Sashe 33
Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi Aminu ka tashi, don ba zan bar É—akin nan ba sai tare da kai" Ganin ta kaÉ—e masa hankali jin an shiga sallah ya fito daga É—akin ya barta a ciki, banÉ—akin Saddiqa ya nufa amma cikin rashin sa'a ya same shi a kulle, dawowa ya yi lokacin ta idar da raka'atainil fajr ya ce
"Saddiqa ina mukullin banÉ—akin?" Cikin rashin fahimta ta ce
"Mai za ka yi da mukullin banÉ—akina" Ya ce
"Shiga zan yi mana" Ta É—an yi jim sai ta ce
"Ai ba a bakina ba kake, don haka ka je ka shiga banɗakin amaryarka, kuma ina ƙara maka tuni sai nan da sati huɗu da kwana uku ne za ka dawo kwana ɗakina" Tana faɗar hakan ta tashi ta kabbara sallah, hakan ya yi daidai da fitowar Zulaiha, yana ganinta haushinta ya cika shi, ya juya ya nufi ɗakin Zulaihar ransa yana ƙuna ita kuma Zulaiha ta mara masa baya.
Tun da ta shiga É—akin take balbala masa masifa, wai ya ci amanarta ya satar mara kwana, dakyar ya yi sallah tana masa masifa ita kuma ko sallar bata yi ba, da ya idar ya kalle ta ya ce
"Ke yanzu Zulai...
"Wallahi ka daina faÉ—a mini Zulai na faÉ—a maka" Sai ya sake cewa
"Yanzu Zulaiha abin da kika yi kin kyauta, waɗannan fa yayuna ne amma kika faɗa musu magana son ranki ko kunya bakya ji" Kallonsa take sheƙeƙe ta ce
"Kunya? Wace irin kunya, ai ni abin kunya gaba na bashi ba baya ba, kuma da kake kiransu yayunka ai ba iyayenka bane, sannan ni ko daga wajenka ban ga kana girmama su ba, ni ma don ban yi ba ai ba za ka zargeni ba, sannan ina so ka sani batun karatun da na ce zan cigaba da yi a gidanka na fasa dama tun a gida na sanar cewa babu batun karatu kuma an amince mini, don ba zai yiwu in zo ina tafiya makaranta kuna keɓewa da kai da wancan matar taka kuna cin amanata" Tun da fara yake kallonta ganin ba saurarawa za ta yi ba ya ce
"Zulaiha takun da kika shigo gidan nan da shi kinwatsar, saboda ba zan É—auka ba, sannan ina so ki sani ni nan Aminu bani da mutunci nima don ko matata Saddiqa tsorona take ita da ta shafe watanni ma a gidan bare ke da ko sati biyu baki haura ba" Kallon sakarai ta masa ta ce
"Saddiqa ka ce ni kuma Zulaiha nake, tsakanin harafin sunana da sunanta akwai tazarar haruffa bakwai, don haka ka sani babu gudu babu ja da baya" Banza ya yi da ita ya ce
"Ki je ki yi ta yi amma ki sani za ku zuba ne É—an halak ka fasa" Ta yatsina fuska ta ce
"To shikenan, ina ƙara maka gargadi da cewa muddin ka ce za ka koma wajen waccana matar taka a cikin kwanakina da ka mallaka mini to ka sani za a yi faɗuwar baƙat tasa, za a yi haihuwar guzuma don wallahi babu wanda ya isa ya taka Zulaiha" Ganin da gaske take faɗan har jijiyoyin wuyanta suna tashi sai ya ƙyaleta a kan cewa zai je gidansu ya sanar da Umma halin da ake ciki, don shi ya fara takura da rashin Saddiqa.
Har wajen tara sannan ya fita, ko wanka bai yi ba wani farin yadinsa da ya koma milik ya saka, don ko abin karyawa bata yi ba tana zaune sai uban soshe -soshe take.
Gidansu ya wuce yana so daga can sai ya wuce kasuwa wajen sana'arsa. Umma ya samu tana zubawa tattabaru abincin, da sallama ya shiga ta amsa, ganinsa sanyi ƙalau sai ta ji duk babu daɗi don dama ta san duk namijin da ya ce zai haɗa mace sama da ɗaya to tabbas ba zai rabu da damuwa ba, duk da ta san Saddiqa tana da haƙuri amma dai ba za a rasa kishi ba.
Bayan ya gaishe ta, ta kalleshi ta ce
" Aminu lafiya dai?" Hannu ya kai ya sosai gashin kansa da ya taru ba ya samun aski ya shiga zayyane mata halin da gidan nasa yake ciki. Kallonsa Umma ta yi ta ce
"Hmmm! Dama ai duk wanda ya saya rariya ya san za ta zubda ruwa, yanzu kai saboda rashin adalci da kuma rashin tsoron Allah, ka ƙwacewa Saddiqa kwanan sati guda, anya Aminu kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Rarinyar nan ko shekara bata yi ba da aurenka ka mata kishiya, sannan baka tsaya a nan ba don ka musguna mata za ka ba kishiyarta bakin kwananta?" Tunda ta fara magana ya sunkuyar da kai, lokaci zuwa lokaci yana sosa kansa da yake ta masa ƙaiƙayi, ya ce
"Umma ni fa ba don musguna mata na ce hakan ba, ai gani na yi ita Zulaiha amarya ce" Umma ta ce
"Wato amarya sai a bata kwananta wata? Yanzu don Allah kalli kayan jikinka, ko wanki babu baka ji yadda warin dauɗa yake tashi ba Aminu, yanzu a ce wannan kayan mai datti a jikin magidanci mai mata biyu, shin sai yaushe za ka gyara wanann ƙazantar da kake fama da ita, ai wallahi mace mai zama da kai sai ta kai zuciya nesa, kuma dole ka siyawa kanka raini wajen mace shi ya sa ma Zulaihar ta rainaka" Da sauri ya ce
"Umma dama fa Zulaiha ita ƙazama ce, wallahi da na yi baƙi ranar nan baki ga kwamacalar da ta haɗa musu ba, wai ta kaɗa lalle a matsayin kuka, ta dafa zabuwa da suga Umma wai girkin indiya da na marocco ta musu... Dariyar da Umma ta fara shi ya katse masa maganar ya ɗago yana kallonta. Sai da dariyar ta tsagaitawa Umma sannan ta ce
"Kuma sun ci girkin Æ´an indiar ko na maroccon suka ci" Ta tambaya cike da gatse. Aminu da bai fahimci magana Umma ta faÉ—a masa ba sai ya É—ora da faÉ—in
"Wallai basu ci ba Umma, hasali ma ƙusa ta saka wai don naman ya yi saurin dahuwa amma bata cire ƙusar ba ta zuba musu a ciki, ranar na kunyata Umma, abin haushin har rigar nono ta je... Kafin ya kai aya Umma ta dakatar da shi don duk ta fahimci inda ya dosa ta ce
"Babu ruwana da duk wani ƙorafinka Aminu, yanzu wannan maganar da ka zo danita a kan maganar kwana shi ma zan je in kashe case ɗin ne saboda Saddiqa, tun da haƙƙinta ne amma sauran sai dai ka faɗawa Babanka tun da ni baka ji shawarata ba lokacin da ka ƙara aure" Kai ya shiga sosawa hannu biyu ya ce
"Umma ita fa Saddiqar da bakinta yau ta ce, sai dai in ƙara sati biyu a kan wanda na ɗaukawa amarya, wai ya zama wata guda, kuma wallahi amaryar nan bata son gyara kanta Umma wanka ma wai ba za ta yi da sabulu ba wai ɓarna ce gwara a cancanta" Baki Umma ta cije ta ce
"Ka ce tuwona maina aka yi kai da Zulaiha, wato zani ce ta tarar sa muje mu, ita ƙazanta kai ƙazanta dama ai gwano ba ya jin warin jikinsa, ita kuma Saddiqa haushin abin da ka mata ne ya sanya ta faɗi hakan amma zan je in lallasheta" Kai ya kaɗa yana sosa kai da hannu ɗaya, ɗaya hannun yana sosa wuyansa, kallonsa Umma ta yi ta ce
"Wai ni Aminu susar nan kuwa ta lafiya ce kake yi?" Yana susar ya ce
"Umma kaina ne yake wani mugun ƙaiƙai wallahi, kuma sai in ke jin kamar wani abu yana yawo a cikin kan, har sai na sosa, kuma wallahi ko a cikin mutane haka nake fama Umma" Mamaki ta yi tana ta kallonsa ta ce
"Inda miƙo mini kan naka in gani" Kan ya miƙa mata, tana jin warin gashij da gumi da ya cakuɗe, ga warin jikinsa na rashin wanka, haka ta shiga buɗe cikin gashin don ganin mene ne, cike da mamaki a maganarta ta ce
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Aminu ka san mene ne a cikin gashinka? Ka san mene ne cunkus a gashin?" Da mamaki ya É—ago yana son jin mene ne wannan wanda ya sanya Umma faÉ—in haka ya ce
"Mene ne a ciki Umma?" Umma da ta ga abin da ta gani, har guda É—aya ya gangaro wuyansa yana yawo a jikin farin kayansa....
*MUNA GAB DA GAMA BOOK 1*
*GA MASU BUƘATAR BOOK 2 NA ƘAZAMIN MIJI ZA SU BIYA 500 KACAL DOMIN JIN LABARIN HAR ƘARSHE, AKWAI CAKWAKIYA, SARƘAƘIYA, TURKA-TURKA, ZAN IYA CEWA A GABA ZA MU NUTSA CIKIN LABARIN*
*ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY*
*SHAIDAR BIYA TA 09025576222*
*INA SAYAR DAMAGUNGUNAN MATA MASU INGANCI NA KAMFANIN MEERAH B HERBS, AKWAI MAGANIN MATA, AKWAI NA RAGE TUNBI AKWAI NA RAGE ƘIBA, AKWAI NA GYARAN NONO, AKWAI NA ƘARA ƘIBA, AKWAI MAGANIN CIRE NANKARWA, DA SAURANSU*
*AKWAI ZANNUWAN GADO, LABULAYE, FRAMES MAYAFAI MASU BEAD WORK, MAYAFAI NA SHAGO, KAYAN YARA, TAKALMA, LESUNA, ATAMFOFI* *DA* *SAURANSU*
*MAI BUƘATA YA MINI MAGANA 09025576222*
[5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo
*KAZAMIN MIJI*
NA
MAMAN AFRAH
First Class Writer's Asso.ðŸ“
Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 16
Mamaki fal a fuskar Aminu ya ce
"Ba dai kiyashi ne a shigar mini kai ba kwana da kwanakin nan da nake fama?" Ya faɗa yana kafe Umma da har lokacin ta ras bakin magana, rai a ɓace da haushin maganarsa jin wai yana batun kiyashi cikin masa gatse ta ce
"Tururuwa ce (Ant) Ta yi gida a cikin gashin naka" Aminu da bai fahimci gatse Umma ta masa ba cikin mamaki yana mai sosai kan tare da nutsa yasunsa cikin gashin ya ce
"Tururuwa Umma? Amma abar nan ta cuce ni wallahi, baki ga yadda nake ta fama ba amm dama Umma tururuwa tana shigarwa mutum kai, ko dai ba ta lafiya ba ce?" Haushi ma dakyar ya bari Umma ta ce