin da take nunawa ba, shi dai buƙatar maje hajji sallah wato ya samu biyan buƙatarsa. Rigar baccin jikinta ya shiga ƙoƙarin raba ta da ita. A daidai wannan lokacin ne a halin da suke ciki, suka ji an banko ƙofar ɗakin ba Saddiqa ba hatta Aminu dai da ya razana da bugo ƙofar, kafin su yi wani yunƙuri an dalle su da wata fitila mai haske.
Zulaiha kuwa ganinsu a manne da juna ya mugun ɗaga mata hankali, ga wani tuƙuƙin baƙin cikin da ya tokare mata maƙoshi a take ta fara jin wani jiri yana juyata, da sauri ta juya ta je kicin a guje ta ɗakko taɓarya dawowa ta yi ta shiga cewa
"Ihu mutanen gida, kwarto, kwarto a kawo É—auki ihu kwarto" Aminu duk tunaninsa bayan fitowarsa ne kwarto ya kaiwa Zulaiha farmaki, ashe bai san iya shege ne ba da shi take.
A ɓangaren Sule jin ihun kwarto sai ya fito daga ɓangarensa ɗauke da wata ƙatuwar sanda, haka Yaya Shafi'u ma ya fito ɗauke da wata zarɓeɓiyar wuƙw da take cikin gidanta. A gigice suka iso wajenta, don sun gane amaryar gidan ce amma ganinta a ƙofar ɗakin Saddiqa sai suka fara tunanin ko ɗakin Saddiqa kwarton ya shiga, shi ya sa ta tsaya a wajen, suna zuwa a kusan tare suka ce
"Yana ina ko ya fice" Cikin muyarta wacce tamkar kuka zai fito ta ce
"Yana ɗakin wannan" Ta faɗa tana musu nuni da ɗakin Saddiqa, su kuma sai suka jinjina mata, ganinta ɗauke da taɓarya sannan kuma tana gadin ɗakin da kwaton yake.
Aminu kuwa jin muryoyin Yayunsa bai sanya ya yi girgizu ba, Saddiqa ce ma jin ya sakar mata jiki sai ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon. Tana sakkowa su duka ukun suka kawowa ɗakin farmaki, Yaya Sule, Yaya Shafi'u da kuma Zulaiha kowanne ɗauke da makami.
Yaya Shafi'u ganin Saddiqa cikin kayan bacci, da yake suna shigowa Yaya Sule ya kunna fitilar ɗakin, ga kuma hasken fitilar hannun Zulaiha. Jikinta kawai Shafi'u yake bi da kallo don ba ƙaramib kyau ta masa ba cikin rigar baccin, duk da doguwa ce amma dai ta bayyana asalin suffarta.
Zulaiha kuwa ta shagaltu da kallon ɗakin ne, tana wani taɓe baki jin yadda ƙamshi ya zauna a ɗakin tamkar yanzu aka saka turaren wuta.
Yaya Sule kuma ganin Aminu zaune dirshan a kan gado yana sanye da gajeran wandonsa, sai abin ya É—aure masa kai, shi ma Yaya Shafi'u da ya mayar da ganinsa wajen mamakin ne ya dirar masa. Cikin Kakkausar murya Yaya Sule ya katse Zulaiha da faÉ—in
"Ke Zulaiha mene ne wannan É—in, Aminun ne kwarto, haka kawai muna bacci kin zo kin É—agawa mutane hankali" Yana kaiwa aya Yaya Shafi'u ya É—ora da faÉ—in
"To wai mai hakan yake nufi?" Jin kalamansu cikin tsiwa ta ce
"To amma haka za ku ce ko tambayata za ku yi dalilina na yin hakan?" Da hanzari Yaya Sule da ya fi jin zafin É—aga musu hankalin da ta yi ya ce
"Mai za a tambaye ki a nan to, bamu ga kowa ba sai Aminu kuma kin ce kwarto yana É—akin" Ita ma cikin fitsara da rashin girmama na gaba ta ce
"Ai ba kowa bane ƙasurgumin kwarton illa Aminu" Su duka da kallo suka bita ganin ko a jikinta. Yaya Sule a zuciyarsa ya ce
'Taɓ lallai Aminu ya auro mace daidai shi' A fili kuma ya ce
"A ina ya yi kwartancin" Shi kuma Aminu ya rasa ma bakin magana, ba komai ne ya bashi haushi ba illa yadda aka katse masa wani yanayi mai ban al'ajabi wanda ya san a wajen kaÉ—ai ne yake samun wannan yanayin, bai tantance haka ba sai da ya auri Zulaiha ya gane Saddiqa ta keta Zulaiha da tazara mai nisan gaske.
Yaya Shafi'u ne ya ce
"Kin san me kike faÉ—a?"
Cikin harzuƙa ta ce wai ku haka ake alƙalanci, ba za ku tambaye ni dalili ba sai kawai kuke yanke hukunci, to bari ku ji abin da baku sani ba, Aminu tun kafin in tare a gidan nan ya mini alƙawarin sati biyu zan yi ina amarci, amma yau saura kwana huɗu shi ne zai yi satar hanya ya mini satar kwana" Ta faɗa tana aikawa Aminu harara. Su duka mamaki suke inda Saddiqa ta sunkuyar da kai.
Yaya Sule ne ya ce
"Wai haka ne Aminu?" Aminu yana jin kamar su duka ya rufe su da duka, ganin sun hana shi rawar gaban hantsi ya ce
"Haka ne" Kai Zulaiha ta kaɗa irin ai kun ji da kunnenku. Yaya Sule cikin ɓacin rai ya fara magana
"Kai yanzu Aminu ka kyauta kenan, ka yi wa Saddiqa adalci a ce ka É—auki kwananta ka haÉ—awa amaryarka, muna gidan nan amma bamu san wannan cakwakiyar da ka haÉ—a ba" Aminu ya buÉ—e baki zai yi magama Saddiqa ta yi saurin faÉ—in
"Yaya da sanina kuma da yardata aka yi hakan, yanzu ma na ƙara masa sati biyu ka ga wata ɗaya kenan" Ta faɗa don ita zuwansa yau da ta ji warin da ta shaƙa sai ta ji ta ƙara son nesanta kanta da shi.
Da sauri Aminu ya diro daga gadon cikin É—aga murya ya ce
"Wallahi baki isa ba, daga kwana goman nan dole ki karɓi girki"
Zulaiha jin haka ta sakin taɓaryar hannunta ta ce
"Idan akwai shegen da ya isa ya yanke wannan hukunci shegiya nake" Yaya Sule kai ya sunkuyar yana danne dariyarsa ganin ƙanin nasa ya samu daidai da shi in ba don sakayya da Allah ya yi wa Saddiqa ba, ya za a yi a ce amaryar kwana goma tana wannan masifa.
Sosai hargitsi ya kaure na faÉ—i in faÉ—a, tsakanin Aminu da Zulaiha, dakyar Yaya Sule ya sasanta amma abin ya ci tura!.
A ƙarshe dai Aminu ya yi wa su Yaya Sule rashin kunya saboda suna masa faɗan rashin kyautawar da ya yi wa Saddiqa, hakan ya sa kowa ya kama gabanshi suka bar Zulaiha da su Aminun a ɗakin Saddiqa.
Zulaiha ta ce
"Wallahi ina ɗakin nan babu inda zan je" Ta faɗa tana samun kan kujera ta zauna tana riƙe da taɓarya, ta ce Aminu idan ya yi gigin taɓa ta kai za ta ɓare masa, don sosai kishi yake nuƙurƙusarta musamman da ta ga Saddiqa rigar jikinta ta mata kyau, sannan har lokacin bata daina hango hotonsu a idanun zuciyarta ba, yadda ta same shi rungume da Saddiqar hakan ya sa take jin tamkar ta same su da taɓaryar ta yi ta duka ko ta samu rangwamen abin da take ji.
Aminu yana tsakiyar gado a zaune, ya kifa tagumi don yau ya ga abin da ya turewa buzu naÉ—i, Saddiqa kuwa wuri ta samu ta zauna tana kallon ikon Allah, amma yadda amarya da ango suka É—umama É—akin da warin dauÉ—a kaÉ—ai ya isheta.
Zulaiha har aka kira assalatu tana zaune a wajen, ita kuwa Saddiqa ta fito ta barsu a É—akin, bayinta ta buÉ—e da yake kullewa take da mukulli ta je ta É—auro alwala ta dawo É—akin ta É—auki sallaya da hijabi ta fita waje ta kabbara sallah. Shi kuwa Aminu lokacin har ya fara gyangyaÉ—i jin sanyin asuba yana ratsa shi, hakan ya sa sai yana cikin gyangyaÉ—in Zulaiha ta ce