← Book details Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 25

Sashe 9

Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

uwar goyon wa? Cikin natsuwa ta ce min shi Mubarak mana, na sake kallonta sai ta shiga yi min bayanin saboda ta gane abn san komai ba kan maganar da take nufin yi min din. Ita Hajiya Ummulkairi ai ba ita ce mahaifiyarshi ba, na azro ido ina kallon baba Sumaye cikin tsananin mamaki, ban taba kawo irin wannan tunanin ba cikin raina, saboda ban taba tunanin akwai wata kyakkyawar mu'amala tsakanin matar uba da dan miji ba balle har aje ana samun dama ko shagwaba irin wacce na saba gain Mubarak yana yiwa Ummanshi ita kuma ta bar komai da takeyi tayi ta tarairayarshi. Mahaifiyar Mubarak ai Hindatu ce budurwa ya aureta tazo ta haifeshi shi kadai zaman yaki dadita tsallakeshi ta yi tafiyasta tunda ta tafi kuwa ban sake jin ko da labarin ance ta zo ganinshi ba, ina ganin kuma sanda ta barehi baifi.shekara guda ba a duniya don sansdin mutuwar, aren ne. ya zama sanadin yayeshi saboda shi uhen ya ce ba zaa tafi mishi da shi ba, sai ya baiwa ita Ummulkairin shi da yake mata ce mai hikima sai ta sa hannu biyu ta rike irin rikon da ko ya'yanta bata yiwa haka ba, bata bari mummunan zaman da sukayi da uwarshi ya shafeshi ba. Na sake kallon baba Sumaye saboda tsananta mamakina yayin da ita ukma ta ci gaba da bani labarin da ban sani ba. Shi Alhaji Muhammadu ai ya auri mata da yawa a sanina nama akan idona ina ganin sun kai biyar, iyaka dai mafi yawancinsu basu haihu da shi ba daga ita Ummulkhairin ce sai A'indatu su ne masu 'ya'yan, ita Ummulkhairi ya'ya mata uku su ne su Kaltume ita kuwa dama ba budurwa ya aureta ba bazawara ce ta ma haifi 'ya'ya biyu a can wani gidan, a cikin jikokin ta na can gidan nema yanzu aka baiwa Mubarak din guda daya, ai Rumasa'u ce yarinyar da zai auran. Ban san yanda akayi ba sai kawai na tsinci kaina da tsanar Mubarak da Ummanshi da babanshi da ma i ta Rumasa' un tunda na santa na saba ganin tana zuwa gidan sai dai ban taba sanin alakar dake tsakaninsu ba da ya wuce na 'yar babbar yarsu ce na fassarasu a matsayin wadansu irin mutane mayaudara marasa adalci wadanda basu san kowa ko komai ba in banda kansu. Shi da ai darajanta shi ake yi a adanashi a yi tattalin darajar shi da mutuncinshi baka barin shi ya wulakanta a gaban jama'a balel ya je yana lalacewa masoya da makiya suna kallo wasu na bakin cik wasu na madalla, shi Alhaji Muhammadu ya yi nufin adana danshi ne don ba zai yiwu ya zuba mishi ido yana nema ya shiga wani al'amari ba, ita kuwa Ummullkoiri sai tayi amfani da damar da tas am wajen oshi jikarta ya aura, kunga ai ya kara zama nata a. hakan kuma sai ta kara samunshi a hannunta kamar yanda hikimarta tasa ta samu mijinta, to shima malam Habu da. samun wani yayi ya daura miki aure da shi ya kaki dakin mijinki da ya fi ye mishi barinki da ya yi ana yi miki wannan wulakancin da tozartarwar, to bai yi ba bai kuma da mafadi abokiyar shawararshi daya ce matarshi ita kuma bata taba shawarta mishi wani abin ariziki ba sai na sharni za kuma ta ga yanda abin zai juya mata. Sallama nayi da baba Suimaye na fita na koma cikin gidanmu na fasa zuwa gidan yaya Dija. Ina shiga gidan naga baba Lantana tare da Asabe a zuciyata na tabbatar labarin auren Mubarak da ta ji ne ya dawo da ita. Baba Lantana sai farin ciki take yi tana kyalkyalewa da dariya irin wacce ta dade bata yi ba, ita mace kowacce ai tana da kufu'in aurenta in kana da hankali kaima ba sai an gaya maka ba ni dama can nasan wannan yaron mubarak ba zai aureta ba yaro dan gata irin wannan ya rasa matar da zai aura sai ita, ai kema kin san ba zai yiwu ba, a yanda yake da irin arzikin ubanshi da rin gatan da yake da shi habawa? Timatiri ne fa sana'ar ubanta kowa ya sani to ko basu lalace tare ba yaushe zai aureta? Ita ba kyau ba ita ba gata ba, ita ba dangi ba, ita ba asali ba haka kawai? Ai idonsu ya rufe ne kawai.a kan sun duniya ba don haka ba da tuntuni suka gane gaskiya da akayi abin nan da sai malam ya bi bayan Alhaji Muhammadu Nalami ya bashi hakuri a daura' aure to baiyi ba saboda shi agwagwane bin ya'yan shi yakeyi yanda suke so haka ake yi don haka nunawa ido ne. dama kuma ina addu'a na kuma san alhakina ne ya fara kamasu, nayi nufin yi musu abin arziki in rufa mata asiri duk da cikin da na san tana da shi na hadata da wanda nasan zai aurcta duk da cikinta don asiri ya ruf da 'yar uwarta da taimakon ubansu suka watsa min kasa a ido, to ai mu na nan da su. Ta yi kwafa ta mike ta nufi dakinta. Asabe dai ba ta ce mata ba to balle kuma ni can cikin zuciyata dai mamaki ne ya kamani na yanda ita da bakinta ta zauna tana bayanin gata irin na Mubarak a yau alhalin kullum abinda ta saba fadi shi ne karyar banza karyar wofi mu za a kawowa barazana, daga karyar ziki kawai haka masu kudin suke. A wannan lokacin sai baba Lantana ta zama bata da wata hira sai na Mubarak da iyayenshi tayi ta bada labarin arziki da irin alherin Alhaji Muhammadu a wurinta a kuma bakinta naji wai ashe sabon gini aka yiwa Mubarak din a can cikin gidansu banda haka kuma aka saya mishi sabuwar mota, don ya yi angwanci a ciki, ai kwarya tabi kwarya in tabi akushi sai ta fashe, karin maganar da baba Lantana ke wuni tan ayi kenan a yanzu. Asabe dai bata shiga harkata ba nima ban shiga tata ba ta dai dawo gidanmu gaba daya har da kayanta da na watsar sai dai kuma a yanzu ba abinda yake gabana kenan ba ina ji da kaina, ina cikin wani irin tashin hankali da rudanin da ban san yanda zanyi in fita daga cikinshi ba. Gaskiya ne duk wani abinda baba Lantana ta fada akan Mubarak da irin gatan da iyayenshi suka shirya mishi tunda aka fara bikin ummanshi ke bin gidajen makwabta da abinci dana sha ko kaje gidan bikin ko kar kaje za a kawo maka nau'o'in abincin da aka girka kala kala, ina ganin tamkar a unguwar nan gaba daya gidanmu ne kawai bata yiwa irin wannan aiken ba. A ranar da aka kammala bikin kuwa ina kwance a kan gadona ina jin dirin motocin abokan Mubarak da suka rakoshi wurin babanshr ya a mishi albarka kafin su rakashi dakina maryarshi don ance wai tunda aka yi abin yau ne ranar farko da baban nashi ya yarda zai ganshi. A wannan daren bana iya kwatanta komai game da halin da zuciyata ke ciki, iyaka dai kawai na san kasancewar Asabe a dakin nan ba ya hanani yin kuka ba tare ikuma da na damu da ta ni ko bata ji yi kawai nake yi don in samu in samu saukin ciwon da kirjina ke yi. Ban san abinda take ciki ba sai jinta nayi ta ce, uhun dama kin hakura kim yi shiru tunda taki mas'alar ma ai mnai sauki ce. Ban kulata ba itama bata sake ce min komai ba. A wannan lokacin sai na zama babu abinda nake sha'awa irin in ga mutane masu yan uwa da dangi a wasu garuruwan na nesa sai in rinka jn tamkar inama dai nice da tuni na tattara kayana na koma can inda suke dan in samu in samu seukin 6acin ran da nake ciki, wani lokacin kuma nice inama dai dai babana yayi min irin abidna baba Sumaye ayi sha'awar ace ya yi min na aurar da ni ga duk wanda ya ga damada yanzu nima ina can gidan mijina ko ina son shi ko bana sonshi kuma ai zan zauna darajar shi baban nawa ne ya bani shi sannan ko bana son nashi kuma ina ganin ba zan gamu da bacin ran da ya kai wanda nake fama da shi ba a yanzu. Ana gama bikin Mubarak kuma sai na sake zama abin nunawa wurin 'yan mata da samarin da dama na rike musu wuya sai da ya gama da ita sannan yaje ya auro gal a leda, abinda suke ta fadi kenan ko naji suna fada suna dariya bana kulasu ko kuma su yista rera wakokin da makada da mawaka sukayi ta rerawa Muberak din da iyayenshia wurin bikin, sai da ta kai ma na sake daina fita waje saboda tsananin dana shiga cikin zuciyata na rika tambayar kaina sai mace? Kullun in za a yi maganar ta nashi bangaren da ya gama da ni din akan furta a yansyin da bai yi kama da aikata wani iaifi ba sai dai ma kaga tamkar ya yi wani alin gwaninta ne ko bajinta, a nawa bangaren ne za a yi ta a yanayi na wulakanta ko tozarta ko kurna muna ailkata wani abin kunya da wuiakantar, kai da na lura da kyau da yanayin da ake bayar da labarurrukan sai na gane shi Mubarak ma sha'awa yake baiwa mutane ga kuna gatan da iyayenshi suka yi nishi wanda mutanen unguw8r basu gsiiya da bayar da iabarin, bisa wanan lurar da nayi da abinda ya sameni sai nima da kaina na yardanwar kang da cewar ita mace ita ce mai yin abin kunya in har abin kunyar ta zo, ita ce kuma mai tozarta in abin tozartar ya zo, ita ce mai shiga ta wulakanta saboda ita ce mai rauni komai ya faru a kanta yake karewa, ita ce a kasa, ita ce take bukatar mutunci da kunya don su zamo sutora a gareta, shi namiji karfi kawai yake nema. Dana kara tsunduma cikin tunani sai na tuna da wasu kalmomi da na taba gani a cikin wani littafi a hannun Mubarak, ga abin da suka ce: MAN IS BORN FACE AND EVERY WHERE
Chapter 9 · 0% Book details