Sashe 24
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da kudi ne da za a yi min amgana da bazawara? Sannan da girmana da komai ita mace ace miki tana son tsoho ne a shekarun. kuruciyarta. A hankali na ce mishi, baba ai ita yaya Dija ina ganin kamar sun fahimci juna ita da matar tace min ne in yi maka magana in ka yarda ta turo maka ita don ka ganta, a hankali ya ce a'a ni kam ai ba sai na ganta ba in dai ku tayi muku ai shi kenan fitina ce dai kawai ni bana so. Nace mishi too nayi mishi sallama na tashi na tafi, can cikin zcuiyata kuwa mamajki nake yi ban taba zaton haka amsar babana zata zamo ba, na kama hanyar tafiya wurin malam don karbo alkawarin da akayi duk da wata zuciyar tana nunamin in fara ganin yaya Dija tukunna sai kuma naga to bari dai kawai inje can din in yaso in na dawo sai in biyo ta wurinta in yi mata bayanin yanda muka yi da babana daga nan kuma taga abin da na karbo wurin malam. Wajen karfe goma sha dayan safe na isa kauyen nan inda daga shine muka soma yin tafiyar kara, nayi tafiyar kafar har na raina kaina sai da na soma kaiwa matuka wajen gajiya ne ma na tuna ko sunan malamin da zani wurin nashi ban ji ba balle kuma na kauyen da zanin, abin ace na bata hanya ban san yanda za a yi inyi tambayar da zata zamo mai amfani a gareni ba, sa'a kawai nayi da na ci gaba da tafiya sai kawai na ganni a mararrabar nan wacce daga ita ne muka dauki hanyar da ta nufi gidan malam. Tsayawa nayi cak. na zubawa hanyoin nan ido ina kallonsu tare da tunanin wacce muka hau ne a ranar? Na gaji da dubawa na yankewa kaina bari kawai in hau kan guda daya tunda bajuyawa baya zanyi ba don haka na kama ta tsakiyar nayi ta tafiya a kanta banga komai ba banga wata alama da na gani wacce ta karfafaa min guiwa ba don haka na juyo da baya zuwa inda nararrabar nan take na sake zabar wata hanyar na hau an nma nayi iyakacin iyawata nayi tafiya sai da na fara debe tsammani ina cikin tunanin komawa da baya kawai in koma gida inje in gayawa Yakurmbo Halima cewar ban gane hanyar ba tazo kawai ta karbar min maganin da kanta ko ta tasoni a gata mu zo tare kamar yanda tayi min rannan tunda ni na kasa gane wurin da kaina sai kawai naga mutum tsaye cif a gabana tamkar daga sama aka jehoshi, tsoro ya.yi matukar kamani ba tare da ya ce min komai ba sai naji ya ce min, wuce mu tafi malam ne ya turoni in kai mishi ke saboda an gaya mishi cewar kin kauce hanya don haka ya kwatantamin inda zan sameki shi yasa na yanko ta cikin bishiyoyin can, nabi hannun nashi da kallo don inga can din da yake magana akai, wani irin surkukui ne da sunkurun duhun bishiyoyi da ban taba tunanin dan adam zai iya shigarsu ba ban iya buda baki na ce mishi komai ba haka nan duk da tsananin tsoron da nake ciki n ba zai yiwu in yi musu binshi ba tunda ban san inda zan dosa ba. Tasani kawai yayi a gaba muka kama hanya 'yar tafiya "yar kankanuwa sai kawai gamu mun isa gidan. Shiga nan, yana bani umarni nayi maza na shiga sai ga malam zaune daram a kan buzunshi cikin manyan kaya ga hularshi a kanshi yayi kwalliya irin wacce ta dace da shi. Maryamn da so ya kira sunan nawa yana ma kallona, ina babar taki? Na isar da gaisuwarta gareshi bayan na gama gaisheshi ya ce, alheri ya gaieta, ai ga kwaryar da na hangki a ciki can, nayi maza na waiwaya na kalli kwaryar da ya ce min daga cikin nata ya hangeni babu komai a ciki in banda ruwa, na sake juyawa gareshi na kalleshi don jin bayanin da yake yi, yayin da zuciyata ke ta faman harbawa 6al 6al 6al, daga nan din ne na kira wanda ya daukokin don kar ki je ki yi wa mutanen hanayr da kike ta kakkaucewar wani ta'adi unda su di mafi yawancinsu ba hakuri ne da su ba. Wani mutum ya ashigo rike da zangarniyar dawa a hannunshi ya tsuguna ya mikawa malam, bai kalleshi ba ya ce mishi, kwaya bakwai nake bukata, ya mika mishi kwaya bakwai din ya fita da zaugarmiyar a hannunshi. Malam ya jawo wani tsohon kasko fasasshe ya debo kasa tafin hannunshi uku ya zuba a ciki ya dauki tulun dake gefenshi ya jika kasar da ruwa ta jiku sannan ya shuka kwayoyin dawan nan guda bakwai a ciki kan kace meye wannan sai kawai naga dawar nan da ya shuka a kan idona ta kamna tsirowa a cikin kaskon, nan na zuba ido ina kallon abin mamaki wanda ben at ganin kwatankwacin makamancinshi ba, na yi matukar kokarina wajen 6oye halin da nake ciki na tsoro saboda ganewar da nayi ina cikin wani babban al'amari,don haka nayi maza na soma karanto addu'o'i na neman tsari. Kina da wani wanda ya dameki ne a yi miki maganinshi? Na'am na amsa ina kallonshi don ban fahimci abinda maganar tashi take nufi ba, eh abinda nake nufi kenan in kina da wani wanda ya dameki kawo sunanshi mu gwada miki aikinmu a kanshi ta hanayar kashe miki shi nan take. Kalululu, sautin da cikina ya bayar kenan a lokacin da na ji maganar tashi, da kyar na iya girgiza kaina don nuna mishi alamar babu, cikin zuiyata kuma tarnbayar kaina nake yi me yasa malam yake yi min irin wadannan abubuwan tunda ni ai ba abin da ya kawoni wurinshi kenan ba, sannan me yasa bai yi ba ranna na gaban Yakunbo sai yau da ya ganni na zo ni kadai Kina saurarona? Na yi maza nace mishi eh, ita babar taki ta yi miki bayani a kan ka'idojin aikinmu ko? Na girgiza kai nuna alamar a'a, to muna da ka'idojn da karyasu yake da hatsari kwarai shi yasa muke bayani a kansu don kar mutum ya jawa kanshi wata fitina da zata zo ta dameshi ta damu duk wani wanda yake tare da shi, ba a yin musu da umarnin da ake bayarwa anan ko mai tsananinshi, sannan ba a yin gardama ko jayaiya domin nan din Wuri ne da ake mu'amala da nau'o in halittu guda uku wato jinsi mutane da na aljanu sai kuma rauhanai don haka ba wurin wargi kika zo ba, yin daya daga cikin ukun can dana ambata miki ina nufin musu gardma ko jayaiya sakamckonshi yin hauka ne hauka kuma irin wacce bata warkewa. Cikina ya sake bada wani sautin na kulutuiu har ma ya fi na farkon karfi saboda tsananin tsoro da na samu kaina a ciki din. Kin taba ganin aljani ko rauhani? Na yi maza na ce mishi a'a, to ai za ki ganshi yau din nan. Na ji kamar in zabura in mike in karta da gudu in shige cikin dajin nan in huta. Ya gyara zama ya soma yi min bayani, kin san akwai jinsih mutum da na aljan da raunahni kafin mala'iku ko? Angi maza na ce eh ba tare da na fahimci koami ba da yake nufi ba. To mu nan fadar rauhani kika zo ki gane? Na sake yin karfin halin cewa eb. Ya zuba min ido yana kallona ban sani ba ko shima ya gane halin da nake ciki na tsoro ne. Yanzu kafin rauhanin da zai yi miki aikin ya iso tunda mum riga mun kirashi yana can yana dawafi ne in ya gama zai taho, kin taba yin sata? Tambayar tashi ta zo min a bazata, na yi maza na kalieshi don inji ko abinda aa jin daidai ne, ya ce eh abinda na tambayeyi kenan, kin taba yin sata? Na ce mishi a'a, sata ko wacce iri baki taba ba? Kin san fa ba a karya a nan, in ka riga ka shigo nan to gaskiya da gaskiya ne kawai, in kayi karyar ma za su gane ka don baka yi tunani sosai don kar su kamaki da laifin yin karya. Na gama tunanin da zanyi sai na ce mishi, sai dai ko na abinci ko naman miya a wurin matar babana. Ya yi maza ya ce, a'a ai wanna ba sata bace bari kawai a gaya musu baki taba sata ba ko da yake ma suna nan tare da mu suna jinki, ko kina yin karya? Na dan yi shiru cikin nazari kafin .shima na ce mishi wani loakci na kan yi amma ba ko da yaushe ba. Ya gyada kai tare da fadin, to babu laifi ya yi kya, kina da kiyayewa kenan? Na ce mishi ch, to ai shi kenan sun jiki, tambaya ta karshe ki fa yi hakuri ba daga ni bane kaidarsu nake bi don haka suke bincike kan kamewar mutun kafin s shigar mishi, kin gamsu? Na ce eh. Kin taba yin ziua? Na girgza kai na nuna alamar a'a, to ai ma shi kenan aikin naki mai sauki ne tunda baki da kazanta mai yawa a tare da ke sai ta kananan zunubai wannan kuwa dukkanmu ne don haka ki kwantar da hankalinki shi wannan nikin naki mai sauki ne kwarai an yi irinshi yafi sau nawa anan in dai kin bada hadin kai ai shi ke nan tsanani wana uku ne zuwa bakwai magana ta kare don haka bari ya iso ya sallameki, na riga na ji tasowarshi don haka bari in yi miki tuni ka'idojinshi banda musu banda gardama banda jayaiya ba abokin wasanki bane sakamakon yin hakan hauka ce da babu nagani kin gane ko? Na ce eh, can cikin zuciyata kuwa addu'o'i nake ta yi na neman rabuwa da rauhani lafiya. Ana cikin haka naji wani abu ya fara bayar da wani sauti na shuuuuuw sai dai ban san daga ina yake fitowa ba, wata irin iska'mai sanyi ta fara shigowa dakin. Yauwa gashi nan ya doso mu gashi nan ya dunfaro gashi nan zuwa kar ki mance da abinda na gaya miki don ni