← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 44

Sashe 11

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ta shiga damuwa ganin ita tana ta fama da shi ya sauya halayyarsa ta ƙazanta da tsakaninsa da ubangiji, amma bai ji maganar ta ba ko don haƙƙinta, sannan yanzu ya ɗauki kayan da ita ta sha wahalar wanke su da goge su duk don ta faranta masa, amma a ƙarshe sakayyar da zai mata da ya saka su wajen mace zai je, tun da gashi nan tas kamar dai ba wannan Aminun da yake zaune da ƙazanta ba yana warin dauɗa.

Tana nan tana ta saƙa da warwara ta kasa jurewa don sai zuciyar ta take ta raya mata cewar yanzu fa yana can tare da wata, wataƙila ma yana ta mata murmushi. Waya ta ɗaga ta shiga kiransa amma har ta tsinke ba a ɗauka ba, bata daddara ba dai ta shiga kira a karo na biyu amma amsar ɗaya ce no answer.

Tana riƙe da wayar bacci ya yi awon gaba da ita bata tashi ba sai sha biyu, ta yi mamakin irin baccin da ta yi. Haka ta tashi zuciyar ta duk ba daɗi, kayan abincin nan ta kwashe ta mayar kicin don yadda take jin zuciyar ta ba za ta iya
cin wani abu ba.

Dawowa ta yi da nufin ta gyara ɗakin, tun da yau babu abin da ta tsinana, bedroom ta shiga tana shiga ta ji wani irin wari ya haɗe ɗakin. Fuska ta yatsina tana ɗaɗɗaga hanci tana son gano daga inda warin yake amma ta kasa ganewa sai take ma tunanin ko ɓera ne ya mutu.

Ganin gajeran wandon Aminu da ya cire da singlet da alama wasu ya saka, sai da zuciyar ta ta tashi ganin farar singlet ɗin ta yi wani irin datti har ta zama milk ta ƙarfi da yaji. Da tsantsani ta ɗauke su ta ta kai hancin ta wai ko warin su ne ya haɗe ɗakin amma sai ta shaƙi warin dauɗa da na gumi da sauri ta kawar daga wajen hancin ta.

Kayan wanki ta jefa su ta dawo tana duba inda warin yake. Sai da ta duba har bayan drower da ƙasan gado, ta yi ta duba ɓera amma ta sha binciken ta bata ga ɓeran ba.

Dakyar ta iya share É—akin saboda yadda warin yake damun ta ta rasa daga ina ne kuma.

Da ta gama gyaran sai ta cire kaya za ta shiga wanka, tana buÉ—e banÉ—akin wani irin wari ya bugi hancin ta. Sai yanzu ta gane daga inda warin yake sai dai ta yi mamakin jin wari a banÉ—akin domin kuwa bata barin banÉ—akin da datti, dama yanzu ma nufin ta idan ta shiga ta wanke banÉ—akin sai ta yi wanka.

Sai da ta toshe hancin ta ta iya shiga bayin tana tunanin a banɗakin ne dama ɓeran ya mutu.

Duk ta duba babu ɓera babu alamar sa, ganin an rufe toilet (Shadda) Da murfin sai ta buɗe. Abin da ta gani ne ya ɗaure mata kai. Kashi ne Aminu ya yi bai yi floshing ba. Da sauri ta danna wajen floshing ɗin kashin ya tafi da ɗan gudu ta fito daga bayin, bata tsaya a bedroom ɗin ba sai falo ta taho saboda yadda ta ji warin duk ya ɗumame ɗakin.

Idanun ta har ƙwalla suka kawo tana tunanin wannan wace irin rayuwa ce a ce mijin ka bashi da aiki sai ƙazanta, har ta kai a ce mutum ya yi kashi amma ba zai zuba ruwa ba ya tashi ya bar shaddar a haka, to wa kenan yake son ya yi floshing ɗin?.

Ta jima a nan sai da ta tabbatar zuwa lokacin warin ya fita sannan ta je ta wanke bayin ta yi wanka.

Bayan ta shirya ta fito sai ta nufi kicin ta dafa indomie ta dawo ta zauna ta ci, don ta lura in ta ce saka damuwar É—a namiji a ranta ne zai sa ta daina cin abinci to tabbas!. Tana dab da komawa kamar tsinke don rama ko dai ulcer ta kama ta,.

Ana kiran sallah ta ɗaura alwala ta gabatar da sallah, don ita bata wasa da sallah ko kaɗan, lokaci yana yi take yi bata yarda ta saɓa lokacin sallah ba.

Har aka yi la'asar Aminu bai dawo ba, ganin zaman ya gundure ta kuma tana ta saƙa da warwara sai ta ɗauki hijabi ta saka ta nufi part ɗin Amina don ita Sumayya yau ta tafi gidan su wuni.

Da sallama ta shiga Amina tana zaune tana cin jallof na shinkafa wanda ya sha alayyahu.

"Inyee yau amarya ce da kanta" Ta ce tana dariya.

"Ni har wani kai gare ni" Ta faÉ—a tana zaunawa fuskar ta É—auke da murmushi.

Sun shiga yin hira inda take tambayar ta Yusuf da Albani ta ce mata da Baban su zai fita ya tafi da su ya miƙa su gidan su. Suna ɗan tattaunawa Saddiqa sai ta ji Amina ta ce

"Kai gaskiya Saddiqa kina ƙoƙari"

"Ƙoƙarin me?" Ta tambaya cike da rashin fahimta.

,"Zama da Aminu mana"

"Ban gane ba?"

"To miji ƙazami ai sai ka jinjina zama da shi, don dai ni ina son ƘAZAMIN MIJI, saboda babu ruwanki da ciwon kai wato duk namiji mai ado da kwalliya ɗan ƙwalisa ƴan mata kullum suna kai masa farmaki" Bakin Saddiqa buɗe yake wayam tsabar mamaki ta rasa mai za ta ce.

"Ni yanzu da nake tare da wannan mijin nawa mai shegen tsaftar jaraba, koyaushe cikin ado da kwalliya kin ga kowace mace ta gan shi dole ta ƙyasa wallahi shi ya sa wani lokacin sai in ce duk macen da ta auri ƘAZAMIN MIJI ta huta"

'Ikon Allah wato dai ita magana sai ka barta iya kai kaɗai ne take sirri? Daga ka fitar ka faɗawa wani shikenan ba sunan ta sirri ba za ka iya tsintar ta a ko ina ma' Saddiqa ta faɗa a zuciyarta tana mamakin ashe dai Yaya Sule ya kwashe maganar da ta faɗa masa ya faɗawa matarsa, saboda ita dai ta san bata taɓa wannan maganar da ita ba, sannan duk da suna zaune a gida ɗaya ko da za a ce ita Aminar ta ga wasu alamomi a jikin Aminu wanda ya danganci ƙazanta ai ba za ta tunkare ta da maganar ba.

Shi ya sa ake cewa kowa da abokin zancen sa, idan ka faÉ—awa wani sirrinka ko da ka ce kar ya faÉ—awa kowa shi ma in ya tashi faÉ—awa wani sai ya ce masa kar ya faÉ—a, shi É—in ma idan ya ba wani labari sai ya ce kar ya faÉ—a, a haka maganar za ta yaÉ—u baka ankara ba sai ka ji ta je inda baka yi zato ba ko da bata dawo kunnen ka ba to wanda suka sani za suke kallon ka da abun.

"Ai ni tun da ya ce wai kin kawo ƙaran Aminu a kan rashin tsafta na ce masa dama ni ce" Maganar Amina ta katse mata zancen zucin.

Murmushin yaƙe Saddiqa ta yi ta ce

"Haka ne kam kowa ai da ra'ayinsa kuma ai da aka masa maganar ma ya ce zai gyara"

"Amma kuma ya ce mini baram-baram suka rabu bai Aminun bai amsa laifinsa bama?"

'Wato dai sai da ya kwashe komai ya faÉ—a mata?' Saddiqa ta ce a zuciyar ta.

"Bari in je kar ya dawo na ga lokacin dawowar sa ya yi" Saddiqa ta ce cikin sanyin murya ta mata sallama ta baro sashen ranta cike da haushin abin da Yaya Sule ya yi, dama an ce wasu mazan sai sun kwashe komai sun faÉ—awa miji, su ma wasu matan haka suke kwashe zance su faÉ—awa miji ko da kuwa sirrin gidansu ne shi ma mijin haka ne, amma bata zaci Yaya Sule zai faÉ—i sirrinta ba gashi facala ce watarana za ta iya yi mata gori.

Ta fito sai ga Sumayya ta shigo gidan.

"Amarya mai daÉ—in tuwo"

"Ni dai na rasa ranar da sunan nan zai canja zuwa asalin sunana" Ta ce tana Æ´ar dariya.

"Ina!. Ai sunan nan in kin ga an daina faÉ—a miki, sai ranar da Aminu ya rambaÉ—o miki amarya wato ya miki kishiya, sannan ne sunan ki zai tashi daga amarya ya koma uwar gida ita kuma ta zama amaryar" Sumayya ta faÉ—a cikin wasa.

Dammm!. Ƙirjin Saddiqa ya buga jin wannan furucin na kishiya, a take sunan ƴar aljanna da ta kira Aminu kuma ta turo masa saƙo ya faɗo mata, lokaci guda ta ji komai ya tsaya mata kishi kumallon mata.

"Gaskiya haka ne fa" Ta faɗa tana yin murmushin yaƙe.

"Ruma Æ´an mata" Ta ce tana kallon Ruma da take cin biskit. Ta faÉ—i hakan ne don ganin ta kawar da waccan maganar.

"Gata nan!. Bari mu shiga mu fatsar don a ƙafa muka taho" Sumayya ta ce tana yin gaba. Ita ma nata ɓangaren ta nufa tana jin yau tamkar bata fito a sa'a ba don duk maganganun facalolin nata basu mata daɗi ba. Yanzu ta fara tunanin Allah sa dai shi ma Yaya Shafi'u bai faɗa wa Sumayyar ba, duk da ita ma ƙazamar ce.

Ta shiga kenan jim kaɗan sai ya shigo da sallama, da sauri ta fito falon amma abin da ya bata mamaki ganin duk fulawa a jikin sa. Tambayar kanta ta shiga yi kenan dama kasuwa ya tafi? Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da ta yi tunanin ko dai bai je wajen ƴar aljannar ba.

'Ko dai sai da ya je can ya tafi kasuwa?,' Wani sashen na zuciyarta ya faÉ—i hakan.

"Sannu da zuwa" Ta faÉ—a ganin ya zauna a kujera yana ambaton wash!. Alamar gajiya.

"Yawwa" Ya amsa a taƙaice.

"Kawo mini abinci" Ya furta fuskarsa babu walwala don ta lura tun da ya shigo sai wani cin magani yake.

"Ban dafa ba"

"Kamar ya?" Ya ce yana wani yatsina fuska.

"Kamar yadda ka ji mana, da safe da na dafa abincin ka ci?

",Don banci ba sai a ƙi dafa mini wani abincin, wa yake nemo mini?"

Kalaman nasa sun daki zuciyarta kuma ta san ba ita take nemowa ba, amma da yake ita ma dama a cike take da shi sai cewa ta yi
Chapter 11 · 0% Book details