← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 44

Sashe 19

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yammacin wata ranar laraba tana zaune tana yanke farce a ƙafafun ta da suke kumbure, wayarsa ce ta yi ƙara ganin sunan ƴar aljanna sai ya washe haƙora, da tashi zai yi daga wajen sai kuma don ya ƙona mata rai ya ɗaga wayar a gabanta ya ce

"Hello ƴar aljannata" Daga ɗaya ɓangaren Zulaiha ta ce

"Na'am É—an aljanna albishirinka" Ta faÉ—a cike da É—okin sanar da shi. Baki a washe ya ce

"Goro fari ƙal" Cikin murna ta ce

"Babana ya ce ya amince a yi bikina, wai na cigaba da karatun a É—akin mijina shi ne ya ce in faÉ—a maka ka turo manyanka"

*INA SANAR DA KU CEWA WHATSAPP SUN KULLE MINI WANNN ACCONT ÆŠIN 09013181851 YANZU DA WANNN NUMBER NAKE CHARTING 09025576222*

*DUK MAI BUƘATAR MAGANA DA NI YA MINI TA WANCAN ƊIN KAFIN SU BUƊE MINI ƊAYA, MAI SON LITTAFI KO KAYAN MATA NA KAMFANINMU NA MEERAH B HERBS KO KAYANA NA ZANNUWAN GADO TAKALMA ATAMFOFI DA SAURANSU YA TUNTUƁENI*

*MAMAN AFRAH 09025576222*

[5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*

BOOK 1
PAGE 11

Gaban Aminu ne ya buga da ƙarfi, jin wani ɗan jijjiɓin tashin hankalin kuma, a zuciyarsa ya ce

'Ana wata ga wata hallaw, ni da nake ta fama da matar ɗaya ma abu yana neman gagara, ita ma tana zaune da ciki turtsitsi ke ma ki zo da wanga batu' A fili kuma sai ya haɗiye wani yawu muduk, yana mai mayar da kallonsa kan Saddiqa da take yankan farcenta hankali kwance a zuciyarsa ya ƙara faɗin

'Saddiqa wannan abu ba ke kaÉ—ai ya samu ba har da ni, mata biyu ni Aminu ta ina zan fara É—awainiya da su' Ya faÉ—a yana jin tamkar ya kurma ihu. Saddiqa kuwa ganin ya tsare ta da ido sai ta ce

"Lafiya dai?" Ta faɗa tana kallonsa, yaƙe ya saki yana wani ciccira ido tamkar kwarton da aka kama a ɗakin amayar ya ce

"Babu komai Saddiqa cigaba da yankan farcen naki, ni ma kya aramin rezar in yanke" Ya ce bayan ya ɗan kawar da wayar saga kunnensa yana sakin wani yaƙen a karo na biyu. Saddiqa kuwa mamaki ne ya kamata ganin mutumin da ko kaɗan ba ya son ya raɓi tsafta, amma yau har yana batun zai yanke farce, duk da haka bata yarda da maganarsa ba don ta ga rashin gaskiya ƙiri-ƙiri a tare da shi ga wani uban gumi da yake wanke masa fuska da wuya, tamkar wanda ya yi wa sarki ƙarya. Daga ɗaya ɓangaren Zulaiha ƴar aljanna ta katse shi da faɗin

"Wai É—an aljannata ya na ji ka yi shiru? Ko baka yi murna da jin wannan kyakkyawan albishir É—in ba" Jin abin da ta ce sai ya tattaro jarumta ya tashi ya fita daga falon,

Takalmi ya saka ya fice daga gidan, yana zuwa ƙofar gida ya buɗe baki ya ce

"Kai amma Baba ya kyauta" Wannan kalmar kaɗai ya yi ƙarfin halin faɗa, don shi gabaɗaya sai ya ji an rikita masa lissafi ai shi tun da aka ce sai ta gama karatu ya ɗauka shekaru ne a nan gaba. Zulaiha jin amsar ta yi banbarakwai don ta ɗauka ɗoki da murnarsa ya wuce haka, cikin jin haushi ta ce

"Ni ban gane maka ba, yanzu in zo maka da wannan albishir amma ka ce wai Baba ya kyauta, sai wani kame -kame kake anya kana da gaskiya kuwa? Ko dai tsoron matarka kake?" Jin ta harbo jirginsa tana cewa yana kame-kame kamar dai bai yi murna da jin maganar ba sai ya saki wata dariya yana mai bayyana farinciki ya ce

"A haba ita ɗin banza, yo har akwai wata mace da za ta sa in ji tsoronta saboda ke, ai kawai i cewa Baban zan aiko kawai ya shirya watannin aure in ma shekara zai saka to, in kuma yana ganin ma har kya gama karatun ai duk ana kan hanya... Jin furucinsa sai ranta ya ɓaci cikin harzuƙa ta ce

"In ce maka ya janye batun karatun kake cewa wai in har na gama karatun, kuma da kake cewa watanni ko shekara shi cewa ya yi wata ɗaya zai saka" Ta ce ranta yana ƙuna, gabansa ne ya faɗi wai wata ɗaya, dakyar ya shawo kanta yana lallaɓa ta bata san gabaɗaya shi ta saka shi a matsala ba, ba wai ba ya sonta ba amma riƙon matan biyun ne ya sare.

Washe gari da daddare ya nufi gidansu, da Fatima ƙanwarsa ya fara cin karo don ita ta amsa masa sallama, bayan ya shigo ta ce

"Yaya barka da dare" Hannu ya ɗaga mata bai amsa ba, saboda ya lura yarinyar nan ta ga makwancinsa don ko ranar da ya zo ɗaukan gajerinan wanduna sai da ta leƙa ɗakin nasa, tana tambayar ina zai kai wannan tsumman ko ƙonawa za a yi ya bata ta ƙona a murhu. Ita ma ta faɗi hakan ne saboda ta san wataƙila gidansa zai tafi da su saboda ta san mai hali ba ya canja halinsa, amma wata uwar harara da ya jefe ta da ita, hakan ya sa ta bar wajen ba shiri.

Falon Babansu ya wuce a can ya same su shi da Umma suna ɗan taɓa hira, bayan ya gaishe su Umma take tambayarsa Saddiqa ya ce tana lafiya. Kai ya sunkuyar yana son faɗar maganar gidansu Zulaiha Umma ce ta ce

"Aminu lafiya kuwa? Ko dai Saddiqar ce babu lafiya?" Murmushi ya saki yana mai sosa ƙeya ya ce

"Lafiyarta ƙalau, kawai dai ina tafe da wani batu ne" Kallon tsaf Umma ta masa tana jin bata yarda da batun nasa ba amma sai ta ji Babansa ya ce

"Mene ne Aminu" Jin abin da Baban ya faÉ—a ya shiga zayyana abin da yake tafe da shi cikin É—ari-É—ari.

Wani salati da Umma ta kwasa, shi ya sanya shi É—agowa yana kallonta, tana dire salatin ta shiga faÉ—in

"Aminu ashe baka da hankali? Yanzu yarinyar nan mai ladabi da biyayya, tana ɗauke da ciki za ka je mata da batun ƙarin aure, kai yanzu ko wani ya ce ka yi aure ai ka ce ba yanzu ba am... Maganar da Baba ya yi ce, yana mai ɗaga mata hannu ita ta dakatar da ita daga faɗa da ta fara masa ya ce

"Yanzu ke mene ne na tada jijiyoyin wuya, kawai don ya ce zai ƙara aure, sunnar ma'aikin kamar dai ya ce zai yi saɓon Allah" Wani murmushi Aminu ya yi yana mai sunkuyar da kai, jin Baba ya goyi bayansa ji yake kamar ya tashi ya taka rawa. Kallon Baba Umma ta yi za ta ce wani abu amma ya ƙata dakatar da ita da faɗin

"Ku mata dama ai bakwa ƙaunar kishiya, kin ga idan kika yi amfani da kalmar bahaushe da yake cewa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ba za ki so a mata kishiya ba" Jin furucinsa sai Umma ta buɗe baki wannan karon bai dakatar da ita ba, ta ce

"Yarinyar nan ba ƙaramin haƙuri take da Aminu ba, amma kuma maimakon ya bari ma ta haihu duka yaushe aka yi auren?" Murmushi Baba ya yi tare da faɗin

"A rana ɗaya ma ana iya ɗaurawa namiji aure, da mace sama da ɗaya, kin ga kenan ƙara aure bayan watanni ba zai zama laifi ba, sannan a zaman aure ai kowa haƙuri ake da juna ba wai mutum ɗaya ne mai haƙurin ba" Bata ce komai ba don ta san ko kwana za a yi ba zai sakar mata ba, kallon Aminu ta yi ta ce

"Ka faÉ—a mata?" Cikin sanyin murya ya ce

"A'a so nake sai abu ya kankama" Tana mai jin takaicin furucinsa ta ce

"Allah tabbatar da alkairi" Baba ne ya ce amin don shi Aminu ya sunkuyar da kai" Gyara zama Baba ya yi ya ce

"Zan sanar da kai lokacin da za mu je sai ka faÉ—a mata, ita kuma sai ta sanar a gidan nasu, Allah baka ikon yin adalci" Daga haka ya shiga yi wa Baba godiya ya musu sallama ya fita.

Yana fita Baba ya kalli Umma ya ce

"Ki godewa Allah, da har aure ne a ransa ba wai neman mata ba, nawa suna da auren amma suna neman matan waje , kawai ki masa addu'a Allah bashi wuyan ɗauka tun da dai har yana sana'arsa" Kai kawai ta gyara don takaici ma ya hana ta magana, tana tuna Saddiqa da irin haƙurin zama da shi da take, fa shegiyar ƙazantarsa.

Aminu yana fitowa suka yi kiciɓis da Fatima, ta zo wucewa ta wajen falon Baba kallon tsaf ya mata kawai sai ya ji bai yarda da ita ba, cikin kakkausar murya ya ce

"Ke zo nan" Tahowa ta yi sai da ta zo cikin girmamawa ta ce

"Gani Yaya" Yana aika mata harara ya ce

"Ba ke uwar ƴan rawar kai ba, mai shegen surutu idan kika sake ƙaiƙaiyin bakin ki ya sa, kika faɗawa Saddiqa wata magana ni da ke ne" Kallon rashin fahimta ta masa ta ce

"Wace magana kuma Yaya?" Bai faÉ—a mata komai ba ya sake cewa

"GargaÉ—i nake miki dai" Yana kaiwa nan, ya tafi ya barta tsaye tana ta mamaki wace magana ce wannan da yake ta faman faÉ—in kar Saddiqar ta sani.

*BAYAN KWANA UKU*

Su Baba sun je nema masa aure, sun bayar da kuÉ—in gaisuwa sannan a wajen aka tsayar da rana da yake har kayan sa ranar Baban Zulaiha ya ce su kai kawai a yi zama É—aya. Fatima ta ji ciwon auren nan da Yayanta zai yi amma dai sai ta yi addu'ar Allah sa ta kirkice kuma mai tsafta kamar Aunty Saddiqa.

Bayan kwana biyu, yana zaune a falo tana shan garin kwaki da suga da madara, sai gyaɗar da ta saka a ciki. Aminu ne ya zo ya zauna a kan kujera da yake ita a ƙasa take a zaune ta miƙe ƙafa ɗaya, ɗayar kuma ta lanƙwasa ta. Cikin izza ya dube ta yana wani shan ƙamshi ya ce
Chapter 19 · 0% Book details