Sashe 43
Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma yau da take ganin za a yi amarci dole za a buƙaci yin wani abu, kenan tsaftace ko ina ya zama dole saboda kar ɗaya ya cutar da ɗaya. Cikin ɗan jin nauyi ta muskuta mazaunanta, Aminu yana bin mazaunan da kallo ta ce
"Al'amin ya baka wanke baki ba" Dimmm gaban Aminu ya faɗi jin wata sabuwa da sauri ya shiga dariyar yaƙe yana cewa
"Ai na wanke da safe" Ya faÉ—a rashin gaskiya yana bayyana a tare da shi, don shi ko brush ma bashi da shi, a halin da ake ciki ma ba zai ce ga ranar da rabonsa da ya wanke baki ba. Bidik ya sauko daga gadon yana cewa
"Bari ki ga in je in yi, saɓi biyar zan yi, ina yi ina maimaitawa" Ya faɗa yana ƴar dariya gabansa yana faɗuwa, ita kuma Aisha tun da ya ce ya wanke da safe sai ta masa ayar tambaya tana ta mamaki.
Yana fita daga ɗakin, ya kama hanyar ɗakin Saddiqa sai dai ta rufe ƙofa amma haka ya buga ta buɗe, tana kallonsa ta ce
"Ango ka sha ƙamshi" Bai amsa ba ya ce
"Brush za ki aramin" Wata dariya ce ta so ƙwace mata amma sai ta dake ta ce
"Brush kuma? Dama ana aron brush?" A ƙufule ya ce
"Idan ba za ki aramin ba shikenan" Tana danne dariyarta a ranta ta ce
'To ni na ara maka brush kuma ai na sallama shi' A fili kuma ta ce
"Akwai wani sabo bana amfani da shi, bari na baka" Cike da murna ya washe baki, tana miƙo masa har da maikilin ya shiga saka mata albarka, ita dai bata ce komai ba kawai dai tana son ganin diramar auren ƙabila da Aminu.
Buta ya je ya cika ya tafi bayin tsakar gidan, sai da ya cika kan brush É—in taf da makikilin, ya shiga wankewa, jini bakin ya ringa yi kasancewar bakin ba ya samun wanki. Sai da ya wanke sau biyar don har ya fara jin duk ya karce dadashi duk don ya birge amarya.
Da ya koma É—akin ya same ta ta sanya kayan bacci, cikin ganin ta ruÉ—a shi ya ce
"Amarya ta ango" Yar dariya ta yi don har lokacin tana cike da tambayar dalilin da ya sanya tun da ya wanke baki da safe bai sake ba. Ta ce
"Na'am angona na biyu, ni ai na san daga kai na rufe wani namijin, dama can mijina na farko wanka yake yi sau ɗaya a rana, wannan ne babban dalilin da ya sanya muka rabu, ni duk inda ƙazanta take bana son in raɓe ta" Suuuttt wata tusa marar ƙara ta kufcewa Aminu lokaci guda ya haɗa zufa, murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce
"Amma wannan an yi ƙazami" Yana tuna shi da sai ya rufa sati jikinsa bai ga ruwa ba, ko jikin nasa ya ga ruwa to ba za a samu sabulu ba, to an rabu da mai wanka sau ɗaya ina ga shi, dariya ta ce
"Kai ma ka faÉ—a" Daga haka sai suka lula duniyar ma'aurata, tun daga fara É—an wasanni kafin a je ga mai É—ungurugum, hannun amarya na dama ya sauka a tsakiyar hamnatar Aminu, inda ta ji lallausar fatarta ta sauka a cikin wani cumus É—in gashi mai gaushi, idanu ta zaro shi kuwa gogan bai san mai ake yi ba, kafin ta gama mamaki sai ta ji mararsa ta gogu da jikjnta inda nan ma ta ji wani gashi, biyubiyu.
Hankalinta tashe ta shiga damuwa, tana mamakin yaushe mutum zai bar gashi haka a jikinsa, ita tun da ta kai munzalin gashi ya fito mata bata taɓa bari gashi ya kai ko rabin na jikin Aminu da ta ji ba.
Ana sunna tana kukan zuci, zuciyarta tana ƙuna, ta shiga tashin hankali amma dai tana son tabbatar da zarginta.
Da asuba bayan sun yi wanka sun yi alwala, Aminu da yake ƙoƙarin saka wando sai kare jikinsa yake kar amarya ta ga gashin nan, ai kuwa sai gani ya yi amarya tana kallonsa wajen ƙasa-ƙasa a ransa ya ce
'Ai indai baka yin abu ka ce za ka tarka to kuwa sai an samu matsala' Ya faÉ—a a ransa don yana ta zuci-zucin ya yi aski saboda amarya amma zumuÉ—i ya mantar da shi.
Amarya kuwa ta shiga kokwanto a kan ango, ta ɗora masa ayar tambaya. Haka suka yi nafila, don ma kar ya ƙara wani laifin sai ya saƙala takalmansa ya ce ya tafi masallaci, don ya lura Aisha ma tana da riƙon addini kamar Saddiqa. Tana masa a dawo lafiya ya tafi, bayan tun da suka tare a gidan ma bai taɓa zuwa masallacin asuba ba.
Ko da ya dawo dai ya lura da sauyi a fuskarta sai ya kasa sukuni, idanu ta ɗaga ta sauke a kan gashinsa wanda tun da fake zuwa wajenta yake ƙaƙaba hula, sai yanzu ta lura gashin ba ya samun gyara. Ganin gari ya ɗan waye suka koma bacci, bayan sun tashi suka sake yin wankan sabulu, wannan karon Aminu bai yi ha'ince ba ya yi wanka saboda yana son cirewa amarya kokwanto don ya lura kamar tana zarginsa ne.
Tun da ta kalli ƙafar Aminu ta ga wani ɓaskara-ɓaskaran faso tamkar ƙazangare zai samu mafaka a ciki, sai ta hau salatina ranta, don ta lura da Aminu bai taɓa zuwa wajenta da normal takalmi ba kullum da kambas yake zuwa, sai ya ce mata wai yana jin daɗin sakawa ashe faso yake ɓoyewa, don ƙafar kamar ta tsoho ko baƙauyen mutum marar gyara haka ta koma.
Bayan sun karya sai ya fita, ta shiga gyara ɗakin, ita abin da ta lura kayan da ya cire na jiya su ya mayar da ya yi wankan, abin da bata sani ba kayan wankinsa suna nan tare banda kayan jikinsa babu wankakke, dama duk masu dama-damar na fitar bikinta ne kuma duk ya saka. Dama ta kai ƙyallyen da suka yi amfani da su banɗaki ta wanke ta shanya, yanzu kuma tana son sauya zanin gadon ne, tana shirin cirewa sai ta ga ƙwaro ƙarami yana tafiya, da ta zuba ido da kyau ta gane kwarkwata ce, mamaki ruɗeni suka rufe ta, tana tunanin yadda aka yi kwarkwata ta zo kan gadon tun da ta san bata da ita. Tsantsani ya sa ta cukurkuɗa zanin gadon da rigunan filon da ta cire don kwarkwata uku ta gani raɗo-raɗo sun ƙoshi da jini.
Jikinta har karkarwa yake lokacin da ta fito tsakar gidan, hango Zulaiha tana harararta bai hana ta gaishe da ita ba amma ta ɗauke kai, ganin Saddiqa za ta shiga ɗakinta ta ƙarasa tana gaishe da ita, ta amsa mata cikin sakin fuska, tana ɗan jin nauyi ta ce
"Don Allah in ba damuwa ina son tambayarki, amma mu shiga daga ciki" Dama Saddiqa ta bata suka É—higa É—akin, ta É—auki Nihal tana mata waya zuwa can cikin muryarta da kake gane ba asalin bahaushiya bace ta ce
"Don Allah ke ce uwar gidan Aminu" Kai Saddiqa ta gyara alamar eh. Cikin sanyin murya ta ce
"Ina son sanin waye mijinki" Da mamaki Saddiqa ta kalleta nan ta shiga faɗawa Saddiqa abin da ta gani a kan gadonta, murmushi Saddiqa ta yi jin tana haɗata da Allah ta faɗa mata gaskiya, Saddiqa kuwa ganin matarsa ce sai bata ɓoye mata komai ba.
Tsabar karkarwa da hannun Aisha yake sai da Saddiqa ta karɓi Nihal, idanunta yana kawo ruwa ta ce
"Wallahi ba zan juri wannan abin ba, ai ni ba zan ma iya shan ruwa a inda Aminu yake ba, don haka a yau ba sai gobe ba zai sawwaqe mini" Ta faɗa tana share hawaye. Haƙuri Saddiqa ta bata, sai Aisha ta ce
"Ba ina kukan komai bane ina kukan yaudarata da ya yi matsayinsa na ƙazami, amma na miki alƙawarin sai na gyarawa Aminu zama, sai na saita Aminu, sai na zamewa Aminu dodo a gidan nan" Murmushin gefen baki Saddiqa ta yi ta ce
"Aisha kenan, ba za ki iya da Aminu ba, Aminu a ƙazamai ma shi dole a bashi mulki ko sarauta" Baki Aisha ta damƙe da haƙori, fitowa ta yi ta je, ɗakinsa ganin halin da ɗakin yake ciki ya ƙara tada mata hankali, ɗakinta ta ɗau waya ta kira shi.
Dama wajen su Kabiru ya je, don ya ɗan bata waje saboda baƙi, ganin kiranta sai ya ɗauka ko har ta yi kewarsa ne, sai dai jin tana batun zuwa duba mamanrta babu lafiya kuma ta ce kar ya zo yanzu za ta dawo, hakan ya sany Aminu ya mata izini.
Wayarta ta saka a jaka ta É—auki kuÉ—i ta saka a jakar.
Napep ta hau ta nufi kasuwa, wajen masu siyar da soson ƙarfe na wanke bayan tukunya irin manyan nan ta je, guda uku ta saya ta kaɓata a waje guda. Ta wuce wajen masu siyar da klin viva manyan nan ta siyo guda huɗu, wajen da ake siyar da aska irin ta wanzamai da suke aski ta wuce ta saya wata mai kaifi ta, ta je wajen masu gugar kaushi ta siyo magogin kaushi, ta hau napep ta koma gida.
Tana shiga ta ajiye ledar a É—akinta, É—akinsa ta shiga bayan ta saka safar hannu, kayan Aminu karkaf mararsa wankin nan ta kwaso ta tare su libgi guda a tsakar gidan.
Wani ƙaton baho ta ɗakko sabo, ta cika da ruwa ta buɗe klin viva ta zazzage kusan rabi a ciki, ta kaɗa kumfar, duka kayayyakin da ta siyo ta fito da su ta ajiye a gaban bahon, aska, dutsin gugar kaushi, soson ƙarfe, sai kuma sheba da ta ɗakko a ɗakinta.
Saddiqa ce ta zo ta kalle ta da mamaki ta ce
"Ba dai ke kaÉ—ai za ki wanke wannan kayan wankin ba?" Ta faÉ—a tana kallonta, yatsina fuska Aisha ta yi cikin hasusarta da bata fita ta ce