Sashe 7
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai kawai na ji tsoron ya gushemin ban tsaya tambayarta yaushe aka yi hakan ba sai na sunkuya na kwashe abinda zan iya kwashewa naje na ajiyewa kaina na sake daukan wani kwanon naje na sayo wa babana wani na kawo mishi sai da naji ya gaya ci na bashi maganinshi ya sha sannan na fito na shigo dakinmu na kama diro da kayan Asabe ina yin watsi da su a waje ina fadin in baki rama abinda nayi miki ta hanyar wulakanta abincin da ubana zai ci ba ai ba zan kara gane ke baki da uban ba Asabe wanda ya san darajar ubanshi ai zai san na uban wani don haka yau za ki bar min gidan nawa uban tunda ya rufa mi1k asiri baki gane haan ab. Da gudu ta baro wurin baba Lantana da suke tare ta 20 zata rarume ni nayi maza na juya kanta muka rincabe da danbe ba a je ko ina ba yauma na raruma Asabe na dagata sama na fyadata da kasa. Baba Lantana tana ganin haka ta zabura da gudu ta dauko itace wai zata bugamin tana fadin na gaji da danben rashin da kike yi min a gida don haka yau za ku gamu da ni za ku ji a jikinku kum ta fara nufowa da itacen nata nayi maza na kamashi na rike na kalleta cikin natsuwa na ce mata babu sauran duka a tsakanina da ke wanda kikayi min a baya ya isa, na sakar mata itacen ya fadi kasa. Ta zabura ta nufi dakin da babana yake kwance tana fadin, ina malam din yake kana jin abinda yake faruwa amma kayi gum. da bakinka kamar. na yi maza na katseta ta hanayr gaya mata cewar ya isa haka kar ki sake zaginshi a gabana kar kumaki nemi ki daga mishi hankali. In nayi hakan me zaki yi? Za ki buge ni ne? Ban ce mata komai ba na wuce na nufi dakinmu. Sallau ya ce uhun baba kenan ai ba ki yarda ba ne da kin yarda....kan ya karasa ta sunkuci itacen da tazo da shi din ta shiga rafka mishi tare da fadin zo ka bar gidan nan zo ka tafi. Ai babu inda zanje baba in dai ba baba da kanshi ne ya koren ba ban taba samun inda na zauna lokaci mai tsawo a rayuwata ba sai da na zo hannunshi in har kuwa ki na so in atfi to ki kwatantamin inda zan samu dangin ubana tunda kin ce wai ya mutu su kam in kika nunamin su to ba zan sake zuwa inda kike ba sai don gaisuwa amma haka kawai ba za ki kora ni in shiga duniya ba. Na fito daga wanka na kalli A sabe na tabbatar jikinta yayi matukar sanyi kan abinda ya faru tsakanina da ita jiya da yau nace mata haka a yanda kike na fama da abinda kike fama da shi kice zaki buge ni ina budurwa gal a leda? Ai ke ma kin san Karya kike yi ubana ai ya rufa muku asiri dukan ku. Daga ita har baba Lantanan babu wacec ta tanka min iyaka dai na ganta tayi wanka ta shirya ta fita ta bar gidan ta tafi, nima nas hirya na nufi gidan yaya Dija na gaya mata halin da jikin babanmu ke ciki sai dai ban zauna ba na dawo gida. Ina shigowa na samu baba Lantana tana rabon abinci nayi maza na kwaso kwanuka guda biyu ance mata ga nawa ga na babana, tayi kamar ba zata zuba ba ban san tunanin da tayi ba sai kuma naga ta dan minmindira mana a zuciyata nace oho na dauka na tafi na kaiwa babana ya ci ya rage sannan naci, ban wani dade da dawowa ba sai ga yaya Dija ta iso babana ya yi ta fada kan zuwan da nayi na gaya mata. Ta ce to baba za ka yi ta ciwo ne ban sani ba? Ya ce to wannan ciwo da ya riga ya zama jiki ai ba kullum ya tashi ne za a je a fada ba tunda dai ikitama ya riga ya yi bayanin shi cewar ba a warkewa shi abokin tafiya ne, nayi maza na ce a'a baba ba fa haka ake nufi ba ai kca da hanyar tafiyar shi bai kuma zama dole don kana da shi a ce shi ne abokin tafiya ba ai ana jin saukin shi. Ya ce uhun fata dai ai bai wuce na rokon ubangiji ya bamu sa'a ba rmuka ce amin. Ta gima abinda zata yi ta fita zata tafi na bita ina yi mata rakiya ina bata labarin abin da ya faru tsakanina da su Asabe da uwarta sai dai babu alamar natsuwart tana tare da ita saboda yanda na ga tana ta faman har dewa har tana buga tuntube. Yanzu nan har yanzu wadannan mayun yaran basu dain aw adannan wakusn naSu na sharri ba? Na ce mata ch, tyo amma shi ne kike fita? Na yi murmush na ce to vaya zanyi? Ai ya zama min dole in fi ta ta ce haka ze hausawa suka ce wai watan kwaram daya ne in ya mutu sai na wnai ya kama amma mu namu watan kwaran din bai zamo guda daya tunda yau waien kwane sittin ne har da bakwai har yanzu bai mutu ba, bance mata komai ba shiru kawai nayi har ta gama maganganunta muka yi sallama na juyo gida. Da daddare ina zaune a dakina ni kadai saboda tunda Asabe ta fita ta bar gida bata sake dawowa ba shirin tafiyarmu asibiti nake yi gobe saboda umarnin da yaya Dija ta bani kenan ta kuma kawo mana kudin zuwa asibiti. Ina cikin kammala abubuwan tunda nasan sai munyi sammako sosai ne zamu iya ganin likitan a kan lokaci sai ga Sallau ya daga labulen kofar dakin tare da ya min magana a hankali, sannu Mero. Na daga kai na kalleshi, yauwa sannu Sallau, ya ya mai jikin? Na ce mishi da sauki. Ya sake rage muryar tashi ta kara yin kasa kafin ya ce min da wata shawara nazo da ita ban sani ba ko zata samu karbuwa a wurinki. Na ce to shigo m na in ji shawarar, cikin natsuwa ya shigo ya nemi wuri ya tsuguna kamar wani mai shirin biyan bukata. Da ka zauna ai kamar zai fi yi maka dadi, a'a babu damuwa, na ce to shi kenan me ya faru? Ya danyi kame-kame kadan kafin ya iya fitowwa sosai ya yi min bayanin rumfarn an ce ta baba da kullum in bashi da lafiya ake rufeta babu kowa tumatirin ciki dama duk wani abinda ake da shi su yi ta lalacewa tunda ba masu jirar zaman bane shi ne nace ko zan rinka bude ta ne ina zama a ciki? Sanin da nayi da gaskiyar magana Sallau din ya fada na kuma san in ma ban barshi ya bude rufmar ya zauna ya dan taba abinda ya taba na cikina ba to duk ranar da aka budeta za a kwashe komai ne a zubar tunda za su gama lalacewa to da a yi irin wannan asarar kuwa gara ko ba zai baiwa baban koami ba ya bude ya sayar, nasan shi zai dan samu wani abu don haka sai na kalleshi na ce mishi, to ai hakan yana da kyau Sallau gobe da safe sai kaje ka bude tunda shi baba goben zaije ganin likita, ya ce to Ubangiji ya sa mu gani lafiya, na ce mishi amin. Washegari da yamma mun dawo daga asibiti bayan sallar La'asar a dlailin dogon layin da muka tarar daga nesa na hango Sallau a cikin rumfar baba yana tashe da yan timatirin da suka saura muka wuto shi muka shiga gida sai kusan magariba ya dawo ina kallonshi bance mishi komai ba baya ga gaisuwar da muka yiwa juna sai da ya tabbatar baba Lantana ta shiga dakinta ta kwanta sannan ya turo kofata ya shigo a hankali gaba daya cinikin da ya yi ya zube min a gabi.na na zuba ido ina kallo nace a'a ciniki mai kyau aka yi ne haka Sallau? Ya ce eh an dan taba kadan, to madalla na fada ina mai sauraron abyaninshi sai da ya gama na ce mishi, to su wadannan kudin sai ka rikesu kawai a wurinka ba ka ce kayan bai karasa karewa ba? Ya ce e, na ce to daga nan zuwa biiba ya gama jin sauki sai mu ga abinda za a yi, ya ce min to sai da safc ya fita. Kwana uku bayan nan baba ya fara bude rumfarshi bayan ya saro wani sabon timatirin a dalilin saukin da ya samu ban san yanda akayi ba sai na ganshi tare da Sallau suna zaune a rumfar tare shi yana can ciki a zaune Sallau yana salalmar masu zuwa saye, ni ma kasuwar zai tafi sai ya tasashi a gaba su tafi tare. Rannan ina kwance a kan dan gadona na bono da hantsi bayan na yi wanka na shafa man basilin din babana saboda gaba daya kayan shafana sun kare bani da komai in banda man wanke baki. Ina cikin tunanin halin da nake ciki ne sai kawai na ji an kwala sallama, ina jin sallamar na gane wanda ya yi ta nan take na shiga lissafin rabonshi da gidan yau zuciyata ta tunamin kwanaki tara ne cif. Sallama dai sallama dai, na fa iso na kuma san ana jina yauwa ita rana ai bata karya sai dai ko uwar diya ta ji kunya, to ni don kar a ji kunyar ma sai na mutunta na kara kwanaki har biyu kan alkawarin da aka yi min din, ga zatona za a biyoni da su har rumfata a mutunce to da ban gani ba kuwa gani na taho karbar halali na. Baba Lantana ta fito daga dakinta dankwalinta a hannu fuskarta kuma a daure abinda na tabbatar shi ne bata yi azton zuwan nashi ba a yau don kuwa jiya da shekaranjiya da ta yi tsammanin zuwan nashi tun sassafe take barin gidan bata dawowa sai cikin dare. Ah naso karbar halalina ya yi maganar cikin wani irin yanayi yana mai kawar da ido daga gareta, watakila