Sashe 14
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ni ce mai zumudin maganar ba ni yar tawa ce. Wurin baba Lantana mai yade maganganu a tsakar gida na samu labarin wai ashe da baban nashi ya dawo ya kai mishi maganar sai ya ce mishi ba zai sake takowa ya zo wurin babana kan maganar aurena ba ya dai zuwanf arko ya kuma isheshi haka don haka in har auren yake so da gaske to ga 'yan mata nan bila adadin tun daga na dangi har bare yaje ya duba gida na mutunci ya zabi yarinya zai tsaya ya aura mishi ita ko da kuwa nawa zai kashe, amma bani ba in ba rashin hankali irin nashi ba ko iyayen Mubarak da suka san da dansu na rinka lalacewa ai ba su bar shi ya aureni ba balle shi. Wannan bayanin da naji a bakin baba Lantana ba Raramin dukan zuciyata yayi ba, don kuwan a riga na Sakankance na saki jiki zuciyata ta riga ta amince da maganar aurena da Mansur sai dai duk da haka ban bari yanayin da na sanu kaina a ciki ya baiyana ba sabdoa na riga na koyi shanye bacin rai ba komai ya taba zuciyarka sai na kusa da kai ya gane ba, haka nan 6acin ran da na samu bai sa naji haushin iyayen Mansur ba to balle kuma shi Mansur din da na tabbatar shima bai ji dadin hukuncin da aka zartar mishi ba, sai dai ya yi biyaiya kamar yanda kowane da na kirki yake yiwa iyayenshi biyaiya kan umarni ko hani da sukayi mishi, bai dai ce min komai ba nima kuma bance mishi na ji ba sai dai kuma biri yayi kama da mutum gaba daya ya canza fara'arshi, kuzarinshi duk sun sauya mainakon zuwa kullum ya koma yin fashi in yau ya zo gobe ba zai zo ba watarana ya yi kwanaki na yi kamar in ya zo in rinka kin fita sai kuma na ga to a na me? Rannan dai ya gaji shi da kanshi ya zaunar da ni ya yi min bayanin komai, hakuri mai yawa ya bani ya kuma rokeni kan kar gaya min gaskiyar da ya yi ya kawo karshen mutuncni dake tsakaninma, na ce mishi a'a ko kadan ba za a yi haka ba sai dai ma a kara nima nayi mishi godiya kan alherinshi a gareni. Ko ban tsaya yin bayani nayi bacin rai ko ban yi ba an san nayi saboda na riga na so aure na kuma soo Mansur don haka fadama batawa ne kawai. Tunda Mubarak ya taso ya zo gidanmu ya rokeni in fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba na Tura al'amura sun sauya a tsakanina da shi amma ban kara sanin irin tsananta da lamarin yayi ba sai a ranar da nayi shiri da niyyar zuwa gidan Yakumbo Halima saboda dadewar da nayi banje ba har na samu labarin korafinta wajen yaya Dija. 'Yar madaidaiciyar kwalliya nayi a dalilin tsala kwalliyar ta daina burgeni ta daina sanyani nishadin da ta saba sanyani a baya sai dai kuma bai hana kwalliyar tawa zamowa mai ban sha' awa ba. Ina tafiya cikin natsuwa ba tare da na damu da kallo ko sanin su wa nake wucewa bisa hanya ba har na kai ga shiga lungund a fi ta daga cikinshi zan bulla kan layin da gidan su Yakumbo Halima yake. Kasancewar lungun a matse yake gashi kuma da .yawan kwata 'yar hanyar da ake bi din ba wata mai fadi bane ya sani hi hanyar waiwayawa in ga wanda ke biye da ni yana taku cikin sauri dan in kauce mishi in bashi hanya ya wuce in har naga alamar akwai bukatar hakan, abin mamaki Mubarak na gani gabana ya yi mummunan faduwa bisa dalilin guda biyu dalili na farko shi ne faduwargaban da na saba samu a duk lokacin da na ganshi ko na ji nmuryarshi wanda kwanakin baya nakem urnar na rabu da shi to ya sake dawowa, daliil na biyu kuma shi ne mummunan kallon da ya tsiri yi min a tsakanin nan ko yana walwala ya hangoni sai ya yi maza ya daure fuskaw ani irin daurewa kuma mai tsanani. Na maida kaina kan hanyada nufin ci gaba da tafiyata, yayin da wani 6angare na zuciyata yake bani shawarar in karta kawai da gudu don in samu in yi nesa da shi tunda ga dukkan alamu zai kamoni saboda dogon taku: da yake amfani a tafiyar ta shi. Tsaya mana mu yi magana, na yi kamar ban ji abinda ya ce ba na ci gaba da tafiyata sai kawai na ji caraf ya kamo gyalena ya rike, ina yi miki magana kina ji nakina tafiya. Raina a bace saboda fusatar da nayi na rike min gyalena na juya da nufin yi mishi tuni kan hana shi yi min hakan da na taba yi in da hali ma in yi mishi tuni cikin tsiwa den kar gobe ya yi tunanin sakewa. Muna hada ido da shi gabana ya sake faduwa na yi maza na sunkuyar da kaina kasa saboda wani irin kallo da yake yi min wanda ban saba da shi ba. Kina nufin ko saurarona ba ki da lokacin yi da pake kiranki kina ji na? So nake in tambayeki yaya naji maganar aurenki da.masoyin naki tayi sanyi kamar ma babu ita? Sakarya kawai sokuwa mara wayo wacce rashin mafadi ya hanata sanin abinda ya kamace ta in taso in zo in rokeki ki fita hanyar shi ki ce min wai ba za ki yi ba? Ai nayi hakan ne don ina zaton ina da matsayi a wurinki saboda kin yaudareni kin yi min abinda na yi zaton ni din daban ne a wurinki sabdoa kin yaudareni kin yi min alheri wanda na yi zaton bani da abokin gami a wurinki, ashe ba haka bane to amma kuma na gode shi da akayi mishi hani a kanki ya hanu. Gabana sai harbawa cikin sauri yake yi, bakaken maganganunshi sun yi tsanani da nauyi cikin zuciyata kokari mai yawa nayi kafin na danne hawayen da ke shirin zubowa a idanuna na hanasu zuba don kar in yi kuka a gabanshi don haka najuya da nufin ci gaba da tafiya, sai naji ya ce, ni babu inda za ki sai kin bani amsar tambayar da na yi miki. Cikin natsuwa na bude baki wanda bai ma san zan bashi amsa ba dan ya san ban cika yin hakan da shi ba na ce mishi, kayi hakuri ba yaudara ya sani yi maka hakan ba kuskure ne. Ya yi maza ya gyara tsayuwa tare da kara tsareni da idanuwanshi cikin saurarona binda zai kara fitowaa daga bakin nawa, ni kuwa ban fasa ba na ci gaba da yi mishi bayani, kuskure na yi nayi maka abinda na yi makan wanda ya sanyaka yin tunanin kana da matsayi na daban a wurina da har zaka ganni a masoyina ka roki alfarmar in fita hanyarshi, ko Mansur ya rabu da