Sashe 23
Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ji ya yi tamkar ya yi kuka, yawu ya tofar a daddafe ya yi wa Ruma wanka suka fito, lokacin Sumayya ta tashi tsaye, priod ɗin ya gani ya ɓata mata zani daga baya sannan har inda ta tashi ma gashi nan ya taɓa bedshet ɗin, kallon bedsheet ɗin ya yi yana jin wani haushi zanin gadon da ya yi oder wajen Maman Afrah ne yadi mai kyau da inganci ba ya tashi bare koɗewa amma saboda tsabar rashin gyara da ba ya samu duk ya fita hayyacinsa.
Ita ko a jikinta ma, kayan wanki ta birkita ta kwaso panties ɗin ta masu yawa, duk babu wani mai wanki sun yi duƙun-duƙun wasu da priod a jiki, zazzagawa ta shiga yi ta ɗauki wani ta mayar da sauran, baya ta juya ta saka pant ɗin tare da ɗaukan wata doguwar rigar bacci marar wanki ta saka ta cire zanin gadon ta haɗa da zanin da ta cire da pant ɗin, ta tuƙunƙuna ta tura su kayan wanki.
Wayarta ta ɗauka a kan madubi ta koma bakin gadon ta zauna. Shafi'u sai da ya shirya Ruma dakyar ya samo wankakkiyar riga ya saka mata, ya ɗakko turare ya fesa mata, tuni ta shiga murna don yaro ma yana son gayu amma ita bata samu saboda ƙazantar uwarta.
Drower Sumayya ya buɗe ya ga yadda ta jera pad(Always) Kowacce yadda ya siyo ko buɗewa bata yi ba, idan wani watan ya yi sai ya ƙasa siyowa amma saboda rashin tsafta shi ne take tarawa kamar wanda za ta siyar.
Kamar zai yi kuka ya ce
"Sumayya ƙazantarki ta ishe ni wallahi, yanzu a matsayinki na mace bakya jin ƙarni ma a ce kina priod amma babu pad a jikinki kin gwammace jini yake ɓata miki jiki, bakya ma kunyar kike shiga cikin mutane babu wanka babu tsafta ce jikin ki matsayin na mai haila? Maimakon daga pad ɗin ta jiƙe ki sauya amma ke sakawa ne na bakya yi" Jin yana ta zuba cikin ƙufula ta ce
"Faɗawa kunne ƙeya ta baka amsa" Tana gama faɗar haka ta juya masa ƙeya.
Kallonta ya yi ya ce
"Haka kika ce ko?" Yatsina fuska ta yi ta ce
"Ni wallahi na kasa gane maka, anya ba haushina kake ji ba saboda ina mace Allah ya ɗaga mini yin sallah idan ina priod, ai ina lura da kai ko a watan azumi idan ina fashin azumi saboda priod sai in ga kana ta ɓata rai, da alama baƙinciki kake saboda ku maza bakwa fashin yin sallah" Wani takaici ne ya cika shi, ganin ana ga yaƙi tana ga ƙura, bata san cewa shi tsabar ƙarnin da take yi in tana priod ne ba ta so ba saboda bata gyara jikinta.
Ruma ya kama zai fita da ita falo, sai ji ya yi Sumayya ta ce
"Bari dai in je in watsa ruwan nan, kar a jima a ga bana nan na ɓace" Juyowa ya yi don ya san da shi take ya ce
"Tun da ga maye ba, mai zai hana a rasa ki" Baki ta taɓe ta ce
"Ni dai ban ce ba" Tana faɗar hakan ta faɗa banɗakin, Ruma ya ce ta je wajen Aunty wato Saddiqa tana fita ya koma ɗakin, ganin vata rufo bayin ba karowa ta yi ya ƙarasa bakin ƙofar bayin ya tsaya yana kallonta da yake ta bashi baya ne yana gani ta ɗauki sabulu wankan ta goga a pant ɗinta, ta wanke pant ɗin ba wani fita ya yi ba ta matse ta rataye ta fara watsa ruwa ko sabulun bata saka a wankan ba bare a yi zancen soso.
Tana gama sheƙa ruwanta ta janyo pant ɗin da ta wanke da lema ta saka, ta ja zaninta ta ɗauro, da sauri ya matsa daga bakin ƙofar, tana fitowa ya ji wani ƙarni ga fatar nan tata sai sheƙi take alamar an tado dauɗa.
Yana ƙare mata kallo a fusace ya ciro belt ɗin jikinsa, idanu ta zaro ganin ya ɗaga fuskarsa a murtuke babu alamar wasa ya ce
"Ko ki koma ki yi wankan kirki, ko wallahi na zazzabga miki" Ganin ransa ɓace sosai ta ga babu wasa ta juya tana gungune, yana tsaye ta yi wankan ya koma ya kwaso panties ɗinta guda goma sha biyar na Ruma goma, ya watsa mata banɗakin, ya ɗauko klin ya jefa mata ya koma gefe ya kama ƙugu, tuni ta shiga wankewa tana sake saɓawa har sai da suka fita ta ɗauraye sannan ta shanya ya bar wajen, da yake tana da abin shanyar panties a banɗakin.
Ɗaya daga cikin wasu sabbin panties da ya shigo da su jiya ya ajiye a drowersa ya ɗakko, always ya buɗe ya ɗakko ɗaya ya buɗe ya manna a jikin pant ɗin, bayan ya goga miski a jiki. Miƙa mata pant ɗin ya yi sannan ya gogo muskin ya shafa mata a mara ya ce ta saka pant ɗin.
Tana sakawa ta shafa mai, ya bata rigar abaya a drower sa saboda ƙazantar ta, yanzu ko ya sayo kaya ba ya son ya bata don duk dafe su za ta yi da dauɗa. Sai da ta saka sannan ya ji wani sanyi a ransa ya kalle ta ya ce
"Ina sonki Sumayya halayenki ne ba na so" Murmushi ta saki, ya ce ta kwaso kayan wankin nasu su je ya taya ta ta wanke, bata yi gardama ba saboda yau ta ga ya sauya kamar dai ba Yaya Shafi,un da ta sani ba.
Washe gari ya yi wanke-wanke ya lallaɓata ta musu abinci ta ce shinkafa da miya za ta yi ya je ya iyo markaɗe ya siyo salad, ya dawo ya ji ɗuriyarta a kicin can ya je hakan ya yi daidai da sheƙa shinkafa da ta yi a cikin tukunyar kan wuta. Da mamaki take kallonsa ganin ya tsaya bakinsa a buɗe yana binta da kallo, ta yi ƙarfin halin faɗin
"Lafiya dai?" Kamar zai yi kuka ya ce
"Haba Sumayya shinkafar na ga kin zuba a haka fa" Cike da mamaki take kallonsa ta ce
"To ba ita za a dafa ba dama?" Wai baki ga abin da kika yi ba" Ta ce
"Ni ban ga komai ba" Ledar hannunsa ya ajiye yana faÉ—in
"Shinkafar fa kika zuba ba tare da kin wanke ba" Kasaƙe ta tsaya tana kallonsa ta ce
"Ikon Allah na kwance ya faÉ—i, amma kai ban da abinka har a nunawa na ringingine farin wata, ina mace za ka nuna mini aikina wannan fa shinkafar gwamnati ce wacce ake kira daga buhu sai tukunya, ko a cikin sunan da ake kiranta ka ji an ce daga buhu sai ruwa sai tukunya?" Jin bai ce komai ba ta É—ora da faÉ—in
"Shinkafar gwamnati ba a wanke ta, shinkafar hausa wacce ake tsince tsakuwa da datti ita ce ta dace da wanki" Tsabar takaici ya rasa bakin magana sai komawa ya yi ya jingina da bango.
*AMINU*
Dariyar da Zulaiha take yi ce ta dakata da yi, jin ya ambato mata sunan kishiyarta a É—akinta tana aika masa harara ta ce
"Me ka ce, Saddiqa ka ambata Aminu" Idanunsa ya buɗe warai sai yanzu ya gane suɓutar baki da kuma katoɓarar da ya yi, ya san dai zafin faɗuwar da ya yi ne da kuma kewar Saddiqa da ya ji tana masa dabaibayi yau ɗaya.
"Ba ce wa ka kira a tsakar É—akina" Kallonta ya yi sai yanzu ma ya ga ashe babu kaya a jikinta a ransa yana fatan Allah sa dai wankan sabulu za ta yi, ganin tana tsare shi da ido a ransa ya ce
'Gaba da gabanta aljani ya taka wuta, wato baba ma da babansa kenan'" A fili kuma sai ya ce
"Cewa zan yi fa Saddiqa ta fara zama tarihi a gidan nan tun da kika bayyana, to ke kuma baki bari na ƙarasa ba" Shiru ta yi tana nazarin maganarsa sannan ta juya ta koma ta rufo bayin, yana nan yana naƙudar tashi saboda yadda kwakwason sa yake ji tamkar kakkaryawa ake yi sai gata ta fito, tana cewa
"Yo ni mantawa na yi amarya tana shiga ruwan É—umi, shi ne ma yanzu nake É—an jin raÉ—aÉ—i sannan kuma ina jin tafiyata tana sauyawa shi ne na juye ruwan flaks É—in na shiga" Kai kawai ya gyaÉ—a mata jin bata ce ta yi wankan sabulu ba.
Haka ta karɓi katin ta koma ta zauna, ko taimaka masa bata yi ya tashi ba, ta loda kati a waya ta shiga kiran ƙawaye da ƴan uwa tana faman cewa su taho gidan amarya mana a zo a dafa a ci a sha. Aminu fa sarewa ji ya yi kamar ya ce kar kowa ya zo masa gida amma dai babu yadda ya iya, haka suka rinƙa zuwa kamar mai suna taruwa wasan mai kuwa da suka ringa soye-soye duk sun yi wa man gara lahani.
*BAYAN SATI GUDA*
Sannu -sannu halayen Zulaiha sun bayyana, ƙazama ce fitik ta ajin ƙarshe wannan ya sanya Aminu yi da na sanin aurenta don ya lura ta dame shi ta shanye a ƙazanta. Yanzu duk abin da ya ga Zulaiha ta ɓata sai ya tuna yadda Saddiqa take gyarawa.
Abin da yake ci masa tuwo a ƙwarya yanzu bai wuce yadda bata iya girki ba kwata-kwata, kuma baban tashin hankali da ƙalubalen da yake gabansa shi ne, zuwan abokansa gidansa jibi, akwai abokinsa Kabiru, Lawan da kuma Bukhari wanda yake aikin soja, ba a garin yake ba don haka ko lokacin da ya auri Saddiqa ba ya nan sai yanzu ya ce tun da ya zo gobe za su zo da sauran abokanan nasa guda biyu Kabiru da Lawan.
Da yake Kabiru da Lawan su a gari suke, kuma sun zo lokacin amarcin Saddiqa ta musu abinci na gani na faɗa, ko ina a gyara ko ina yana ƙamshi.
Abin da yake ci masa tuwo a ƙwarya shi ne, tun saura kwana huɗu ɗaurin aurensa, ya samu Saddiqa ya ce mata idan amarya ta tare sai ta yi sati biyu tana girki, duk da Saddiqa ta ji haushi amma sai ta ce ta amince tun da dama ita har murna take za ta samu salama da kwana da Aminu a gado ɗaya.