Sashe 18
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai zo ba babu yanda za a yi a yi shi, watakila mijin naki bai zo ba, ita kuma mace bata aure sai mijinta don hakaki dawo karatu kin gane ko? Nace mishi to malam. Kar fa kice min to'ki zo baki dawo makarantar ba don sau biyu ina turo yara abokan karatunki su zo su kiramin ke ba ki zo ba. Kamar ince mishi babu wanda ya zo ya kirani sai naga bari in yi mishi shiru kawai. Ai ba a girman da ake wuce yin karatuna addini, shi dan adam yana rayuwa ne a kan neman ilimin sanin nahalicci don haka ki dawo makaranta kin gane? Na sake ce mishi e malam. Muka yi sallama ya tafi nima na shiga gida, a zuciyata na'rinka tunanin ko su waye malam ya turo su kirai oho, ina cikia tunanin hakan sai kuma na watsar na bari saboda na gane sanin ko.su waye din ba zai amfanar da ni da komaib a. Zuwan da malam Yahuza ya yi ya sanya ni na ji wani canji cikin zuciyata saboda irin nasihun da ya yi min, kwadayin karatu ya sake dawowa cikin raina, sai dai kuma yaya zanyi in sake fuskantar yan makarantar bayan duk irin kwaramniyar da na yi ta fama da ita? Da wane idon zan sake kallonsu? Wannan shi ne abinda ya fi komai tsaya min a rai. Kwana biyu bayan zuwan malam har lokacin ban fara zuwa makarnatar ba sai dai kumna bana jin dadin hakan da nayi, in na yi tunanin menene ya dame ni wanda ya sa zuciyata take yi min nauyi? Sai int una malarn Yahuza ya tako har gidanmu ya nemi in koma makaranta in yi ka ratu abin yi hakan ba, abinda ni da kaina na sani ba sai an gaya min ba yin hakan rashin girmamnawa ne ga na gaba musamman malaminka. Rannan dai na daure na tafi gabana kuwa sai faman bugawa yake yi, kirjina yana ta faman harbawa da sauri-sauri, a tsarge kawai nake zaune a ajn motsi mai dan karfi in akayi sai inji na kara takura in yi kamar ni ake nunawa ko ake bada labari na. Malam Wahuza ya yi matukar farin ciki da ganina ya yi mana karatu ma1 gamsarwa ya yi mana kuma nasiha kan yan uwantaka irin na musulunci tare da bayani kan wanene musulmi? Lokaci mai tsawo ya dauka yana bayani akan siffofin musulmi na kwarai da Manzon rahama (S.A.W) a kai daga cikinsu akwai kubutar musulmi dan uwanka daga sharrin harshenka ya gama, ya y mana addu'a muka shafa nad awo gida. Na soma zuwa makaranta a kunya ce a darare sai dai ba a dauki lokaci mai tsawo. ba sai na wartsake har ma karatun nawa ya zamo daga cikin abubuwan da suke ragemin damuwata su nutsar min da zuciyata musamman ma da yake yayi dalilin da na koma yin karatun Alkur'ani mai girma sosai da sosai wanda da na daina yi saboda damuwa da rudewa in ba haka ba ai na dade ina jin malamai suna fadin cewar shi Alkur'ani waraka ne ga duk wata cuta ciki kuwa har da na zuciya. Daga komawata makarantar Islamiyya sai mu'amala mai karfi ta kullu tsakanina da malam Yahuza, saboda kullum idonshi yana kaina na zo makaranta ko ban zo ba. Ki koma makarantar oko don ki samu damar mallakar takardarki ta karatun college, na ce a'a malam ai ni bokon nan ba wani damuna yayi ba. Ya vi murushi to at ko bai dameki ba kin rigakin yi shi takardar da za ki mallaka ta zame miki shedar wahalar kiken emaki yi wasa da ita, alhalin ilimin yanzu ya ta'allaka ne a kan abidna aka gani a rubuce don hakaki koma ki yi karatunki karki yi wasa da lokacinki, shi lokaci da kike gani ba a wasa da shi tsada ke gareshi, baki ji abin da wani bature mai hikima ya fada ba? Ya ce "A man who dares to waste an hour of time was not discovered the value of life. Mamaki ne ya kamani jin da nayi malam Yahuza yana rangada lafiyaiyen turanci da bakinshi bayan na dauka arabiya ko larabci kawai ya iya. Shirund a nayi ya sashi tambayata ko kinfi gane dai ki jira mijin aurenki ya zo ki yi.aurenki kawai? Shiru nayi ban amsa ba iyaka dai kaina a sunkuye ban kalleshi ba, amma nasna murmushi yayi kafin ya ce min, iaina zamna jiran miji Maryam saka al'amura masu yawa a gabanki sai ki ga ma yafi saurin zuwa gareki tunda shima ya san bashi kadai kike jira ba kin gane? Na ce mishi to. Kalamai da nasihohin da malam Yahuza ya yi ta yi min su ne suka karfafa min zuciyata da ta riga ta karaya da al'amuran rayuwa har na rinka ji da ganin tamkar bani da wata mas'ala ko damuwa a tare dan i in dai ba ta rashin lafiyar babana ba ne. Makarantar koyar da sana'o'in mata ta Markas wacce Mansur ya taba bani labari na shiga da taimakon malamina malam Yahuza shi ya karbomin form din na cike ya mayar ya kuma biya kudin form din gashi kuma anyi sa'a kyau ta ce form din kadai ake saya, ajin dinki na shiga shi en.a raina tun sanda Mansur ya ce min ya fi sha'awata da yin dinkin. Na fara zuwa Markas mas'alolin da na fuskanta ba su wuce na wahalar tafiyar kafar da nake yi da kuma dawowa gida da nake yi ban samu abincin da zanci ba sai na nemawa kaina hakan kuma na jira. Na wayi gari rannan ina gida banje wurin koyon sana' ata wato Markas a dalilin renar da Jumaa ce ranar Juma'a kuma ranar hutu ce a garemu, ina kwance kan gado na na hutawa bayan na kammala wanke mana kayanmu ni da babana sai kawai naji Sallau yana cewa uwarshi, kai an aun arziki yau dai an daura auren Asabe magana ta kare. Sauri nayi na kara maida hankalina wajen jin maganar tasu tare da tunanin Asabe tayi sa'a itama ta samu tayi aure dukd a cikins hegen da tayi ta haihu ni ce dai... kan in karasa tunanin zuciyar tawa sai naji baba Lantana ta ja wani mummunan tsaki tare da fadin, to wani kokari kayi a hakan? Ina ce takardar filina da ya karba kawai nace ka karbo min a matsayin sadakin auren nata ka kasa ka karbomin nera goma. Ya ce, uhun baba kenan ba ki ma san yanda akayi ya bada nera goman bane abinda ja yayi ya tsaya a kan nera bakwai zai bayar sai da malamin da zai daura auren ya ce mishi bai kai rubu'u dinar din da shari'a ta yarda a karba a matsayin sadaki ba shi ne ya bada goamn, ni dai tunda Asabe ta samu mijin aure zata isa gidan mijinta yau danta kuma ya samu uba ba zai yi ta watangaririya a hanya bai san ubanshi ko danginsu ba ai shi kenan magana ta kare a wurina. Duk da ganewar da nayi Alhaji Nalami Asabe ta aure kalaman da Sallau ya yi sun sani girmamashi tare da auren da Asaben tayis aboda na gane aure daraja ke gareshi Sallau kuma na gane natsattsen yaro mai kuma hankali tsayaiyar tarbiya ce kawai bai samu ba. Na fara zuwa wajen koyon sana'a ta a Markas babu dadewa'sai kuma malam Yahuza ya sake yi min magana kan wata babbar makaranta ta ilimin addini mai zurfi da aka bude duk da irin kudaden da ya yi min bayanin za a kashe kafi in so ma karatun na shige ta saboda yaya Dija ta amince da shigar tawa ta kuma bayar da duk wani abinda aka nema shi kuma malam Yahuza sai ya taimaka min da manyan litattafai masu tsada a matsayin aro kafin ta samu ta saya min nawa in mayar mishi da nashi tunda shima ba daina karatun ayyi ba tunda shi littafi abin ajiyewar dalibi ne. A wannan lokacin sai na zama kusan kullum ina da abin yi mafi yawancin lokacin ma nakan fita da safe ne in dawo da yamma saboda zan tashi daga nan in nufi can don ma dai kawai babana yana raina kowane lokaci. A wannan lokacin baba Lantanaa wuni take yi tana yiwa babana gorin auren da Asabe tayi da na hada 'yarka da shi kuka ki ai gashi ni na bashi tawa tana kuma zaunen abin ta tsaf cikin rufin asiri da kwanciyar hankali ga mutunci shi aure ai darajarshi yawa ne da ita ba kowane yake samun darajar yin shi Na jinsu bana cewa koami, iyaka dai na sani na kuma yarda da kalaman nata duka iyaka dai can cikin zuciyata a yanzu bani da damuwa mai yawa kan maganar yin auren nawa na yarda na kuma gamsu da cewar dak ullum malam Yahuza yake yi na komai lokaci ne kowa kuma yana da nashi lokacin, Nalami kuwa in dai shi zan aura to ina ganin kamar gara in yi rayuwata kawai a haka ya fiyemin don haka ko kadan bana jin zafin kalaman nata. Ina zaune a dakina bayan na idar da sallar magariba takardun da zan tafi da su wajen malam Yahuza nake hadawa saboda muraja'ar da yake yi min kan wasu darussan masu dan nauyi da nake bukatar fahimta mai kyau a kansu, har zan yafa hijabina in fita sai kawai naji yaro ya shigo yana cewa wai ana sallama da Maryam a waje. Na daga ido na kalli agogo cikin zuciyata na ce kar dai Halliru ne ya z0 a wannan lokacin. Halliru shi ne sabon saurayina da Yakumbo ialima ta turo min a dalilin ya ce mata ta duba mishi budurwa mai hankali da iya kwalliya kasancgwar shi dan mijinta da ta rike ya sa ta ce bai dace da kowaccc budurvwa ba sai ni, ni kuwa a wannan lokacin bani da wani zabi na daina Pzaba ince ga irin saurayin da nake so ko ga irin mijin da zan aura, aurcn kawai nake so wanda duk yazo kuma a shirye nake zan aure shi, in dai huta babana ma ya huta mu duka mu huta damunmu da ake yi ana bada bayanin mu a kan idona sai ka ji dattawan unguwar suna cewa ai nan