← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 44

Sashe 29

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Lawan, to ni ina amarya ya zan yi in muki girkin ƴan ƙasarku baƙaƙen fata, ai ni da kake gani na yi girkin ƙasashe da ban da ban" Su duka ukun sai suka bi ta da kallo ban da Bukari da yake jin kamar ya shaƙo mata wuya, Lawan cikin son jin girkin ƙasar da aka musu ya ce

"Yanzu dahuwar naman nan ba na Nigeri'a ba ne" Murmushi ta yi jin tarkonta ya kama tsuntsu ta ce

"Kaima da wani abu, ai dahuwar naman nan na ƙasar indiya ne, ka san su da suga suke amfani ba gishiri ba, shi ya sa na ce wataƙila baku taɓa ci ba, shi ya sa na gwangwaje ku da shi" Kallon rainin wayo Kabiru ya mata ya ce

"Shi kuma tuwon nan mai miyar ɗaci na wace ƙasa ne" A zuciyarta ta ce.

'Na shiga uku, É—aci?' A fili ta ce

"Miyar ƙasar Marocco ne" Kafin wani ya ƙara jefo mata tambaya ta fita daga ɗakin da sauri, kicin ta nufa tana zuwa ta ɗakko robar kuka ta duba, tana dangwala ta ɗanɗana sai kuwa ta ji ɗaci, a take ta tuno cewa daga gidan an ce mata ƙullin kayan miyar nan na baƙaƙen leda ɗaya kuka ce ɗayan kuma lalle, sai yanzu ta gane ashe lallan ta juye a robar ba kuka ba don haka shi ta kaɗa musu miya da shi.

"Ni Zulaiha yau na kunyata, waɗannan ƴan rainin wayon abokan Aminun sun zo suna wani damuna da mini tambaya ƴar ƙure, dole sai sun ƙure ni, to an yi ma da wane shegen ya kawo su ƙwalama" Ta faɗi hakan a fili tana fitowa daga kicin ɗin ko a jikinta

A can cikin É—aki kuwa, kowa naman hannunsa ya ajiye Kabiru yana tsokanar Aminu da cewa

"Yo kai abokina ka ce girki sai na ƙasar da ka zaɓa za kake ci, ka auri ƴar Nigeri'a amma tamkar ka auri mata ne na mabambanta ƙasashe" Aminu bai yi magana ba, don gani yake ma da gangan Kabiru ya faɗa masa magana. Hannu suka saka suka wanke a ruwan robar nan, cikin ɗan ƙarfin hali Aminu ya ce

"Masallaci za mu je?" Harara Bukari ya aika masa ya ce

"Ni dai tafiya zan yi, sai dai su ku je masallacin tare da su don yunwa nake ji gida zan je" Cikin sauri Aminu ya ce

"Haba kai kuwa ga abinci an shirya saboda da ku" Lawan da Kabiru suka kwashe da dariyar irin ta abokai. Banza Aminu ya musu, nan suka miƙe su duka suna masa godiya hatta lemon babu wanda suka ƙara sha.

Suna fitowa suka farawa Zulaiha sallama, cikin sigar wasa ta ce

"Har an fito kenan" Amsa mata suka yi Lawan ne mai ƙarfin halin cewa

"To amarya mun gode Allah ƙara zaƙin hannu" Wani daɗi ne ya baibaye ra don tunaninta bayan fitarta sun ci abincin, tun da ta faɗa musu ba abincin ƙasar nan ba ne, ta ce

"Ba komai ai baƙon ka annabinka" Har za su tafi Lawan ya zaro dubu biyar ya bata, godiya take ta musu, Aminu kuwa yana gefe bai ce komai ba sai harara yake galla mata, ko kallonsa bata yi ba ta ce

"To godiya nake, sai kun ƙara dawowa, ranar kuwa girkin larabawa zan muku" Ta faɗa cike da wasa, Bukari kuwa fuuuu ya yi gaba don in ya tuna breziyar da ya gani a maƙale a jikin hannunsa zuciyarsa tashi take.

Suna fita ta shiga ɗakin, naman ta fara ɗauka ta ɗanɗana wani rin zaƙi kauuu, da sauri ta fito waje ta tofar da yawu ta wuce kicin ta ɗakko ruwa a wani kwano ta dawo, haɗe da maggi mai tauraro.

Zaunawa ta yi ta wanke naman tas ta barbaɗa maggi take ci, tana cikin ci sai ga Aminu ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi. Yana kallonta ya ji wani ɓacin rai, da sauri ya ɗakko rigar leshin nan yana zazzagawa sai ga breziya ta faɗo, ɗagawa ya yi cikin ɓacin rai ya ce

"Zulai wane irin rashin mutumci ne wannan, saboda tsabar rainin wayo za ki ajiyewa mutane wannan abar daƙalƙal da datti, har abokaina su gani" Tsaye ta tashi ta yi wurgi da hular kanta ta kalle shi ido cikin ido ta ce

"Aminu ni kake cewa Zulai? Idan ka daina kirana ƴar aljannar ne ai sai ka kirani da Zulaiha, sunan da aka yanka rago aka raɗa mini, ba wai Zulai ba sai ka ce wata tayar keke" A ƙufule ya kalleta idanunsa suna hasko lokacin da breziyar take maƙale a hannun Bukari ya ce

"An faÉ—a Zulai" Kallon kai aka bari da yawo da zance ta masa tana komawa ta zauna tare da É—aukan wata cinyar zabuwa, ta shiga yaga dakyar kasancewar rashin dahuwa. Kallon takaici ya mata yana ganin yadda farantan suke cike da tuwon da babu abij da abokan nasa suka ci a ransa yana tunanin da Sadsiqa ce ba za a a samu wannan matsalar ba.

Tsabar takaici ficewa ya yi daga gidan, ya zo zai wuce ta gaban kicin ya ji wani ƙamshi tana tashi, a take yunwar cikinsa ta motsa, ya san Saddiqa ce take girki, amma tunowa da ya yi ko maggi ba ya siya mata sai ya kaɗa kansa, yana dab da fita daga gidan sai ga Sumayya ta fito ta ce

"Ango ka sha ƙamshi na Sumayya bada kanka a sare" Ta faɗa cikin sigar wasan ƙanin miji. Ransa ne ya ƙara ɓaci jin wai saboda Sumayya zai bada kansa a sare, ya ce

"Ina Ruma" Haka kawai ya faɗa kafin ta bashi amsa ya juya ya fice kamar zai tashi sama, baki ta taɓe a fili ta ce

"Ba ni na kai zomon ba rataya aka bani"

Tun da ya fita bai dawo ba sai yamma, yana shigowa ya ganta tana bacci a kan gado, kwanukan nan suna inda suke babu wanda ta ɗauke, tuwon ma duk ya sha iska har ya fara ɗan bushewa. Kai ya dafe ya kafe farantin da ta ci naman duk ta ɗaye tsokar sai ƙasusuwan kwanukan ya shiga kwashewa.

Yana shiga kicin ɗin ya ajiye su, ganin tukunyar Saddiqa a rufe ya buɗe sauran jallof na shinkafa da wake ne a ciki, bai fi ka ba yaro ƙarami ɗan yaye ba, amma haka Aminu ya shiga cin abincin da hannu a tukunyar, yana jin wani daɗi yana ratsa shi a fili ya ce

"Yanzu da abokaina wannan suka samu, ai da babu ni babu jin kunya, amma har zabuwa na saya aka kasa fitar da ni kunya" Ya faÉ—a yana jin daÉ—in girkin har tsakiyar kansa.

Saddiqa wacce ta taho za ta ajiye plate a kicin ɗin, kawai sai ganin mutum ta yi kamar almajiri yana ƙanƙare ƙanzon tukunya, Aminu jin motsi ya juyo da sauri sai kuwa ya yi arba da Saddiqa, ga shi dai ta ganshi amma kuma sai ƙoƙarin wayincewa yake, yi ta yi kamar babu wata halitta a wajen, sai dai idanunta sun sauka a kan tuwon da aka yi wa abokan Aminu da aka ajiye farantan a kicin, tana gani ta gane abincin ne ya kasa ciyuwa, don ta fahimci kenan dalilin rashin iya girkin amarya ne ya sa, ya je mata da batun ta yi wa abokan nasa girki saboda bata san ciwon kanta ba.

Ta ajiye plate ɗin za ta fita, sai kuwa ya matso don ƙamshin turarenta ya gama haɗe kicin ɗin, cikin ƴar murya ya ce

"Saddiqa" Wannan furucin ya yi daidai da zuwan Zulaiha ƙofar kicin ɗin, hakan ya sa Aminu dakatawa yana ciccira ido kamar an kama kwarto a gidan amarya.

Saddiqa kuwa tuni ta fahimci tsoron matarsa yake, baki ta taɓe ta raɓa ta gefen Zulaiha da ta tsaya ƙiƙam tana musu kallon tuhuma, ita Saddiqa warin jikin Zulaiha da ta shaƙa ne da kuma kayan jikin Zulaihar suka saka ta a zuciyarta ta ce

'Cakwakiya lallai zani ce ta tarar da muje mu'

Zulaiha kuwa bayan wucewar Saddiqa ta kalli Aminu, rai a ɓace ta ce

"Wato amanata za ku ci, ranar girkina ka zo kun laɓe kuna ƙusƙus a kicin, saboda ka zubar mini da mutunci ka zo kana cin abincinta, bayan ga tuwon da na muku nan kun bar mini" Tsabar takaici ma ya rasa mai zai ce hannu ya wanke ya fice ya bar ta tsaye a wajen. Fuuuu ta bi shi ɗakin tana zuwa cikin tsiwa ta ce

"Kar ka ƙara mata magana ranar girkina, tun da kai ka cw sati biyu zan yi, don haka babu kai babu ita sai ranar girkinnta" Galala yake kallonta a ƙufule ya ce

"Zulai baki fahimci wa kika aura ba har yau ko? Saboda ban fito na nuna miki asalina na Aminu ba... Kiranta da Zulai ya ƙara dagula lissafin hakan ya sa ta ce

"Wallahi ka daina ɓata mini suna, kuma da kake cewa ban sanka ba kana da wani suna ne da ya wuce Aminu ƘAZAMI... Rai ɓace ya yi wajenta zai kai mata duka ta kama ƙugu ta ce

"Ba irinmu bane matan da ake duka, wallahi yadda kake ji da tsagiranci haka nake tantiriya" Kallonta ya yi ya ɗauke ka, yana ji da kansa yana ganin, kamar dai shi Aminu za ta rainawa wayo, shi da Yayunsa ma bai ƙyale ba tabbas bata so zama lafiya ba a gidansa.

Jin zuciyarsa tana masa zafi ya fice daga gidan.

La'asar lis Saddiqa ta shiga kicin za ta wanke ƴan kwanukan da ta ɓata, tana cikin wanke-wanke Zulaiha ta shigo kicin ɗin, ganin kwanukanta a gefe ta ce

"Malama ya za ki ware mini kaya a gefe, nufinki waye zai wanke" Bango Saddiqa ta ba ajiyar Zulaiha, don ta lura irin matan nan ne masu shegen kishi, ita kuma yanzu gani take Aminu ba ya cikin mazan da za ta yi kishin su. Haushi ya sa Zulaiha ta ƙara cewa

"Ba da ke nake magana ba?" Ganin Saddiqa bata tanka ba, sai Zulaiha ta fara jidar kayan tana kaiwa wurin Saddiqa. Juyowa Saddiqa ta yi cikin muryarta mai sanyi ta ce

"Na miki kama da mai aikin wanke-wanke?" Zulaiha ta ce
Chapter 29 · 0% Book details