← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 44

Sashe 4

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabaɗaya shi dai ya yi da na sanin auren Sumayya saboda muguwar ƙazantar ta, ya rasa dalilin da ya sa bai fahimci hakan ba lokacin da yana neman auren ta ko don tana kwalliya tsaf-tsaf idan zai je zance, sai da suka yi aure abu da kaɗan-kaɗan yake bayyana har ta kai tun tana ɗan ɓoyewa yanzu abubuwa sun kai har bata ma jin kunyar ƙazanta.

Da dare tana zaune babu É—anwakwali shi ma yana zaune yana danna waya lokaci zuwa lokaci yana É—an satar kallon ta ganin yadda kitson kanta ya yi tsofa sosai har ba a ganin tsagar ko kaÉ—an duk ya cushe sai wani susa take.

"Sumayya" Ya kira ta da murya mai kamar lallashi, amsa masa ta yi ba tare da ta kalle shi ba.

"Yanzu Sumayya rayuwa ta yiwu a hakan anya? A ce wanke-wanke sai kwanuka su ƙare a kwando kin gwammace in xa ki yi amfani da kwano ki ɗauka ki wanke, haka tukunya ma? Wankin kayan ki da na Ruma har sai kun rasa na sakawa za ki tsakura ki wanke, yarinyar nan bata samun kulawa ta tsafta kullum ka ganta da ƙazanta don Allah ki gyara tun da dai dai gwargwado ina kawo komai kuma duk abin da kike buƙata ina miki" Ya ce cikin rausayar da kai amma ko arziƙin kallo bai samu ba.

"Magana fa nake miki ko?"

"Wai don Allah Shafi'u mene ne matsalar ka da ni ne da za kake takurawa rayuwata? Ni fa babu dalilin da zai saka kullum in ke wahalar da kaina, in ke wanki bai taru ba ko wanke-wanke ko in ƙare bauta a kan ƴa ɗaya ƙwallin ƙwal, haba ita mace bata da lokacin hutu sai na bauta a gidan miji idan abin da nake bai gamshe ka ba za ka iya ɗauko mai aiki take maka duk abubuwan da ba na yi"

"Haka mw za ki ce mai ya sa ke har kullum in dai hanya ta masalaha ce aka ce za a bi amma ke bakya yarda da ita? Ke ko kaÉ—an bakya son a miki gyara? Yanzu daga ni sai ke sai Ruma har sai na zauna É—aukan mai aiki"

"To tun da har ba za ka ɗauki mai aikin ba, sai ka ɗauki na annabawa don ni ba zan ƙare a wahala ba wallahi" Tana gama faɗar hakan ta tashi fuuuu ta shige ɗaki, wani gumus ya shai warin kayan jikin ta da suke warin dauɗa da kuma warin gumi don ya san wannan maimaicin bai san na nawa ba ne, haka take ta maimaita kaya.

Sai da ya kammala da abin da yake a wayar ya tashi zuciyar sa duk a cunkushe, don dama ba komai yake gani a wayar ba illa hotunan ƴan mata yana ganin haɗaɗɗun mata da suka yi kwalliya hakan yake sawa yana jin shauƙi yana ji dama a ce Sumayyar sa ce take haka da babu ruwan sa fa kalle-kalle ya shiga ɗakin kayan jikin sa ya ɗan rage ya shiga ya yi wanka ya fito ya shafa turare, yana hawa gadon ya shaƙi warin jikin ta ga bakin nan da ta hangame tana bacci sai wari yake fitowa daga bakin, warin rashin wankin bakin don ita Sumayya abin ya mata yawa wai shege da hauka. A haka ya yi ta maza ya matsa kusa da ita don a buƙace yake sosai sai sai abin da yake shaƙa daga jikin ta ya sa ya ji tamkar ya toshe hancin ya biya buƙatar a haka don ya san ko mai za a yi ba za ta yarda ta watsa ruwa a jikin ta ba bare ɗan warin gumin da take yi ya kau.

Hannu ya kai ya ɗan taɓa ta, da yake ita Ruma shimfiɗar ta da ban, cikin bacci ta sanya hannu ta buge hannun, ɗan matsawa ya yi kusa da ita duk da yana jin hamamin yana damunsa ya kai bakin sa kusa da kunnen ta ya ce

"Sumy baby" Kiran da ya mata ya sa ta ɗan buɗe idanu tare da ƙanƙance su ta sauke a kan sa ta sauran hasken farin watan da ya haske ɗakin.

Wartsakewa ta yi tare da tashi zaune ta zauna daram, ta haɗe girar sama da ƙasa ta ce

"Haba don Allah wannan ai ɗaukan alhaki ne ya ina baccina mai daɗi za ka zo ka tashe ni kana mini wata raɗa a kunne" Ta faɗa tana haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba. Shafi'u ji ya yi kamar ya yi amai da ya shaƙi iskar da ta fito daga bakin ta wani irin wari, amma da yake a buƙace yake sai ya ji zai jure ko da kuwa yana kawar da kai ne ya samu ya kauda buƙatar sa. Sai dai inda gizo yake saƙar bai san ma ko za ta amince ba.

"Ki É—an saki fuskar mana kin ji baby nah...

"Eh mana dama yanzu za ka kalailame ni da zaƙin baki, saboda kana buƙatata ai ɗazu ka rufe ido ka faɗa mini baƙar magana ka ga ai baka zo wajen ƙazama ba" Ta ce cikin hargowa. Ɗan marairaice fuska ya yi ya ce

"Ki yi haƙuri kin ji Sumy na daina"

"Wallahi yanzu bacci zan yi babu abin da zai sa na ɓata lokaci na ban yi bacci ba kaina yake ciwo, kai da in ka fara abu baka san ka tsagaita ba" Ta ce tana juya baya ta kwanta.

"Don Allah ki taimaka yau kwana nawa ina fama da ke ko so kike in faÉ—a halaka haba ke kuwa"

"Ka daÉ—e baka faÉ—a halaka ba, kuma babu wata halaka sai dai ka ce son zuciya in ba son zuciya ba mene ne kuma ko ma dai mene ne kabarin ka da ban nawa da ban" Ta ce tana jan abun rufa ta rufa ta bar shi, da ya kama bargon ma zai shiga ta daddanne ta hana shi ya shiga.

Jikin allon gadon ya koma ya jingina, ransa yana ƙuna ya gaji da abin da Sumayya take masa ban da ƙazantar ta har da hana shi haƙƙin sa. Bai yi fushi ba ya ƙara kai mata raruma ta kuwa balbale shi da masifa tana mai tashi fuuu ta suri bargon ta koma falo ta kwanta a doguwar kujera. Iska ya furzar daga bakin sa yana jin yadda buƙata take bijiro masa.

Filo ya ja ya runguma yana jin tamkar ya saki kukan takaici da haka bacci ya yi awon gaba da shi.

*SULE*

Zaune yake a falo yana sha tea yana duba news Amina tana daga gefe tama danna wayar ta, É—ago kai ya yi kalle ta cike da kulawa da nuna soyayya ya ce

"Annurin zuciyata, son ki ya daɗe da yon nutso a birnin zuciyata duk ranar da aka ce babu ke a wannan duniyar to ba na jin zan iya ƙara wasu kwanaki ina cikin hayyacina in ma dai ba mu yi mutuwar kasko ba" Kallon sa ta yi sheƙeƙe tana jinjinawa rainin wayo da ƙaryar tashi ta ce

"Abban Yusuf wai me ya sa kai ka zaɓi kullum kake faɗar abin da ba haka ba ne? Yanzu mene ne amfanin wannan tsarana ɗin da kake?"

"Tsarawa"

"Eh mana in ba tsari ba mene ne"

"Soyayyar ce tsari Amina yanzu ina matsayin mijin ki amma don na miki kalaman soyayya shi ne tsari?" Ya faÉ—a yana jon takaicin abin da take masa ita kullum magana É—aya ce shi ne soyayya tsara zance ne ita kuma bata yarda da kalaman soyayya ba ya rasa gane wace irin mace ce ita

"To kai ma Abban Yusuf ka san dai an ce amfanin soyayya aure to mun yi aure a kan me za mu ke wahalar da kan mu yin wata soyayya da kalaman soyayya sai ka ce wasu farin shiga?" Ta jefa masa tambayar hankalin ta a kan wayar ta. Shiru ya yi don ya rasa ma bakin magana.

"Haka kawai ni ba budurwa ba ni ba amarya ba a ishe ni da wata kalamar ina son ki haba!. Ai na daɗe da sanin cewar kana sona ko sai ka yi ta maimaitawa kamar karatu, ƴaƴa biyu mai kuma ake nema a wata soyayya?" Ta ƙara faɗa har lokacin bai ce mata ko uffan ba don in da sabo ya saba, shi mutum ne ɗan soyayya yana son kulawa da nuna soyaya sai dai kash!.

Bai dace da mata ba wasu matan suna son kulawar miji da nuna soyayya amma sai ka ga daga an yi auren an gama cin amarci shikenan sai namiji ya ajiye soyayya a gefe sai dai kuma a fara zaman kurame ko zaman haƙuri amma ba na soyayya ba. Ita ga shi ta samu amma tana wofantarwa shi ya sa sai ya ringa jin babu daɗi kwata-kwata ya rasa ya zai shawo kan lamarin ga ta kuma da shegen masifaffan kishin tsiya amma bata iya kula da miji ba bata iya nuna masa kulawa ba ita ma in an nuna mata kulawar bata damuwa da hakan.

*SADDIQA*

Bayan sati uku abubuwa sun fara cunkushe mata, don babban abin da ta ƙara fahimta daga Aminu shi ne ba ya son yin aski daga askin matse matsi har aske kansa kuwa. Gashin hanatar sa ya taru haka na marar sa sannan uwa uba gemu da gashin kansa babu gyara duk sun cunkushe. Gashin Hammatar har wani tsatsa-tsatsa yake idan ya fita wajen sana'ar sa ya kwaso rana ya dawo tamkar ta yi irin yadda warin ana yake bugun ta daga jikin sa.
Chapter 4 · 0% Book details