← Book details Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 44

Sashe 17

Ƙazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban yi ba Saddiqa tun da ke kika koya mini karatun sallar da nake yi, tun da abin ya zo da cin fuska ba zan yi sallar ba idan ke ake yi wa in na yi ki watso mini" Wannan maganar da ya faɗa a zafafe ya yi daidai da tahowar Khady don haka a kan kunnuwanta ya faɗa gabanta sai da ya buga jin hargowar da yake yi, a bakin ƙofar ta tsaya da yake labule ya shiga tsakaninsu.

Shi kuwa yana kaiwa nan ya tashi fuuuu ya shige ɗaki, jin sallar Khady sai ta yi saurin kawar da kai gefe ta amsa mata tana danne kukan da yake son ƙwace mata.

Ɗaki ta shiga da sauri a kan gadon ta gan shi ko kallo bai ishe ta ba, bayi ta shiga ta ɗauro alwala a can ta yi ɗan kukan takaici kasancewar ta mai zurfin ciki bata son Khady ta fahimci abin da yake faruwa, bata san cewa Khadyn ta ji abin da ya ce na ƙarshe kuma ko ba komai ai ta gama fahimtar Saddiqar tana cikin damuwa.

Bayan sun idar da sallar Khady ta dafa kafaɗar Saddiqa cikin ƙasa da murya ta ce

"Ƙawata na san kina da zurfin ciki, kuma duk da baki faɗa mini ba na san kina da damuwa, amma matsayinki da kuma kusancina da ke ba zai sa in kasa faɗa miki wani abu ba ina so ki yi watsi da zurfin cikin da kike da shi ma'ana ya zama kina faɗawa wani damuwarki saboda kar kike barin damuwa a zuciyarki hakan zai haifar miki da matsala" Wasu hawaye ne masu zafi suka ƙwace mata, ita kanta Khady idanunta cike suke da ƙwalla domin tana jin Saddiqa tamkar ƴar uwarta ta jini ganin Saddiqar bata ce komai ba sai ta ɗora da faɗin

"Ban ce kike fitar da sirrinki ba, amma a ƙalla kike fitar da damuwarki ba a son ake tarawa zuciya damuwa saboda gudun matsala, sannan addu'a ita ce takobin mumini ki dage da ita sosai duk da na san baki da sakincin yinta abu na ƙarshe, kar kike bari namiji ya rainaki ko ya raina wani naki ke dai ki zama mai biyayya amma kar ki yarda ake miki cin kashi, domin shi itace tun yana ɗanye ake tanƙwasa shi abin da nake nufi idan har kina bari kpwace shara namiji ya watsa miki to za a wayi gari har girman ƴaƴanki a gabansu zai ci zarafinki, kuma ko da ya auri wata nan gaba ita in ta nuna ba za ta ɗauka ba sai ya zamana ke kalai ce jujin zuba shararsa, duk da bani da aure amma na san abubuwa da dama a kan aure" Saddiqa sai ta ji tamkar Khady ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi a take hawaye suke sintiri a kumatunta kuma daga hakan ta gane cewa kuka wani ma ya lallashe ka rahma ne, sai da hawayen ya tsagaita ta ce

"Na gode ƙawata kuma duk abin da kika faɗa haka ne, zan kiyaye kuma zan yi duk iya ƙoƙarina" Ta faɗa ita ma cikin raɗar don ta san Aminu zai iya kasa kunne, kuma ta ƙara gane cewa yanzu da yake tare da wata budurwar kenan in tana danne komai in ya auro wata ita ta zaɓa bola.

Ta jima tana lallashinta har dai ta ga ta saki ranta daga nan ta mata sallama ta raka ta ta tafi.

Khady tana tafiya ta tsaya a falo ta share hawayenta tas, tana shiga É—akin ta gan shi yana sallah idanu ta sauke a kan gajeran wandon nan nashi na jikin drower bakin gado ta zauna har ya sallame sallar. Dama yana gama sallama yake barin kan sallaya saboda ba azkar yake yi ba. Kallonsa ta yi yana danna waya ta ce

"Aminu shin mai ya kai wandonka falo saman kujera?" Tambayar ta zo masa a bazata duk da ta yi kama da tambayar rainin hankali amma sai ya maje ya ce

"Kamar ya?" A ƙufule ta ce
"Ya ina tambayarka kana tambayata?"

"Ra'ayi riga" Ya faɗa hankali kwance. Ƙwafa ta yi cike da ɓacin rai ta tashi za ta bar ɗakin ƙiiii ta ji ya janyota ta dawo waiwayowa ta yi ta ga ya haɗw fuska babu zato ba tsammani ya ce

"Daga yau da rana mai kamar ta yau kar ki ƙara gogin yi mini ƙwafa ni ba sa'anki bane" Yana kai wa nan ya saki hijabin nata da ya kama, bata ce masa komai ba ta juya ta bar ɗakin.

Sai da ya ga la'asar lis ya ƙwama uwar hula ya zo wuce ta tana zaune a falo ya ce

"Sai na dawo" Da banza ta yi da shi sai kuma ta ce

"A dawo lafiya" Ta faÉ—a ba tare da ta kalle shi ba tun da ta ga har zai iya fita haka yana warin rana shi abin ma ba ya damunsa ita kuwa har mamakinsa take yi.

Bai dawo ba sai bayan isha'i, lokacin ta shirya tsad cikin fararen kayan bacci, tana kwance tana game a waya, ganin yana washe baki yana wani nan -nan da ita ta san wani abu zai buƙata ita kiwa ta ƙudurce a ranta cewa, duk runtsi yau ba za su haɗa jiki ba har sai ya tsafta ce jikinsa ko dai ya haƙura.

Kamar abin kirki ya zauna yana ta zuba kamar kanya, zuwa can ya ce

"Amarsu ta ango daga ke babu ƙari" Kallon maƙaryacin banza ta masa kafin ta buɗe baki ta ce

"Namiji ai ba mijin mace ɗaya bane" Dammm ƙirjinsa ya buga, a take ƙwaƙwakwarsa ta shiga tariyo masa furucin da ya yi wa ƴar aljanna lokacin suna waya a kicin, tunani ya fara ko dai ta ji wayar da ya yi ranar sai kuma ya kawar da maganar ta hanyar cewa

"Wani namijin ba" Wani murmushin rainin hankali ta yi ta ce

"Uhm in ji mai ciwon haƙuri" Daga haka ta mayar da hankali kan game ɗin pop game da take yi.

Shi kuma jin yana tsuma yana son kawar da abin da yake ji, sai ya ɗan matsa tare da miƙa hannu ya shafo kafaɗarta da yake wuyan rigar sleeping dress ɗin irin wanda yake da kafaɗa a buɗe ne. Laushi da santsin fatarta ya sa ya saki wani murmushin jin daɗi, ita kuma a nata ɓangaren ba haka bane domin kuwa garin shafo kafaɗarta ya karce ta da farce. Bata nuna masa komai ba tana jiran har ya ida nufinsa ta gabatar da tata buƙatar wacce take ganinta a matsayin sharaɗin da za ta gindaya masa na kwanciya da ita.

Ɗan matsawa ya yi yana sosa ƙeya ya ce

"To wai ni a ajiye wayar mana tun da ango ya zo kusa, ni fa saboda ɗokin kasancewa da ke yau ko abincin dare ba zan ci ba" Wani murmushi ta saki wanda ya bayyana kyawawan jerarrun haƙoranta wanda suke a jere kamar masara, suna sheƙi kamar bayan kwanon silba. Ganin kyan da ta yi ya ƙara fusgarsa zuwa gare ta ya matsa kusa, ganin tarkonta ya kama tsuntsu sai ta yi yunƙurin sauka daga gadon, cikin rashin fahimta ya ce

"Ina kuma zaki bayan buƙace nake" Idanu ta farfara tare da langaɓar da kai ta ce

"Ai ba wani waje zan je ba abu ne zan ɗakko maka" A ransa sai ya fara tunanin ko dai Saddiqa ta fara wayewa ne maganin ƙarfin maza za ta bashi, wannan tunanin ya sanya shi ya ƙara jin kansa ya masa gingirin gim.

A hankali ta tafi kan madubi cikin takunta na mace mai aji da nutsuwa, da kallo ya bita yana É—an lashe baki kamar tsohon maye.

Baƙar ledar da ta miƙo ya karɓa, tana tsaye ya buɗe ledar ya leƙa abih da ya gani ciki ne ya sanya fuskarsa sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci ya ɗako kai yana kallonta mamaki shimfiɗe a fuskarsa ya ce

"Mene ne wannan?" ÆŠan murmushi ta yi ta ce

"Sheba da ake shebin da reza da ake yankan farce, Aminu idan ka ga yau ka kusanci ne to sai in har ka aske gashin hammatarka da na mararka sannan ka zauna ka yanke farcenka, abu na ƙarshe sai ka yi wanka soso da sabulu sannan sai mu yi abin da za mu yi babu cuta babu cutar...

"Wannan labarin ƙanzon kurege ne, ki ƙaddara tatsuniya kike mini" Ya faɗa rai a mugun ɓace don zuciyarsa har ta raya masa cewa, Saddiqa bata son bashi haƙƙinsa ne shi ya sa ta ɓullo ta wannan hanyar. Daga nan inda yake ya yi jifa da ledar kan madubin. Kallon abin da ya yi ta yi tana jin takaici ta ce

"Tun da haka ka ce za ka ga labarin ƙanzon kurege" Tsaye ya miƙe tamkar zai kai mata duka ya ce

"Indai har kina ganin kin kai ki saka doka ko sharaɗi in bi, to ki sani baki isa ba kin yi kaɗan kin yi tsarara kamar ruwan shayi, in dai har wannan abun naki kike taƙamar sai na yi aski da yankan farce haɗe da wanka to ki jiƙa ki sha ba a so, sannan ina so idan kin manta in miki tuni ni mijin mace huɗu ne idan kin hana zan iya kawo wacce za ta bani sannan ta tarairaye ni ba tare da ta yi la'akari da ƙazantatar da kike ikirari ba" Yana kaiwa nan ya juya zai yi wajen drower raina sai ƙuna yake ta shiga bayi ta ɗakko ruwa a hannunta tana zuwa ta kama hannunsa bai yi musu ba duk da ransa a ɓace yana son ganin gudun ruwanta.

A hannunsa ta zuba ruwan tare da nannaɗe hannun rigar ta shiga murzawa, aikuwa datti yake fitowa kamar wanda bai taɓa wanka ba, dirzawa take datti yana fitowa da sauri ya janye hannunsa cikin hargowa ya ce

"Wannan rainin naki ya yi yawa har ni kike yi wa titsiye kina son fito mini da dattin da ya ɓuya a jikina, ke baki san akwai dattin da yake zama kariya a jikin fata ba" Kallon raini ta jefe shi da shi ta ce
Chapter 17 · 0% Book details