← Book details Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 25

Sashe 10

Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

HE IS IN SHAKKLE" Da na natsu na dawo cikin haiyacina sai na samu kaina a yanayi na godiyar Ubangiji da ya taimakeni ya rufamin asiri ya bana Mubarak karbar kyautar da na yi mishi, in tuna kaina in tabbatarwa kaina ni din budurwa ce gal a leda, shi ne abin da yafi komai sanyaya min zcuiyata a wannan lokacin. Bikin Mubarak da kwana goma na hangoshi tsaye a Rfoar gidansu a dalilin fitowar da nayi za ni shago don sayawa babana ruwan swan din da nake amfani da shi wajen bashi magani, ban san yanda akayi ba ina tsaye as hagon nan cikin 6ari saboda kaduwar da nayi a dalilin hangoshi da na yi wanda shi ne ganina da shi na farko tun bayan faruwar abubuwan da suka faru a tsakaninmu. Motsi na ji a bayana tare da shakar wani irin sanyayyan kanshin da ya yi sanadin da na yi matukar tsarguwa da zuciyata ta yi, da sauri na juya don fidda rai daga zato saboda in samu natsuwa a tare da ni, sai kawai idanuwanmu suka hadu an yi maza najuya don karbar abinda nace a bani, jikina sai rawa yake yi har rkarwa tamkar sanyin hunturu ne yake kadani, cikin wata irin kwalliya yake ga kamshi gashi in ba kuskure nayi ba sai naga kamar kiba ya yi, nan tkae na ji Zuciyata tana gayamin shi bai da damuwa shi dadi yake ji, shi hankalinshi a kwance baida wata matsala a tare da shi, da sauri na mika hannu na kar6i ledar siyayyar tawa da ya yi nufin karba, ban 6ata lokaci wajeu tsayawa karbar canjin ba nayi maza na bar wurin. To tsaya mana Mero jirani mana ai wurinki na zo. Bai ji kunyar fadin hakan ba a gaban mutanen da suka cika a shagon, ina jin maganganun na shi na yi amza na kara maimakon sauri na yanka da gudu nayi amza na shige cikin gidanmu ba tare da na saurareshi Kwana biyu bayan nan na fita gida da sassafe don sayawa babana kunu da kosan da na saba siya mishi, ina zaune wurin mai kosan ina jiran ta zubamin saboda na samu wasu a gabana da yawa sai kawai na ganshi ya iso wurin, kallo daya nayi mishi nayi maza na sunkuyar da kaina na.dora hannu akan guiwata yayin da na zagaye guiwar tawa da hannayena duka biyu, doguwar farar jallabiya ce a jikinshi duk da ban tsaya kare mishi kallo ba nasan ta karbeshi. Ina kwana baba? Ya soma gaida baba mai kosan tana amsawa, lafiya lau Amadu ya ya su Hajiya da iyalin naka? Lafiya lau. Ya amsa mata, sakun kosan bai so kan Mero baba nc? Da sauri ta ce mishi ko baizo ba ai sai a zuba mata Amadu. Nan da nan ta zuba da yawa fiye kudin da na bata ta kunsa ta mikomin nasa hannu biyu na karba na dora a kan murfin kwanon kunun na dauka na kama hanyar zuwa gida, Mubarak yana biye da ni babu halin in ruga da gudu in tafi in barshi saboda tsoron kar kunun nawa ya zube. Ki tsaya mu yi magana mana Mero. Ban kula shi ba tafiyata kawai nake yi, ban fa yi miki laifin komai ba ballekice na za ki yi fushi da ni, ni da ke mun shiga wani irin al'amari ne a dalilins harrin da matar babanki ta kulla mana na kuma san ba zai yiwu ta shanye ta gama lafiya taga yanda take so a rayuwarta ba tunda ita sharri tasa a gaba, in ma kina da wani tunani ko kulli game da ni a zuciyakri to ki yi hakuriki sake kawai duk abinda kika gani kuma ya zama dole ne kawai ya sa kika ganshi a yanda kika ganshin, a shirye nake kuma in yi miki bayanin da zai gamsar da ke. Ban kalleshi ba balle in tanka mishi har muka zo kofar gidanmu muna isowa kuwa nayi maza na wuce cikin zauren gidanmu na barshi a can waje. Tun daga nan na zama bana fita daga gida kai tsaye sai na dan tsaya na yi waiwaye waiwaye in tabbatar ban hangoshi a kusa ba. Rannan ina zaune a dakina ni kadai sai ga Isiyaku ya shigo yana sallama, na amsa sallamar tare da bashi izinin shigowa, ya nemi wuri ya zauna muka shiga gaisawa har da yin hira tun da dama can abokin hirana ne, na yi ta tunanin abin da zan dan kawo mishi ya dan taba saboda nuna girmamawa ga bakonka ban tuna ba don bani da komai a dakin don haka na hakura muka ci gaba da hirar a haka jimawa can sai ya ce min, Mero ni zan tafi. Nayi maza na ce mishi ai na gode maka Isiyaku sai dai ka shigo yau dakin nawa babu komai a cikisnhi. Ya yi murmushi tare da fadin, babu komai. Ya dan karkace kadan sai naga ya zaro wata takarda daga cikin aljihunshi ya miko min tare da takardun kudin naira ashirin ashirin cunkus a hannunshi wai gashi in kawo miki. Nayi maza na zuba musu ido tare da tambayarshi menene wannan? Cikin natsuwa ya yi min bayani, wasika ce tare da kudi ya ce in kawo miki. A hankali na sake tambayarshi, in ji wa? Ya dan yi murmushi kadan kafin ya ce min, inji yaya Mubarak mana wa zai yi mik i irin wannan aiken in ba shi ba? Ya baka kudi ba kawo min? Ina yi mishi tambayar na soma kuka tun katin ya kai ga amsa min nan da nan ya hidime ya shiga bani hakuri yana yi min magana, to menene in ya baki kudi an shi Mero? Yanda duk kika dauki abin fa ba haka yake ba shi yaya Mubarak. Na yi maza na katseshi, dakata na fadi hakan tar da share hawaycna da bannayena duka biyu, maida mishi kudinshi tare da wasikar na rokeka ka gaya mishi yayi hakuri ya fita harkata bana son kulanin da yake yi bana so bana so, ka gaya mishi na ce bana so. Zai yi min magana na yi maZa na salke ce mishi, acte bana so ko kuwa dole ne? Ya mike ya fita, ya tafi ni kuma na kwanta a nan wurin naci gaba da kuka cikin tsananin bacin rai da takaici, wautar kudin ce ta fi komai kona min rai wato ni kudi ne bukatata, duk abinda akayi min na wulakarici da tozartawa aiken kudi ya kanmata a yi min? Na tuna kalmomin da na ji baba Lantana tana furtawa na rainin arziki ne yasa iyayenshi suka hanshi aurena saboda sun ga babana ba kowa bane face mai saida timatiri, zuciyata ta sake rayamin wasu abubuwan, ya yi aurcnshi ban kulashi ba ban shiga harkarshi ba yana nema ya rinka shiga nawa bayan an tabbatar min da cew r har da fita hanyita cikin sharadin da babanshi ya'sany *mishi, ya amsa sanna ne ya cce ya yafe msihi ya dawo gida; to menene kuma ya saur tsakanina da shi? Ban san dalilk b sai na samu kaina da bacin rai mai yawa da na-kasa daurewa zaman gidan ma ya gagareni na nemi izini wurin babana na shirya na tafi gidan yaya Dija. Tana ganina da yar jakarta dana zbe yan zannuwana na canji a ciki ta saki mirhushi, 'haba to ko ke fa? Ai tun ba yau ba nake fama dake ki baro unguwar nan ki zo nan mu dan kwana biyu tare ki dan huta, ni hun ban cika son barin baba bane a gidan nan shi kadai yanzun ma na dan fito ne kawai. Na kwashe bayanin komai nayi mata ban 6oye mata komiba. Cikin natsuwa ta kallehi, kin san abin da yafi bani tausayi a cikin al'amarinki? Na yi maza na ce mata a'a, sai kawai na ji ta ce min, wai son Mubarak da kikeyi. Nayi maza na cem ata ni? Ta ce eh ke. Nace la yaya Dija ni ai ba son shi nake yi ba. Tayi maza ta ce, ke. matsa can ki bani wuri karki nemi maidani yar nya karama mana in bakya sonshi meke sawa ki na yin bacni rai a kanshi, meke saki kuka? Ai so ne Mero, ya yi miki aike ba yau ko ji a ya fare ba ya dade yanayi ba wulakanci bane in yanzu kin daina karba shi kenan babu 6acin rai a ciki da har za a je ana ta kuka shawarar da zan baki ita ce ki fidda shi a cikin ranki fito da miji kawai ki yi aurennki ga Mansur. Na yi maza na katseta ta hanyar fadin kai Mansur? A'a ni yanzu bana son kowa. Ta sake zuba min ido saboda Mubarak da iyayenshi sun ki mu shi ne shima Mansur laifin zai shafeni, ai in ban manta ba a nan ne mukayi maganar nan da ke cewar da Mansur din da kuma Mbarak rdukansu daya ne wanda duk maganar aurent a kama za a yi da shi, to ba za ki samu mas'ala ba za ki zauna lafiya da shi za kuma ki yi mishi biyaiya domin su dukansu biyun masu alheri ne babu kuma wanda zai iyakacin lokacinki a kanshi. Nan take nas oma yi mata kuka saboda jin irin kalaman da ta tsareni da su na baro gide na zo wajenta don in huta ita kuma ta zo tana yi min wasu maganganu da suke karawa zuciyata nauyi. Assalarmu alaikum, wai ana sallama da Mero a waje. Sau biyu yayi maganar kafin na takarkare na daka mishi tsawa wanda watakila tsayar da nayi misHi'ne ya yi dalilin fusatar yaya Dija tayi maza ta zabura ta mike tsaye ta ce min, maza tashi ki je kiga waye mai kiran naki ai don Mubarak ya yi aure ba zai zamo danin karewar maza a duoiya ba, da ke wata mai zuciya ce ma da tsayawa kikayi kika fidda mijinki nan da kwata talatin a yi bikinki ki tafi gidan mijinki kije ki yi zaman aurcnki kowa ya huta. Na tashi na fito don ba zan iya yin jayaiya da ita ba. Mubarak na gani tsaye a kofar gidan tsaye jikin motar tashi da ga shi har ita sai wani sheki suke yi suna daukar ido, ga dukkan
Chapter 10 · 0% Book details