← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 44

Sashe 25

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce" To tun dare bai maka ba, ka tafi shago ka siyo, sabulun kayan lefen ne zan fitar ka suɗe shi ai na lefe na amarya ne, saboda adani shi ya sa tsawon sati ban ɗakko ko goga na yi na wanke fuska ba, wannan ajiyewa zan yi har ɗan da zan haifa a wanke shi da sabulun kayan auren ubansa, kuma ni ma dai in ina jego ai sai na ɗan wanka ko banza na wanke ƙarnin jego" Har sai da idanunsa suka kawo ƙwalla wai sabulun ne saboda adani za a ajiye har sai an haihu an yi wa ɗa wanka da shi, ko cikin ma babu kai jama'a.

Magiya ya shiga yi mata, a kan cewa zai mayar mata da haka ta É—akko guda É—aya ta bashi, tana cewa sai da ta danne zuciyarta.

Lallaɓata ya yi suka yi wankan tare don sai da ya dirza mata bayanta, suka fito suna ɗan ƙamshin sabulu. Bayan ta shafa mai ta buɗe drower ta ɗakko atamfarta, wacce tun tana gida dama ta kwaso wasu daga cikin kayanta don ta ce va yanzu za ta fara ɗinka na lefe ba, saboda adani.

Kallon atamfar ya yi duk ta sha jiki, ta koÉ—e ya ce

"Mu da za mu yi baƙi" Daƙayar ta yarda ya ɗakko mata wani leshi daga cikin kayan fitar biki, tana ta mitar ita da ba wani waje za ta je ba, zai sa ta saka sabon kaya. A nan ma sai da Saddiqa ta faɗo masa wacce kullum cikin ado da kwalliya take.

Bayan sun shirya shi ma ya saka wankakken kaya, ta shiga kicin ta fara ɗora ruwan tuwo, tun kan ruwan ya yi zafi bare a yi zancen tafasa, ta kwaso shinkafar tuwon ta zuba. Ta rufe ka ruwa bai ishi shinkafar ba, ta rufe ta koma ɗaki bayan ta haɗa kayan miyar ta tsayar da ruwan miyar. Jimawa can ta dawo, tana buɗe tuwo ta ga har ya fara ƙauri, ga shi shinkafar ta jiƙa babu batun dahuwa, wani wajen ma ɗanye ne haka ta sauke ta tuƙa ta mulmule. Miyar ta kaɗa da yake da bushashen kifi ta yi tana saukewa ta zuba a food flaks ta ajiye. A daidai nan Saddiqa ta shigo kicin ɗin ɗaukan kofi, ganin Zulaiha a ciki sai ta shigo da sallama, amma Zulaiha bata amsa ba, sai ma ta tsiri ƴar waƙa tana faɗawa Saddiqa magana ko ta kanta Saddiqa bata bi ba sai ta ba bango ajiyarta, ta ɗauki abin da ya kawo ta ta fita don gabaɗaya ƙaurin kicin ɗin ma tada mata zuciya yake.

Bayan fitar ta suka ci karo da Aminu, ya dawo riƙe da ledar zabuwa, ko kallonta bai yi ba, tana gaishe ya yi banza, don haushinta yake ji bata wa baƙinsa abinci ba ga shi kuma dai ashe amarya za ta share masa hawaye.

Yana shiga kicin ganin sabbin flaks a kan tire wani daÉ—i ya cika shi, gar da saka mata albarka ya rungume ta, yana aika mata da sumbata, ita kuma sai ta ji kanta ya yi wani gingirim ita ala dole ta birge miji.

Nan ya fita sayen lemuka ya barta tana dahuwar nama, tana gamawa ta kai ɗaki ta jera. A ɓangaren Aminu yana ƙofar shagon lemuka wayar Bukari ta shigo, yana ɗagawa suke sanar masa suna hanyar gidan nasa, nan ya faɗa musu inda yake suka je suka taho da shi. Yana gaba suna binsa a baya suka shigo gidan, tun daga nesa ya hango Zulaiha a ƙofar ɗakinta tana zaune a baranda, abin da ya gani ne ya mugun ɓata masa rai, shikenan ya san ta wargaza masa mutuncin da yake tattali a wajen abokan nasa, gashi su duka sun ganta....

ME TA YI? MAI YA GANI? AKWAI CAKWAKIYA FA MU HAƊU A PAGE 13 DON JIN AMSAR DA YADDA BAƘI ZA SU SAMU KANSU A ƊAKIB AMARYA

*GABAƊAƳA ZAN BAKU BOOK 1 DAGA FARKO HAR ƘARSHENSA A FREE, IDAN MUKA GAMA BOOK 1 GA WANDA YAKE DA HALI KUMA YAKE BUƘATA ZAI IYA BIYAN KUƊIN BOOK 2*

*INA SANAR DA KU CEWA WHATSAPP SUN KULLE MINI LAYINA 09013181851 YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI 09025576222*

~NA GODE MAMAN AFRAH~
[5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*

BOOK 1
PAGE 13

*YAYA SULE*

Da sauri ya danne makunnar wayarsa, sai kuwa waya ta kunnu, duk da gabansa yana tsananta bugu amma dai da dama -dama a kan a ce ta ga wayar a kashe domin, a take za ta É—ora masa alamar tambaya haÉ—e da tuhuma.
Hannu Amina ta miƙa masa a lokacin da ta tako zuwa gabanta, jikinsa babu ƙarfin tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Addu'a yake karatowa a zuciyarsa, ƙaran shigowar kira wayar wanda mai kiran tamkar jira yake a kunna wayar ya kira dama. Kaɗan ne ya rage Yaya Sule ƙwalla ƙara, saboda ya san kashinsa ya bushe, Amina kuwa har ta ƙagara ta ga mai kiran don har ta fara tunanin wannan anya kuwa
MAMUDAN ne?.

Yaya Sule cike da fargaba ya duba fuskar wayar, amma cikin iko da hikimar ubangiji sai ya ga sunan Babansa, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da sakin murmushin jin daɗin kuɓuta, cikin ƴar inda-inda ya ce

"Baba ne yake kirana" Ajiyar zuciya Amina ta sauke a fili, hatta Yaya Sule sai da ya ji saukar ajiyar zuciyar a zuciyarsa ya ce

'Yadda kike sauke ajiyar zuciya haka nake saukewa, bambancinmu kawai ni ɓoyayya na sauke ke kuma bayyananniya' Ya ce a zuciyarsa ita ma a zuciyarta ta ce

'Allah na gode maka, ashe dai Baba ne ya kira shi, har gabana ya faɗi ai bana so in ke ɗora zargi a kan mijina, duk da na san ba zai taɓa raɓar wata ƴa mace da sunan so ba, kawai dai sheɗan ne yake saka mini wasi-wasi saboda ba ya so a zauna lafiya' Wayar tana dab da tsinkewa ya ɗaga ya kara a kunne, bayan ya zauna ya ce

"Assalamu alaikum, barka da dare Baba" Daga ɗaya ɓangaren Baba ya amsa sallamarsa, bayan sun gaisa ya tambaye shi su Albani yake cewa sun yi bacci, nan ya shiga cewa

"Sule ni kuwa kun yi magana da Aminu, baka ji gidan su tsohuwar budurwarsa sun ce ya aika ba" Cike da mamaki Sule ya amsa da cewa Aminun bai tunkare shi da maganar ba, nan Baba ya kwashe komai ya faÉ—a masa, cikin sanyin murya ya ce

"Amma Baba da baka goyi bayansa ba, yanzu yaushe ma aka yi aurensa da Saddiqa, yarinyar nan tana ta fama da ƙazantarsa amma yanzu tun ba a je ko ina ba a ce zai mata kishiya" Amina da tun da ta fahimci bakin zaren zancen, ta saki wani murmushin jin daɗi da farinciki, a hankali ta ajiye wayarta, tasowa ta yi ta je kusa da Sulen ta zauna don ta ji ƙwal uwar daka. Baba ne ya ce masa

"Shi fa zai zauna da matarsa, ka ga bai kamata a tauye masa haƙƙinsa ba" Cike da tausayin Saddiqa Sule ya ce

"Wallahi Baba da ka ce masa ya haƙura ba... Hannun da Amina ta sakawa Sule a bakinsa, shi ya masa shamaki da ƙarasa maganar da yake son yi, kallonta ya yi take masa alamar ya daina cewa a hana Aminun, Baba kuma jin Sule bai ƙarasa maganar ba ya ce

"Ni dai na amince, kai ma ka amsa fatan alkairi, da a ce mutum yana bin mata gwara a ce yana da yawan aure-aure ka ga sai dai mutane su ce mutum yana aure É—anÉ—ane amma ba wai zina ba" Jin furucin nan na Baba, sai Sule ya buÉ—e baki don lokacin Amina ta É—auke hannunta daga bakinsa ganin maganar kuramen da take masa ta yi tasiri, ya ce

"Haka ne Baba, to Allah tabbatar da alkairi" Wannan maganar da ya yi sosai farinciki da annashuwa ya bayyana a fuskar Amina.

Son haka yana cire wayar daga kunnensa ta ce

"Haba kai kuwa, ya za a yi ka hana sunnar ma'aiki" Ta faÉ—a tana dariyar farinciki, kallonta ya yi ya ce

"Ina ga fa Amina baki gane inda maganar ta dosa ba, magana fa Baba yake a kan Aminu ya je masa da maganar zai yi wa Saddiqa kishiya" Hannu ta tafa, tare da kai hannun ɗaya haɓarta ta ti tagumin mamaki ta ce

"To kuma mene ne, abin da mutum babu ruwansa ai daÉ—in kallo gare shi" Kallonra ya yi yana tuna irin yadda ta tsani kishiya, amma kuma ga shi tana so a yi wa wani, shi ya sa dama ake cewa mata su ne matsalar kansu da kansu, ya ce

"Amma Amina ya za a yi abin da bakya son a miki, kike so a yi wa wata? Kar ki manta fa yarinyar nan ba a daɗe da aurenta ba, amma yanzu a bijiro da maganar kishiya ai da damuwa" Tsaye ta tashi tana kama ƙugu ta ce

"To ai shi wasa ma waje yake samu, abin da zai iyu ma shi ake yi, ka san dai ai ni bani da abokiyar zama har abada!. Ita kuma in ita ce ƙaddararta waye zai hana a mata?" Iska ya hurar daga bakinsa ya ce

"Allah bata haƙuri da dangana" Harara ta aika masa ta ce

"Dangana sai ka ce wacce uwarta ta mutu, ni sai wani tausayinta kake" ÆŠan shiru ya yi ya ce

"Ba haka bane kin san yarinya ce kuma shi Amina zama da shi sai haƙuri" Baki ta taɓe ta ce

"Kowa ma zaman haƙuri yake da nashi mijin" Tana gama faɗar haka ta koma wajen wayarta, kawai sai ya ji tana voice tana cewa

"Eh mana Aminu ƙanin mijina, wanda ya yi aure kwanannan" Mamaki ne ya rufe shi, daga haka ya zame ya fita siyan lipton ɗin, saboda ko ta kan karɓar wayar bata yi ba hankalinta yana ga bada labari.
Chapter 25 · 0% Book details