← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 44

Sashe 14

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu dai ya wuce amma in zaki saka makilin ɗin kike lakutar kaɗan, ni ma duk ranar da na samu damar yin wankin bakin sai in lakuci kaɗan ɗin, ko kuma in lakuta mai ƴar dama kin ga na yi ƙara'i kenan har na sauran ranakun da ban yi ba" Ya faɗa yana ɗan ranƙwafowa ya miƙa hannu ya dafo kafaɗarta. Kai kawai ta iya gyaɗa masa ta tashi ta haye gadon shi ma ya hau, ji ta yi tamkar ta saki kuka saboda yadda ta ji ya gundure ta da tashin warin rana.

Daga haka ya matsa ya shiga neman haƙƙin nasa babu wani nuna soyayya hannu ta kai ta riƙe masa hannu, cikin sanyin murya mai kamar son lallashi ta ce

"Ba don ni ba don Allah ka zuba ruwa a jikinka" Kallon kin raina mini hankali ya jefeta da shi kafin ya ce

"Saddiqa idan haƙƙin nawa ne ba zai samu ba ki faɗa mini mana sai wani jan rai kike mini, kar fa ki manta sadaki na biya amma kina shimfiɗa mini wami sharaɗi din za ki bani halaliyata" Murya ta sassauta cikin raɗa, don ita in ma mai zai ce gwara ta lallaɓa shi ya raba jikinsa da ƙazantar nan kar a je ta cutu.

Sai da aka kai ruwa rana ta nuna ta yi fushi sa yake yana son biyan buƙata, a haka ya tashi ya shiga bayin wanda ya ga shigarsa shi ya ga fitowarsa, sai sheƙin rashin fitar wankan yake don kana gani ka san dai ruwa ya sheƙa bai saka sabulu ba. Idanu ta lumshi tana jin yadda ranta yake ƙuna, shi kuma fitilar ya kashe musu yana wani washe baki ya hau gadon yana cewa

"Na yi belin kaina dai na yi wankan nan da ake ta faman cewa in yi" Wani gumus ɗin warin gajeran wandonsa dabya cire, garin ajiyewa ya jefo saman fuskarta abin da ta shaƙa sai da ta gwammace kiɗa da karatu, da sauri ta ɗauki wandon ta cilla shi gefen gado.

Kamar dai wanda ya taso da dattin haka ce ta kasance, amma dai da dama-dama wai kibiya a ido, haka dai aka shiga ƙoƙarin aiwatar da sunna, ga shi da ƘAZANTAR rashin wankin baki amma sai masifar son yin sumbata tamkar ba,indiye aiki ya yi nisa ita dai babu wata nutsuwa, don aiwatar da sunna ma ya fi idan kowa a tsaftace yake. Hannu ya kai yake saka mata yatsa a jikinta, wani kartar ta da ya yi da zaƙo-zaƙon farcen da ba ya yankewa shi ne ya sa ta zaro ido tare da saurin runtse idon, duk ya bi ya karce ta, a haka ya gabatar da sunnar sai wani uban gashi da bai aske ba da take ji tana goga a jikinsa.

Lokacin da komai ya lafa sai ya ɓingire da bacci, ko jikinsa bai suturta ba sai bargon ta ja ta rufe masa jiki, ita kuma ta je ta yi wankan tsarki ta dawo ta kwanta don ta san idan ta ce ya yi wankan ma ba zai yi ba, baya ta juya masa ta ja rigar baccinta ta kai hancinta tana shaƙar ƙamshin turaren har bacci ya ɗauke ta.

09013181851

TALLA TALLA TALLA

ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE?

KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST?

BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA, KINA DA MIJI MAI BIN MATAN WAJE BA YA KULAKI SAI MA WULAƘANCI YAKE MIKI TUN DA YANA SAMUN BIYAN BUƘATARSA WAJEN MATAN WAJE?

KO MATSALARKI HIPS NE IDAN KIKA SAKA KAYA KIKE YAWO CIKI KAMAR MUCIYA? BREAST NE TAKI DAMUWAR KINA KUNYAR MIJINKI MA YA GANSU? KO BRA KIKA SAKA TUDUNSU BA YA HAYOWA?

AMARYA CE KE KO ME JEGO DUK MUNA DA KAYAN GYARANKU, MASU BUÆŠEWAR HQ AKWAI WANDA ZAKIYI BANKWANA DA BUÆŠEWARSA.

WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYARAN FATA MUNA DA AKWAI👇

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI

MAMAN AFRAH
09013181851
[4/17, 9:33 AM] +234 806 438 0669: https://chat.whatsapp.com/C2hdHP2TbYy0gjsyNpCN6j

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*

BOOK 1
PAGE 9

Daƙyar ta tashi da asuba don gabaɗaya jikinta ciwo yake mata, tana zaro ƙafafunta ta sauke a kan gajeran wandonsa da ta cillar tsakanin gado jiya, wani irin yamm jikinta ya ɗauka duk ƙyanƙyami ya kamata tunowa da ta yi da yadda ta shaƙi warin jikin wandon jiya da ya sauka a fuskarta. Sunkuyawa ta yi za ta ɗauke wandon amma sai ta kasa taɓawa don hatta zuciyarta sai ta ji tana tashi, ga wani yawu da ta ji ya taru a bakinta.

Fitilar ta kunna haske ya gauraye É—akin, a kan Aminu ta sauke idanunta da yake bacci duk ya cika É—akin da munshari, wani kallon tausayin kanta ta masa ganin wannan shi ne matsayin mijinta, a ce mutum ya samu janaba amma bai iya tsarkake kansa ba ya kwanta a haka, ko ba zai yi wanka ba ai ya je ya yi tsarki ya wanke najasar jikinsa.

Bayi ta shiga ta ɗauro alwala ta fito ɗan guntun ruwan hannunta ta fatsa masa a fuska, ammma ko gezau bai yi ba sai sharara munshari yake kamar an danne wuyan rago. Ƙafarsa ta fara bugawa daƙyar ya buɗe idanunsa da suka masa nauyi saboda baccin ya sauke a kanta, yana hangota duru-duru don baccin bai wartsake a idanunsa ba.

Kallon takaici ta masa ta ce

"Ka tashi lokacin sallah ya yi, yanzu duk na yi ƙaran buɗe ƙofar gida da alama ƴan uwanka ne suka tafi masallaci" Wani irin yatsina fuska ya yi yana jin kamar ya mangare ta don ya ji haushi matuƙa da ta katse masa baccinsa mai daɗi, cikin haɗe girar sama da ƙasa ya ce

"Sai aka yi yaya? Ko ni an ce idan na falka ba zan yi sallar ba, wai sau nawa zan ce miki kabarinki da ban nawa daban Saddiqa amma sai kike shige mini hanci da ƙudundune kar fa ki manta mijinki nake ba ɗanki ba, ni ya dace na baki umarni" Ya kai ƙarshen maganar kamar zai fasa mata kunne da ƙaran maganarsa ganin yadda ya hayayyaƙo mata.

Cikin jin takaicinsa ta danne abin da ta ji ta ce

"Haba don Allah yanzu mene ne na tada jijiyoyin wuya da asubar fari, ka san dai gidan nan ba iya mu kaɗai bane, amma a ce da asuba ana jiyo hayaniya ai sai cibi ya zama ƙari, sannan ni ba umarnina bane yin sallar umarnin Allah ne ai" Kallonta yake mamaki yana bayyana a fuskarsa da alama mamakin kalamanta yake a zuciyarsa ya ce

'Kannan yarinyar tana shiga shirgin da babu ruwanta, ai wani lokacin ma auren mace uztaziya ko mai riƙe addini da alama matsala ne in ba haka ba yarinya kamar ƴar gidan malam Kabiru Gombe duk ta bi ta addabi mutane da magana ɗaya' A fili kuma sai ya ce

"To tun da umarnin Allah ne ba naki ba, ki sakar mini mara na yi fitsari" Yana kaiwa nan a maganarsa ya ja bargon ya rufa har kansa. Galala take kallonsa rufe cikin bargon tana tuna ko jikinsa fa bar suturta ba tsirara yake, ita ce ma ta sakaya jikinsa da bargon.

'Wane irin miji na aura ne na kasa ganewa, haka zan rayu ni da ƴaƴana ƙarƙashin wanda bai damu da addini ba a ce sallah sai mace tana fama da miji zai yi in ba haka ba sai lokacin da ya shirya a shelaƙe zai yi, shin mene ne fa'ida ko ribar auren namiji irin wannan ga muni ga cin zanzana wato ga ƙazanta ga jahilci' Ta faɗa a zuciyarta tana ta tunanin ina ma akwai yadda za ta yi ta sauya masa halayensa, da ta yi saboda tana ƙaunarsa kuma shi ma dai ta san haka ne ta ɓangarensa amma bata taɓa zaton za ta same shi da wannan halayen wanda ba na ƙwarai ba.

Juyawa ta yi ta koma ta saka kaya a jikinta ta saka hijabi ta shimfiÉ—a sallaya, raka'atainil fajr ta gabatar, bayan ta yi addu'o'in ta a cikin sujada ciki kuwa har da addu,ar Allah ya dawo da mijinta kan hanya madaidaiciya wato yake kiyaye salloli da kuma zama mai tsafta don su samu rayuwar mai É—orewa haÉ—e da farinciki don watarana Æ´aÆ´ansu su yi alfahri da su matsayin iyayensu, domin ta fahimci in har zai É—ore a haka to tabbas babu wani yaro da zai taso ya ji daÉ—in ganin mahaifinsa yana wasa da sallah.
Chapter 14 · 0% Book details