← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 44

Sashe 6

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"YAya ina kwana" Muryar Saddiqa ta katse masa tafiyar da yake don har ya bada baya.

"Lafiya ƙalau amarya" Ya ce cike da sakin fuska.

"Yaya dama, uhm, d

"Akwai wani abu ne Saddiqa?" Ya katse mata maganar ganin tana ta inda -inda ta kasa faÉ—ar komai tana wasa da yatsun ta.

"Eh, dama akwai maganar da nake so mu yi" Ta faÉ—a tana É—an jin nauyin sa sannan gaban ta yana faÉ—uwa.

"To ba damuwa mu je" Ya ce yana mata nuni da hannu alamar su shiga daga falon don ya lura kamar bata son yin maganar a wajen. Ta ji daÉ—in maganar sa hakan ya sa ta juya suka shiga falon nata ya zauna sai ya ce

"Ina sauraron ki"

"Yaya dama a kan maganar Aminu ne"

"Mai ya samu Aminun?"

"Dama dai ba ya son tsaftace jikin sa ne, ni kuma abin yana damuna wallahi, na yi ƙoƙarin nusar da shi amma abin ya ci tura!."

Iska ya furzar daga bakin sa yana kallon ta da tausayawa shi ya ga ƙoƙarin ta ma da har ta iya kai wa wannan lokacin bata nemi maslahar faɗawa kowa ba, saboda ya san in ba mai matuƙar haƙuri ba babu mai iya zama da ɗan uwan nasa, sai dai kuma ko ƙazama kamar shi.

"Saddiqa abin da nake so ki gane Aminu ya wallahi mutum ne da yake da taurin kai, dama na san wataran wannan zai iya biyu baya saboda babu macen da za ta iya jure zama da shi ko da tsawon kwana sati uku ne, kin yi haƙuri da jarumta da kika iya kai wa har wata biyu ba tare da kin yi ƙorafi ba" Ya faɗa cikin tausayawa da tausasawa. Idanun ta ne suka tara ƙwalla tana tuno irin warin da bakin sa yake wanda idan ta shaƙa sai ta ji har wani juyawa kanta yake, tabbas!. Babu abin da ya fi ciwo a nata ganin sama da auren ƙazamin miji, duk da kowace mace akwai tata matsalar da take fuskanta a gidan aure amma dai kowane mai ɗako shi ya san inda yake masa yoyo.

"Na masa magana shi ne ya yi biris da maganata na rasa yadda zan yi ne amma don Allah Yaya in za ka masa magana kar ka ce ni na faÉ—a maka"

"Haba Saddiqa magana fa ake ta gyaran aure ai tun da ke ce iyalin sa kuma ke kika fi buƙar ya gyara dole a faɗa masa, sannan idan har kina ganin zai ji babu daɗi in kin faɗa mini to ki cire wannan a ranki domin kuwa Aminu wannan ba wani baƙon abu ba ne a wajen sa sannan ba abin kunya ba ne, abu ne da ya saba ko da za a yi bikin mun zauna an masa faɗa sosai kuma ya nuna ya ɗauki hakan amma dai dama na san da wuya wai gurguwa da auren nesa

"Amma Yaya abin ya yi yawa"

"Ki yi haƙuri zan same shi" Da to ta amsa ya mata sallama ya fito yana ɗan waiga ɓangaren su kar sarkin ƴan kishin nan ta hango shi cibi ya zama ƙari.

Tun da ta faɗawa Yaya Sule maganar sai ta ji wani daɗi da sanyi a ranta ji take tamkar ta sauke wani nauyi. Ɗakin ta koma ta cire bedsheet ɗin kan gadon ganin duk ya dafe da ƙafar sa da ya kwanta jiya, wani wankakke ta ɗauko ta shimfiɗa.

Bayan ta gama komai ta ɗakko freshner mai ƙamshi ya feshe ko ina tuni ɗakunan suka buɗaɗe da ƙamshi sai ta ɗakko qur'ani tana tilawa cikin kwanciyar hankali.

Da yamma ta ƙara shiga ta yi wanka ta sanya kaya marar sa nauyi ta zauna tana jiran dawowar ogan nata, duk tana jin babu daɗi a ranta don ta san daga ya dawo yanzu ɗakin zai sauya daga ƙamshi zuwa wari, don duk ƙamshin nan daga Aminu ya dawo ɗakunan za su yi wani gumus.

"Assalamu alaikum amarya ya ango" Ta tsinkayi muryar Sumayya a falo. Tana daga cikin bedroom ɗin ta amsa mata kafin ta fito zuwa falon tana ɗan sakin dariyar yaƙe.

Ƙarasowa ta yi za ta zauna a kujerar mai daf da Sumyyar amma wani warin gumi da ta shaƙa a jikin ta sai ta ɗan wayinci ta koma ɗayar saboda ba za ta juri shaƙar wannan warin ba, duk da tana ganin mijin ta ma ƙazami ne amma ai shi namiji ne duk da mazan ma akwai masu tsafta amma mace an santa da gayu da tsafta koman ta tsaf-tsaf.

"Saddiqa amaryar Aminu wato wannan kwalliyar yamma ce aka yi wa ango?" Ta tambaya tana kallon ta tare da washe baki kamar gonar auduga. Kallo ɗaya Saddiqa ta yi wa haƙoran Sumayya da ta washe yadda duk suka dafe ta ce

"Eh mana yo ina da wanda zan yi wa kwalliya da ya wuce shi" Ta ce tana Æ´ar dariya.

"Gaskiya babu, ai na farko-farko ne duk amare ai suna wannan gayun a farkon aure amma daga baya sai ki ga komai ya zama tarihi"

"A kan me zai zama tarihi"

"Dainawa sume yi"

"Ni ka in Allah ya aramin tsawon rai har tsufana"

"Muna nan da keSaddiqa duk za ki watsar"

"Ina Hajiya Ruma" Ta tambaya don kawar da maganar

,"Tana can tana bacci'

"Baccin la'asar?"

"Eh"

"Ai kuwa babu kyau" Saddiqa ta ce tana jingina da jikin kujera

Shiru ne ya ɗan biyo baya, sai suka ji sallamar Aminu gaishe da shi da shi Sumayya ta yi ya amsa suna ɗan wasa irin na ƙanin miji. Sallama ta yi wa Saddiqa ta fita.

Bai shigo da komai ba yau don haka yana shiga É—akin ya hau gado ya kwanta, shiga ta yi tana masa sannu da zuwa ya amsa dakyar.

"Bari na kawo maka abinci"

"Na ƙoshi" Ya furta tare da juya mata baya ya kwanta ga jikin sa dirnis da farin filawa.

"Ƙoshi kuma?" Ta tamabaye shi jin wani sabon abu don bai taɓa cewa ya ƙoshi da abinci ba. Danne abin da ta ji ta matsa kuda da shi ta zauna daga gefe ta ce

"Ko baka da lafiya ne?"

"Lafiyata ƙalau kawai dai ba na ra'ayin ci ne" Ya ce yana zaro wayar sa a aljinu ya shiga latsawa. Shiru ta yi tana mamakin kalaman sa ganin yana amsa mata dakyar kamar wanda ya sha magani mai ɗaci, tonowa ta yi da yanzu suka gama gaidawa shi da Sumayya yana faram-faram da washe baki har da wani washe baki yana zolayar ta.

Bai ƙara mata magana ba tana ta satar kallon sa yadda ya mayar da hankalin sa kan waya, sai wani sakin murmushi yake wanda wannan murmushi yana da alaƙa da abin da yake a wayar. Ranta ne yake ƙuna ganin duk lokacin da ta ɓata wajen gyara da kwalliyar da ta masa ko kallo bata ishe shi ba, amma yana zuwa ya washewa ƙazama haƙora sannan yanzu yana yi waya murmushi ita ta zama kamar wani hoto a wajen.

Ganin bai san tana kallon sa ba sai ta É—an yi dogon wuya kaÉ—an tana hango mai yake yi a wayar gabanta ne ya faÉ—i ganin ya yi zoomin na hoton wata mace da take murmushi kanta É—auke da kitson atach ko É—ankwali babu a kanta. Da sauri ta kawar da idanun ta daga fuskar wayar ta mayar fuskar sa har lokacin dai wannan murmushin yana kwance a saman fuskar sa.

'Ikon Allah dama abin da yake a waya kenan, ni ina zaune basho ashe ba ta ni yake ba?' Ta jefawa kanta tambayar a zuciyar ta.

"Aminu" Ta kira shi da kausashshiyar muryar ra da take cike da jin kishin abin da ta gani.

"Ina jin ki" Ya ce ba tare da ya amsa ba kuma ba tare da ya É—ago ya kalle ta ba.

"Me kake kallo a waya kake dariya?"

"Wani abu ne na abin dariya nake karantawa shi ne ya bani dariya" Kallon sa take tana jinjina ƙaryar sa amma sai ta ce

"Gaskiya ne"

Falo ta koma ta bar masa É—akin don ta lura yau kwata-kwata ba ya son zaman ta kusa da shi. Sai da aka kira sallah ta shiga bayi ta É—auro alwala ta fito ta yi sallaha. Amma shi ko gizau bai yi ba, ita kuma bata masa magana ba don yanzu daga ta masa maganar yin sallah sai ya ce mata kabarin su É—aya?.

Har aka kira sallar isha'i amma Aminu bai tashi ya yi sallah ba, ranta in ya yi dubu ya ɓaci. Bayan ta idar da sallar ta fita tw zubo abincin ta zauna tana cikin ci sai fa shi ya fito falon.

"Ni sai na roƙi abincin za ki bani?" Bata ce komai ba ta fita ta kawo masa, yana ci yana danna waya duk ta kasa sukuni ganin yanzu ya fi ba wayar sa muhimmanci a kanta.

Yana gamawa ta kawar da kayan, jin almajiri yana bara ta fita ta karɓi kwanon sa ta juye masa sauran abincin. Bedroom ta koma ta kwanta tana tunanin ko akwai wani laifi da ta masa amma iya tunanin ta bata tuno komai ba.

"Sallamar Yaya Sule da Yaya shafi'u ta jiyo a sashen nasu, wani irin bugawa ƙirjin ta ya yi da ƙarfi, don bata taɓa tunanin zuwan su ba, sai ta fara jin da na sanin sanar da shi ta da so ta yi ya masa magana kamar dai hannun ka mai sanda ashe dai har wani zai gayyato tabbas!. Suna shirin ɗora mata jakar tsaba kaji su bi ta.

ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA?

KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST?

BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUÆŠI BA

WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYATAN FATA MUNA DA AKWAI👇
Chapter 6 · 0% Book details