Sashe 5
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
iya cewa na saba jinta haka nan a duk halinda nake ciki bana rasa wani dan canji kulle a bakin zanina wanda nake dan tsakura ina baiwa babana abin karyawa in ayso ni in hakura don bana yarda ya fita su kuwa nasan da kyar ne in suna da wani abu. A wannan lokacin a gidanmu rashin yin girki bai zamo komai ba tunda baba Lantana tana kin yin girki da gangan yanzu mai dalili ya sameta, kasuwar babana ta yi kasa jarinshi ya yi matukar karyewa tun yana kawo mata dan cinikin da yake yi tana rainawa tayi watsi da su ko tayi ta zage-zage tana tambayarshi wadanann me za su yi mata har ta hakura ta zuba ido don ta gane abin bana kare bane tunda kullum raguwa yake yi sai da ta kai ma tana tambayama ace mata ta yi hakuri tayi ta maganganu to yanzu babu kawai yake cewa ya ja bakinshi ya yi shiru ya barta ta fadi duk abinda take son fada. A wannan lokacin sai ta zama bata da aiki sai na fushi ko mita ko ka ji ta tana baiwa Asabe labari irin zaurawan da suka nemeta wai ta kisu ta auri babana sai ta yi kwafa ta ja tsaki tace, to rabon wahala ni kuwa sai in kyalkyale da dariya tayi ta zagina, Asabe tana kallonta bata tsoma baki nima bana cewa komai baya ga dariyar can cikin zcuiyata ina kiranta da sunan da na saba jin Alhaji Nalami yana kiranta wato Butulu. Muna cikin wannan zaman ne muka ji an kwada wata irin sallama a kusa da kofar shigowa gida gabana yayi mmmunan faduwa arnma kuma nasan na baba Lantana yaf nawa faduwa saboda yanayin da na gani a tare da ita tun kafin ta kai ga amsa salalmar tashi sai gashi ya fado tsakar gidan. In ce ko da ba za a amsa sallamar tawa ba ne? Ta soma kame-kame tana rantse-rantsen wai bata ji salalmar tashi ba nan da nan ta shiga yi mishi oyoyo tana sannu da zuwa cikin sauri ta shiga ta dauko mishi shimfida tana yi tana, habawa yaya za a yi inji sallamarka in ki amsawa to a wanne dalili? Ta gyara zama, yana fadin a dalilin cuta mana aike tsunma ce. Na mike na soma tsince kayana da suka soma bushewa na wuce na nufi dakina cikin zuciyata ina kokarin danne dariyar rawanin da naga yayi wanda yafi kama da na waziri aku. Rawani kuma Alhaji ya koma yi? Tayi tambayar cikin yanayin sakin f ska da fara'a, ko an baka wata yar sarauta ne ban ani ba Alhaji Muhammadu? Ta sake janshi da wat rahar. Ya kara tsuke fuska saboda watakila fara'ar tata ta yi mishi yawa, kinga bana son irin sunayen da kike kakabg min ni, naje Makka*ne da kike ce min sunana Muhamm du? Nalami kawai sunana kenans hi na fi so shi nafi sani. Ta yi murmushi Alhaji ai sunan mai niyya ne bana wanda ya je bane, Muhammadu kuwa ai sunan maza ne menene aibi don an kiraka da shi tunda Nalami ai ba sunan gaskiya ba ne. To ni shi nafi so da shi aka yanka min ragon suna ko sai ace bai yanku ba? Ta ce ya yanku, ya ce to ni ba ma wannan ne ya kawoni ba. To ka cire rawanin naka mana ka sha iska. Ya yi maza ya ce na ki din in cire yaran unguwarku da basu da tarbiya su hangoni su zo su kara sani ko? Ko da yake an gaya min cewar ke kika biyasu kika ce musu su kasheni in nazo wurin daurin auren to ta Allah ba taki ba gani nan daramin gabanki da raina da lafiyata. Da sauri ta tambayeshi ni? Insa a kasheka ake wane dalili? A dalilin dukiyata da kika karba man tunda ai an gaya min komai ba kudina ni kadan kika ci ba, tayi murmushi, wanda ya gaya makan bai gaya ma kag gaskiya ba, niikam ai ina nan a kan bakana tunda dai kaima ka.ganta da idoka tana nan ba... .Ba ta karasa ba ya ji maza ya ce ma ce a'a bana so ina? Ai wautar tawa ba ta kai haka ba ai ni kuma kin, sanni ba a cutata: sau biyu ko da yake dai ke zatiddawahice ko gamsheka bata kaiki sharri ba wato in sake dawowa da sunan karbar aure don ki samu su karasani ko tunda burinki bai gama cika ba a kaina to naki bana son auren shiga kawai ki fito mirn da abinda kika sani nawa sauri nake yi. Ban san yar da akayi ba naji baba Lantana ta rage murya, tayi wata magana sai dai kuma shi bai rage muryar ba wajen bata amsa don haka na gane abinda ta ce mishi. Asabe kuma? In zo in auri Asabe to a kan me? Ai dai kasan ba finta komai tayi ba tunda ita Asabe ma ga kirji a cike ga mazaunai ga diri ita wannan ai haka singul take tsawo ne kawai kamar sanda. Ya yi tsaki ya ce ai duk a banza gara ma singul din ita Asabe in ita nake so ai 1asan inda zan sanieta bani kudina akwai. Ranta ya 6aci da jin maganar tashi cikin yanayin fusata sai ta ce mishi karfa ka ce zaka yi min wulakanci ina binka cikin sauki kana sake baki kana caba min ma gana da wasu labbanka masu kama da saukan markade nawa ne kudin naka? Ya gyada kai una alamar gamsuwa da jin maganar ta ta cikin natsuwa ya ce basu da yawa kawo min su in tafi in bar miki gidanli jaka bakwai ne. In banda baba Lantana a zaune take sanda ya ambaci jaka bakwai din nan watakila da ta fadi kasa warwas saboda tsananin kadirwar da tayi, a'a jaka dari zaka ce ba jaka bakwai ba in ka tsaya a jaka balkwai ma ai sharrinka bai kai sharri ba la'anannen tsoho kawai matsiyaci da ma abidna ya sa ka zo kace in baka ita kenan don ka samu damar kullamin sharrin daka dade kana son kullamin? To bani da su ban ma san su ba. Nan take kuma ta soma rusa wani irin kuka. Ban yi mamakin ganin gigicewar baba Lantana kan ambaton kudin da Alhaji Nalami ya yi ba saboda a wancan loakcin jaka bakwai din ba karamin kudi bane kudi ne da ake iya siyen gida da su kudi ne da akc iya biyan aikin haji da su har aje a karbi guzuri na zunzurutun kudi dalar Amcrica dubu daya a can kasa mai tsarki, haka nan ko da ban san abinda yake tsakanin baba Lantana da Albaji Nalami a kan maganar kudi ba to nasan shi Nalami zaiyi wuya warai in yana da kudin da suka kai jaka bakwai balle ya iya bada su saboda bai da kamannin wanda ya mallaki irin wadannan kudaden. Yanzu nan banda fam hamsin dinika guda uku da ka bani ka taba kawo wani abu bayan nan ka bani? Sai da ya kara juya mata keya kafin ya ce, fam hamsin hamsin sau uku wasa ne? Tunda kika ambanci wadannan da bakinki ai sauranma zaki fito da su ai kin yi kokari ni kam ma ai duka nayi za ki ce ban taba baki komai ba k ma in ma iyakar abinda na baki kenan to zaman nawa sukayi a wurinki? Da a wurina suke ina ta juya abina da yanza nawa suka zanma? Sannan dukan tsiya da kik sa aka yi min fa? A nawa dukan yake? Nawa kuma na kashe wajen yin jinyar kaina? Dankwala dankwalan kajin da na rinka sayowa ina kawo muku kuna ci ke da mijinii da su lemon gongoni da na kwalaye fa? Su a nawa suke? Ko kina nufin za ku ci bulus ne? Sannan kwana nawa nayi ban fita kasuwa ba a dalilin jinayr? Zan dau asara ne? Ai kema kin san riba nafi ganewa ba na fahimtar asara. A fusace ta ce mishi to asara kam sau nawa kayi ta a rayuwarka? Babbar sana'arka fa daudu ne? Yayi maza ya ce yaurwa ga kudin kulla sharri da bata suna ai hada lissafni koami nayi n8 rattaba wuri daya don haka ki bani kudina tun muna sheda juna dake cikin mutunci tun bamu kai ga wulakanta juna a bainar jama'a ba don ba zai zamomin komai ba in kai maganar gaban alkali in kira masu sheadr zur mu yi lada da su su je su yi rantsuwa su yi min sheda gaban alkali ya karfar min kudina in biyasu ke ni na yarda ma in bar musu kudin duka su cinye zaifi min dadi akan ace na bar miki su. Fita min daga gida fita tun ban kira yara sun zo Sun nada maka dukan tsiya ba, tayi maganar cikin wani yanayi dake kara baiyanar da tsananin bacin ranta. Ya yi murmushi to ai gara ki hanzarta yin hakan kinga inda sai na tafi neman shedar zur kafin in samu biyan bukata a kotu sai ya zamo ba sai na yi hacan ba zan samu don hakan zan sake gaya mikiki bani kudina da na gaya miki jaka bakwai ko kin san tunda na ambacesu zan karbesu ai kin sanni sarai nima na sanki ni dake kar ta san kar ne kin san abinda zan iya da, Wanda ba zan 1ya ba, ya rantse da kwarankwatsa da aradud a matsattsaku in baki bani kudin nan ba, Ya gyada kai nuna alamar wani babban abu zai auku ko yanzu din nan in gaya niki babu fa inda zani sai kin bani don ba zai zame min komai ba in kwana a kan gadon da mijinki ke kwanciya irin kuma tsakaninku bari ma ki gani. Yayi maza yu mike ya nufi hanyar shiga dakinta itama tayi maza ta sunkuci tabarya taje gabanshi ta tsaya. Kasheni kenan za i yi da kika sunkuto wannan shirgegiyar tabaryar kamar za ki kashe maciji. Ai gara maciji da kai Nalami ai kai tsohon banza ne tsohon najadu wanda ya tsuta bai san ya tsufa ba kullum kai kenan kana riga fuska da jiki da shuri don na kashcka ai babu abin da zai faru shigowa kayi cikin gidana wadanda suka