Sashe 19
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
kusa kusa duk ai babu sauran sa'arta kai kannenta na kusa ma babu duk sun garna yin aure sai ita kadai. Na debi littafin nawa na rungume na jawo kofata na rufe na yiwa babana sallama na fito da nufin in mun gama maganar da za mu yi sai kawai in wuce na kuma san ganina tare da litattafan a hannuna zai kara sashi tafiya da wuri tunda yasan ina da abin yi. Ina fita waje maimakon in ga Halliru, Mubarak na gani a tsaye, wani irin lalataccen kallo ya yi min da ya sanya gabana faduwa cikin zuciyata na yi maza na ce, ban yafe maka ba zuwa kofar gidanmu da kayi ka fadar min da gaba. Shima malamin naki yana nema ya rikide ne ya Zama saurayinki? Da sauri na daga ido na kalleshi cikin tsananin mamaki abinda ban taba zaton wani zai yi tunanin hakan ba don babu wata alama da take nuni da hakan. Idan kika kuskura na gane da wani abu a tsakaninki zaki bar karatun naki gaba daya ki koma Zaman gida in kumakina ganin kamar wasa nake yi to bari in gane halkan ki gani kina nufin don yana koyar da ke karatu a da sai kuma a yanzuki rinka kwasar litattafaikina zuwa wurinshi kuna zama ku biyu? A kidune nace mishi, ba fa mu biyu bane? Ya yi maza ya katseni ko ku dubu ne ban yarda ba kar in sake gani ko jin kin fita daga gida bayan sallar magariba, na gaya miki. Kuka na soma yi mishi saboda bakin cikin abinda yake yi min, takuraw ar ta kai duk inda ta kai, komai nake yi ya sani ko baya nan nayi in ya dawo zai ji labari. Cikin karfin hali na daure zuciya ta na ce mishi, to wai ni ina ruwanka da ni ne? Ina abinda ya shafeka da abinda nake yi, kullum sai ka shiga harkata, kullum sai ka takurawa rayuwa ta. Ban san dalili ba rannan sai na kasa zuwa wurin mraja'ar da Malam Yahuza ke yi min, maimakon washegartnma inje ban i cb a sai kawai na hakura da muraja' ar na koma maida hankalina sosai a aji wajen fahimtar dukkan darussan da ake yi mana. Kullum dai burina bai wuce in samu lokaci in tatawa Mubarak rashin mutuncin da zai sa ya fita harkata kwata-kwata ba amma in na ganshi sai in kasa saboda kwarjininshi da yake yi min nauyi a idona. Gabatowar watan azutin ra:nadan mai girma ya sa aka shirya mana jarrabawar da a bayanshi muka samu hutun makaranta har sai bayan salla mu koma, farin ciki sosai nayi a wannan. Jlokacin a dalilin jarrabawa ta tayi kyau banda haka zan dan samu hutun wahalar da nake yi ta zuwa makaranta da kafa in dawo da kafa, Sannan zan dan fuskanci wani abinda nake kuma dokin yi shi ne dinki don na dan fara iyawa har yaya Dija ta gamsu da labarina bayan dinkin 'ya'yanta dana dade ina yi musu ta hada min har da nata nayi a dalilin hakan kuma ta ma karbar min na kawayenta da abokan zamanta. Ki natsu sosai ki yi musu mai kyau don sai ya zamo tamkar tallan iyawarki kikayi, nace mata to. A wannan lokacin hutun makaranta da dokin dinkin azumi da nake yi ne ya ragemin damuwa ko bacin ran da na samu kaina a ciki ra turowar da Halliru ya yi a ka karbe mishi kayanshi, shi ko kayan na gani ina so kamar yanda wasu suke fada da da ya kawo gidan mu haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba wadanda suka kawo kayan suka zo suka ce a yi hakuri a basu bisa wasu dalilai da suka ce wai su ne sukayi dalilin in sa auren nashi a wannan lokacin. Yakumbo Halima dai ta ce min wai yayi mata bayani da cewar ya fasa auren ne a dalilin akwai wani dodo dake biye da ni mai tsoratar da mutane matukar kuma ba a tsaya an rabani da wannan dodon ba to aure na zai yi wuya. Bayanin 1ashi ya yi tasiri mai karfi a zuciyar Yakumbo don salati ta rinka yi tana fadin, wai dama tuni ta dade tana tunanin watakila aljani ne da ni wanda ya hanan11 yin aure. Ni kam tattara maganar nayi na ajiye a gefe ban yarda ba ban kuma karyata ba don ban san komai a kan irin wedannan al'arauran ba, abu guda daya dana sani na kuma yarda na tsaya a kan shine gaba daya mu mutane da kuma aljanu dukkanmu bayi ne na Ubangiji babu mai ikon cutar da wani a tsakani sai da abin da Ubangiji ya yarda ya kuma kaddara fil azal wannan din zai cutu da shi, wannan shi ne bayanin da kullum malamin mu na tauhidi yake yi mana da sai kuma na yarda sai na samu natsuwa da kwanciyar hankalin dana fuskanci al'amurana na dai san kawai na koyi yin addu'a. Sai dai kuma tawakkalin da sanin da nayi cewar babu mai yi ko hanawa sai Ubangiji bai hana zuciyata kuntata ba a dalilin aure nake so auren kawai nake so, SO nake in ganni nima a zaune a nawa dakin ina zaune ina aurena ga Asabe tunda ta yi aurenta tana dakinta ban sake ganinta ba, kullum kuma sai uwarta ta yada magana a tsakar gida ta ce, yin aure ai rufin asiri ne Asabe asirinta ya rufu tana can dakinta cikin ntin asiri, ubangiji ya sanwaka ace yar mutum tayi ta galantoyi a gaban shi, yana kallonta kowa ya zo ya yi kamar zai aureta in ya taya ta sallama yaga araha sai kawai ya yi dani ya tafi. Tin, ta ja tsaki fa ci gaba da harkokinta. Cikin zuciyata dai na kan yi mamakin al'amarinta saboda a farkon abinda ya faru da Asabe na dauka zata fita banyar irin wadannan abubuwan sai ya zamo ko a jikinta ba ta ma tuna nata sai dai na wani dama bai karasa natan lalacewa ba. Ana cikin haka watan azumin ramadan ya iso sayaiya sosai Mansur ya yi min, ina zaune a dakina ina. buda baki mun kai azumi na biyu ina jin baba Lantana tana cewa babana wai ita din ai rabon wahala ne ya se ta aurenshi in banda haka ai shima ya san irin zaurawan da tayi, cikin zuciyata na ce ob oh kowa da irin yanda babu take zuwa mishi, watni ta kara mishi natsuwa wani kuma ta yis anadin wargajcwarshi, wata mai daraja irin' na azumi bai sa ta dan rusunawa al' amiaranta ba. Isiyaku ya yi sallama a kofar dakima ya shigo, anti ina wuni? An sha ruwa lafiya? Na amsa gaisuwar tashi ina mai kallonshi. Ya yi fes da shi ya yi kyau kamar in tambayeshi ka samu wani abin yi ne Isiyaku, sai na yi maza na fasa a dalilin ba wani shiri muke yi ba a yanzu saboda gaba daya al'amuranshi na Mubarak ne. Ya karkata ya zaro envelop daga aljihun shi ya ajiye a gefena, wai gashi in kawo miki. Da sauri na ce mishi, Isiyaku ashe ban ce maka kar ka sake karbo wani abu daga wurin mutumin nan ka kawo min ba? To dauki maza-naza ka tafi mishi da shi ka kuma gaya nishi inji ni na ce ya fita hanyata ya daina shiga harkokina in bai sani ba ko bai gane ba to bari ni da kaina in gaya mishi na tsaneshi, na tsani al'amuranshi, na kuma tsani duk wani abinda ya shafe shi, in ya kuskura ya sake aikoka da wani abu wurina to zan karbi abin in aikawa matarshi don tasan yanda zatayi da shi, ya daina kula al'amarin. Wani irin lalataccen kallo Isiyaku ya yi min da ya yi dalilin da nan take na warware hannu na sheka mishi mari mai kyau a kumatunshi har sau biyu, ina wasa da kai ne da zaka yi min irin wannan kallon? Bai cc min komai ba sa hannu ya yi ya dauki envelop in ya sa kai ya fita ya bar gidan, ya barni ina huci da tunanin haka zan rinka yi mishi duk lokacin da ya kawo min wani sako tunda nace msihi ya daina yaki. Washegari mun taso daga wurin tafsir nufina in taff gidan yaya Dija don in yi mata barka da shiga tamadan mai albarka sai kawai naga Mubarak ya yi fakin din motarshi kusa da hanyar da muke wucewa