← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 44

Sashe 39

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da dare haka ya kwaɓe kaya ya hau mata gado tiƙiƙi, yana son haɗa jikinsa mai dauɗa da nata tsaftattacen jikin, wannan ya sanya ra ji duk ta tsani kanta, amma babu yadda za ta yi ta hana shi kanta saboda gujewa tsinuwar mala'iku, haka ya kusanceta damuwarta ma soshe-soshe musamman cikin kansa wanda duk tunaninta dauɗa ce bata san cewa kwarkwata bace.

A wannan daren mutane biyu ne suke cike da ɓacin rai kasancewar wannan daren da Aminu da Saddiqa suka raya, Zulaiha wacce kishi ya hana bacci tana ta saƙe-saƙen abubuwan da su Saddiqar suke gabatarwa, sai kuma Yaya Shafi:u wanda tun lokacin da ya yi arba da rigar baccin jikin Saddiqa ranar da Zulaiha ta yi wa Aminu ihun kwarto ya ji ya kamu da son kasancewa da ita, wani irin shauƙi da shaiɗan yake ƙiyasta masa a kan matar ƙanin nasa, hakan ya sa yake jin zafi da zugi a ransa don ya san yau Aminu ya koma ɓangaren Zulaiha.

Yana rayawa a ransa cewa an ce idan ka ga wata mace ta birge ka ka koma ga matarka ta gida, to sai dai a nasa ɓangaren abin ba haka yake ba, domin kuwa a halin da yake ciki yanzu da yake jin tunanin wata ya hana shi sukuni, watan ma matar auren, matar auren ma matar ƙaninsa, amma a sannan ne idan ya juya ga tasa matar da take kwance shame-shame a kusa da shi sai ya ji wani ɗoyin rashin tsafta da warin hammata yana tashi daga jikinta. Bakinta da ta buɗe wayam tana bacci wani warin baki ne yake fita, hakan ya sa daga ya doso gare ta sai ya juya can ƙarshe gadon da sauri yana mayar da numfashi tare da yin da na sanin a kan kasancewar Sumayya matsayin mata gare shi.

Tun daga wannan rana ya zamana rabon kwana ya koma kwana bibbiyu, wanda Zulaiha babu abin da ya yi saura a lamuran ƙazantarta sai abin da ya yi gaba, musamman da ya kasance ɓollowar ciki a jikinta, wanda ya dagulawa Aminu lissafi don shi dama cikin Saddiqa ma ba so yake ba bare kuma yanzu abu ya haɗe masa biyu. Ƙazantar Saddiqa ta yi tsamari da tunbatsar da komai ta cunkushe saboda laulayin ciki, hakan ya sanya Saddiqa ta sallama mata kicin, ta biya kuɗi aka mata kicin na langa-langa ta kwashe kayanta ta mayar can, saboda ba za ta iya cigaba da cuɗanya w kicin ɗaya da Zulaiha ba. A ɓangare ɗaya nata cikin yana girma, inda har ya kai matakin haihuwa, lokacin na Zulaiha kuma watansa uku.

Allah ya sauki Saddiqa lafiya inda ta haifa ƴarta mace, Babansu Aminu ne ya ce a saka mata Fatima sunan autarsu inda suke kiranta da Nihal. Tun da Saddiqa ta haihu aka kawi mata mai zaman wanka sai gabaɗaya Aminu ya ƙwaura ɓangaren Zulaiha, duk da ba haka ya so ba, amma hakan ya zama dole a gare shi, ga kuma tasa ƙazantar da babu abin da ya yi saura sai dai cigaba.

Bayan Saddiqa ta yi arba'in sai ta nuna masa dole sai ya canja halayya don ita ba za ta juri zaman wannan da shi a haka ba, ga kuma ƴarta kar ta taso a haka tana koyi da shi, lamarin da ya kawo musayar yawu da tashin hankali don sai Aminu ya nuna ita bata isa ta sauya masa ra,ayinsa ba ki ta sanya shi dole, dama tun da ta haihu yake jin haushinsa saboda yana ganin ta ƙara ɗora masa nauyi ne, ga kuma Zulaiha ita ma da nata guzurin cikin.

Hakan ya sa Aminu ya buɗe wuta, yake taka duk wanda ya so kuma yana nuna babu wanda zai saka shi ko ya hana shi daga Zulaiha har Saddiqa. Ita Saddiqa yanzu sau ta yi sati bata ga Aminu ya saka kaya mai wanki ba, duk ya yi baƙi haƙoransa sun yi yellow tamkar mai cin goro, ƙafafunsa faso babu kyan gani, hammatarsa kuwa tamkar za a yi kitso saboda tsawon gashi, hatta mararsa biyuyu da gashi, sannan tun lokacin da Saddiqa ta gane yana da kwarkwata, a washe garin ranar da ta karɓi girki da safe, tana gyaran gado ta ga kwarkwatar a kan filo guda biyu a kan zanin gadon kasancewar zanin gadon fari ne, ta shiga tashin hankalin da har sai da ta zubar da hawayen baƙincikin auren ƘAZAMI irin Aminu.

Ta nemi magani har sai da ta ga kwarkwatar ta mutu, amma da yake a kan Zulaiha ya kwasa yanzu ma ya sake kwaso wata kwarkwatar ita kuwa Saddiqa duk ranar da yake ɗakinta sai ta yi shimfiɗa a ƙasa ta kwanta, tun da ta ga yanzu da ta haihu ma kansa rawa yake, kamar dai wanda yake kula ƴanmata.

Hakan ya sa yake mata wulaƙanci, bai san cewa ita ta fi kowa baƙincikin zama da shi ba, ga yayansa da yake mata kallo mai ma'anoni da dama hakan ya sa ta ji duk gidan ya gundure ta.

Watan ta biyu da haihuwa lokacin cikin Zulaiha yana da wata biyar, a sannan ne Aminu yake ganiyar neman macen aure wacce za ta maye masa gurbi, saboda yana ganin Saddiqa ta haihu yana mata ganin budurcinta ya kau, duk da wata budurwar ma ba za ta faÉ—a mata matsi ba, kasancewarta mace mai kula da kanta amma da yake hankalinsa ya yi gaba sai yake hangen wasu, tun da ita dama Zulaiha ma ba ya saka ta a layi don a ganinsa ita ta gaza ta fannoni da dama, tun ba a je ga haihuwa ba.

Aminu yanzu idanunsa da suka shiga yawon neman matar aure basu yi masauki a ko ina ba sai a gidan yarbawan unguwarsu, gidan gidan haya ne inda wani bahaushe ya gina yake bada haya shekara da shekaru. Maman iyabo sun dawo arewa ne daga kudu inda mijinta ya kama musu haya, suke zaune, asalinsu ba musulmi bane amma zaman su a cikin musulmi da yake Allah ya saka suna da rabo sai suka musulunta.

Maman iyabo da baban iyabo ƴaƴansu biyu iyabo wacce ta rasu tun tana ƙarama sai kuma Aisha wacce bayan sun musulunta suka haife ta. Aminu ya san gidansu kuma ya san Aisha, tun tana budurwa take gasa masara mamanta kuma ƙosai take yi. Aisha ta auri wani bahaushe inda auren bai je ko ina ba ya mutu, duk da shi Aminu bai san mene ne silar mutuwar auren ba.

Aisha irin manyan matan nan ne masu ƙiba da cikar haiba, amma baƙa ce tana da manyan gaɓɓai tamkar namiji haka yanayin jikinta yake. Aminu tun da ya ganta ya ji duk duniya bashi da wani buri da ya wuce auren wannan matar inda ya shiga mata hidima, yana ƴar tsafta da kwaskwarima don ya samawa kansa matsugunni a zuciyarta saboda aurenta yake son yi da gaske.

Bai sanarwa da su Saddiqa yana neman aure ba, duk da abubuwa da dama sun nunawa Saddiqa haka, don in har mijin mace yana neman aure duk takatsantsan É—insa na kar ta sani tana iya ganewa sai dai ba lallai ta fahimci hakan ba

Bai faɗawa Umma ba don ya san ita tamkar adawa take da aurensa, kullum maganarta ɗaya ita ce ya tsaya ya samawa iyalansa nutsuwa da shi kansa. Baba jin inda Aminu ya ɗakko dala babu gammo sai ma ya ji ya fi Aminun farinciki tun da mahaifin yarinya yana da kamala kuma kowa ya yaba da tarbiyar yarinyar kasancewar ana zaune waje ɗaya shekara da shekaru. Baba ya amince inda Umma faɗa tamkar ta ari baki, sai dai babu yadda za ta yi tun da ita ma ƙarƙashin Baba take umarni yake bata, shi Baba yana kafa hujjar cewar indai yaro aure zai yi ba zai hana shi ba da a ce yana zina gwara auren.

Ita kuma tana hangen na gidan ma da ya suka ƙare, bare kuma yanzu ya je zai auri wacce yarensu ba hausa ba, amma dai ta san kowa ya shiga rayuwar wani akwai darasin da yake ɗauke da shi, tana fatan Aisha ta shiga gidan Aminu da darasi mai ƙarfi wanda za ta zama silar warkewar ciwukannda zukata suke fama da shi a dalilinsa.

Gida ya kama haya, ɓangare uku ne a gidan kowanne ciki da falo da bayi, kicin ne guda ɗaya, sai kuma ɓangaren Aminu wanda ɗaki ɗaya ne babu bayi a ciki.

Kasancewarta bazawara aka yanke aure wata guda, yau da ya rage saura sari uku biki shi ne Aminu ya kirawo Zulaiha da Saddiqa domin faɗa musu auren da zai yi, saboda Umma ya roƙe ta faɗa musu ta ce babu ruwanta ya je ya yi abin da ya ga ya dace.

Zaune suke a falon Saddiqa don dakyar Zulaiha ta zo shi ma sai da Aminu ya mata muzurai, sanye take da zanin falle da riga tshrt wacce faÉ—in ya mata yawa amma saboda yadda take jin daÉ—in saka kayan a haka take sakawa.

Ita Zulaiha ta ɗauka sulhu ne zai yi, a kan rashin mutuncin da yake zai nemi yafiyarsu, shi ya sa take ta wani shan ƙamshi, saɓanin Saddiqa da dama tana lura da takunsa, ta san dai yana waya kuma tana ganin ana kiransa, amma bata san har yana da burin yin aure a kwana kusa ba wanda ya rage sati uku!

Gyaran murya ya yi hannunsa É—aya a kansa yana susa ya fara magana kamar haka...

*MUN ZO GANGARA A BOOK 1 SAURA SHAFI ƊAYA MU KAMMALA WASU TUNI SUN BIYA KUƊINSU BOOK 2 SUNA ZAUNE A PAID GROUP DA ZARAR MUN DATSE ZA SU CIGABA DA SAMUN LITTAFIN HAR ƘARSHE. IDAN KEMA KINA SO ZA KI IYA BIYAN 500 KACAL DON JIN TIRKA-TIKRA DA CAKWAKIYAR DA ZA MU NUTSA A WANNAN LITTAFI NA ƘAZAMIN MIJI,*

*BAN CE NA IYA BA, BAN CE NA ƘWARE BA, NI DAI TAKEN ALƘALAMINA KAƊAI NA SANI WATO ALƘALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME*

*ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222*
[5/5, 6:39 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/J171xDTqqkq4e6hp9PBZU7

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
Chapter 39 · 0% Book details