← Book details Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 25

Sashe 6

Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanka kuma sun san mugun iri aka rage shiga dakin ka grni yanzu in ba nuna maka kai din lalataccen tsoho bane matsiyaci. Cikin duk zagin da baba Lantaria tayi msihi Da lura babu abinda yafi tsaya mishi a rai irin cwar da tayi mishi lalataccen tsoho don abinda yafi nanatawa kenan, ni ne lalataccen tsohon? Wato ni ne tsohon kuma ma lalatacce? Yanzu nan ni tsoho ne? Tayi amza ta ce na banza ma kuwa. Ganin da yayi ta fara yi mishi cin mutunci irin wanda bai zata ba ya sa shi hamzarin fara kudundumarta yana rantse ranste saukin abin ma shi ne yana jin tsoron daga murya don gani yake tamkar in yaran unguwa suka gane shi ne zasu shigo su sameshi anan din sa karasa aikin da suka fara, amma duk da haka sai da suka kacame suka haura sama suka sauko sai kuma na ji su suna daidaitawa a kan yanda zasu y1 su warware lamarin a tsakaninsu ba tare da wasu sun ji maganar ba da kanshi ya ce ya yi mata ragin jaka biyu ta nemi biyar ta ajiye mishi amma babu sauki a haka don kar ta ga ya yi mata sassauci ta dauka ko tsoro ne yana dai so ne kawai su rabu lafiya saboda darajar tsohuwar sanaiya ba a san inda za a sake haduwa ba. Kai kam bana fita in sake haduwa da kai a ko ina har abada kuma. Ya ce to ai shi kenan ni kam ai duk mutumin da na sani bana yardamu yi rabuwar banza ni dea shi don ban san abin da gobe azta haifar ba a tsakaninmu na tafi zan dawo bayan wkana. bakwai ina fata in zo in samu kudina a ajiye. Bai jira amsar ta ba ya sa hannu ya gyara rawaninshi ya sa kai ya fita ya bar gidan. Yana fita daga gidan yanayin baba Lantana ya sake canzawa kana ganinta zaka gane ta tsunduma cikin wani irin al'amari da ita kadai ta san abinda take ji maimakon ta ja bikinta ta yi shiru ko don ta huta gajiyar cacar bakin da sukayi tayi dana Nalmi sai kuma ta shiga kurme kurmcn asahar da isine tsine wanda yawanci ni take yiwa. Wannan tsinannen aure da me ya yi kama? Haka kawai ni banci nanin ba nanin zata ci ni, jalka biyar? To jaka biyar ina na ganta/ ta sake rushewa da wani sabon kukan. Watakila Sallau ya gaji ne da ji ko ganin abinda ke taf aruwa ya sa shi buda bakinshi ya ce mata to wannan abin duka baba ai ke ika jawa kanki in ba haka ba yaushe ake haka ba fa ke kika haifi yarinyar nan ba da ya ce ki bashi ita ai sai ki gaya mishi ba taki bace, amma ba ki yi haka ba sai kika je kina ci mishi kudinshi kina shirya yanda za a yi a bashi ita ba tare da kin nemi hadin kan ta ba, ita gaskiya ai guda daya ce daga kinta kuma ance sai 6ata, mai kwadayi kuma kowa ya san yana tare da wulakanci yanzu wannan jaka biyar din.... Ban ji karshen zancen ba sai ca ji saukas mari mai karfi kau, bai sake cewa koami ba haka nan itama. Washegari da safe babana ya yi shiri zai fita kasuwar timatirinshi nima na yi maza ne zo na tareshi da abin karyawar shi dana shirya misali wanda kunu ne kawai sai yan kosan da basu da wani yawa a dalilin ina tattalin kudin da ke wurin nawa saboda sun kusa karewa ban kuma hango wata hanya ta zuwan wasu ba sai dai addu'a kawai da nake tayi na neman rufin asiri wurin Ubangiji. Yaya nake ganinka wani iri hak baba? Nayi mishi tambayar saboda yanayin dana gani a tare da shi. Jikin nawa ne bana jin dadinshi bani da keri ina kuma ganin wasu abubuwa kamar 'ya'yan sama suka yi min yawo a idona. Ya'y,an rana suna yawo baba be jinin ne yah au ba? Shi ne ba zaka gaya min ba zaika kama ita a haka? Na soma yi mishi kuka sosai, a'a to menene in na fi tan'? Na kalleshi kafin na ce mishi to baba amma in kaje kasuwa kaje ka fadi fa? Ai ka bar fitar kawai ka shiga daki ka yi kwanciyarka in kaji sauki gobe si ka je. Bai yi magana ba na dauke kwandon tumatirin nashi naje na adana, ya yi min magana a hankali, to in na kwanta me za a ci a gidan ne'? Tana daga daki tayi maza, yauwa gara dai kai da kanka ka yi mata wannan tambayar ta baka amsar. Nayi kaar ban jita ba-na ce, to in babu abinci a gida baba sai kaje kana jiri a cikin m utnae kana faduwva suna kwasokasuna kawoka gida? Lafiyar ka bata fiye mana komai ba? Na soma uke, saboda yawan ciwon nashi yana daga min hankali, loakcin da kake da shiai Ciyar da wanda ya kamaka dama wanda bai kamaka ba yanzu kuwa da baka da shi sai kowa ya yi hakuri wanda ba zai yi ba kuma ya san abinda yake ciki. Ke na ce ke za ki zage ni ne? Na ce ba zan zage ki ba amma kuma ba zan barki ki tura min uba cikin halaka ba ina kallo shekara da shekaru ya yi yana kawowa don yanzu bai kawo ba kuma babu mai takura mishi, jeka ka kwanta kaji baba? Tayi maza ta ce, to ba dai dakina ba don ban ga yanda za a yi namiji ya kwanta mia a gado zankwankwan ba don takamar zuciyarshi ta mutu. Na s hannu na bude dakin Sallau ya shiga, kwanta kan shimfidar shi, cikin raina na tabbatar da ma can dole ce kawai zata fitar da shi amma ba dadi yake ji ba. Yana kwanciya na sake daukan kwano naje na sayo waina da miya na kawo mishi yaci ya koshi har ya rage sannan na kawo magani na bashi kamar yanda likita ya gaya min in tafiyarshi kalau ya sha sau daya in da alamar motsawar jiki ya sha sau biyu kafin mnu zo ganinshi, ya kurkure baki ya gyara ya kwanta nima na dawo dakina a cinye masar da ya ragen na wanke kwanon na kife kafin naci gaba da harkokina. Ina dakina a kwance ina sauraron farkawar babana sai na jiwo baba Lantana tana kiran Sallau da sabe wai suje su karfbi abincisu ta gama girki na tashi naje na dauki kwano na kai mata a zubawa babana a nan in kai mishi nashi. Wani irin lalataccen kallo tayi min kafin ta ce min yana daga kwancen ne zan rinka yin girki ina bashi yana kalmasa baki yana lamushewa? Ba ya ce bashi da lafiya ba mai ciwo yana cin abinci ne? Na zuba mata ido cikin tsananin mamakin kalaman nata kafin ince mata komai sai ta ci gaba ai ba nice zan ciyar miki da shi ba ban yi miki wannan alkawarin ba duk ran da kika sashi ya kwanta a gida yaki zuwa kasuwa toni kuma babu shi a abinci na kin ganima don ki kara sanin banyi dashi ba kin ga barkono ga farin magi ga gishiri duk a ciki na zuba in kuma ke ce za ki fake da shi ki ci to banyi niya ba ni ba baiwarki ba ce in kin kallem kuma za ki gane ni ba matar da za a mayar baiwa ba ce. Ban san yanda akayi ba naji bakina ya kama ce mata, to me kike da shi da za a ce ki ciyar da baba? Nace mai ciyar da miji in ya rasa ai babbar mata ce wacce ta san rama alheri da alheri ba mai ci ta goge baki ba saboda butulci. Ina fadin hakan na ga Asabe ta fito daga dakinmu da gudu tana tambayata zaki zage ta ne? Tun kan in amsa baba Lantana ta soma kuka tana fadin to zagi kam na nawa ai ta riga ta zageni. Kan in san menene abin yi tuni har Asabe ta rufeni da duka tana tambayata wannan wane irin raini ne a gabana za ki zage ta. Sanin da baba Lantana tayi na kullum mukayi fadan dambe tsakanina da Asabe ita ke kwarata ya sa wucewa tas higa dakinta ta barmu muna danben. Danbe mai tsanani muka fara yi sai dai ba a je ko ina ba sai ga shi na sunkuceta na fyadata da kasa a gigice ta kurma ihu mai tsanani wanda ya yi dalilin fitowar baba Lantana cikin sauri da kyar ta iya banbareni a kan Asaben tana rabamu ta nufi kan Sallau ta wankeshi da mari, gigitaccen mari tambayarshi kana kallo aka yi hakan ina amfanin zamanka a wurin? Ya ce uhun baba kenan kema ba kina kallo aka fara ba kika wucekika tafi? Ni na daina irin wannan abin na daina shigarwa kowa fada ni dukan su daya ne a wurina dukansu yan uwana ne in banda rashin kunyar tsiya meke hadani da Asabe da zanje ina tayata fadan rashin gaskiya. Tayi ta zage-zage da addu'o'in da ta ga zata iya yi mishi. Ina daki ina jinta tana cewa Asabe ke dama baki shirya fadan ba kika zo kika rarumeta? To dame wannan abinda kikayi yayi kama ai in ba sake danben nan aka yi ki ka yi mata dukan tsiya ba to raini kawai kika kara jawa -kanki a tsakaninku da can da kike dukanta ma yaya kika kare da wulakancinta balle yanzu da ta jibgeki ta yi miki irin wannan kayarwar? Lalle ne na gaya miki daga nan zuwa gobe ki san abinda kike ciki da ita. Duk da na ji maganganun baba Lantana banyi nufin sake yin wani fadan da Asabe ba don nima na fi ganin tsananin sa'a ce ta sani kada ita, amma da gari ya waye da safe naje na sayowa babana abin karyawa zan wuce ta ta sa hannu ta kabe min shi ya kife a kasa na daga ido na kalleta cikin salati mai karfi naji ta ce min, wai rama abinda nayi mata jiya tayi inji in da dadi ai gurin danben da na jata da shi ne na yi dalilin kifewar abincin ta
Chapter 6 · 0% Book details