Sashe 12
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ni gida, tayi ta tambayata menene ban ce mata zan kwana biyu ba? Nace mata eh amma ai na fasa saboda zan bar baba shi kadai a gida. Ta gallamin harara, baba shi kadai m atarshi fa? An ce miki zaki yi ta zaman gida ne saboda baba? Kema zaki yi aurenki. Nayi dariya kawai na kama hanya na tafi. A gida ina zaune ne kawai bana komai bana kuma zuwa ko ina, ba makarantarboko babu ta allo, bana kuma fita ko ina ko daidai al'amura sun dan lafa na wakoki da rashe-rashen mutuncin da akayi tayi min a baya, na dan samu sauki na dan samu saukin ciwon da zuciyata take yi min a kan Mubarak saboda na daina yarda ina zama in bata lokaci wajan tunanin al'amufanshi, ina kuma kiyaye duk wani abin da zai hadani da shi ko da kuwa hango ni daga nesa tunda asan har yanzu ban samo maganin faduwar gaban da nake fama da shi ba a duk lokacin da' na hangoshi ko na ji maganarshi. A cikin gida dai ni da su baba Lantana muna cikin wani hali ga babu ga kuma rashin dadin zama komai a tsaye yake cak, bani da komai n abin amfani ba ni kuma da ko kwandala, rabon da in yi rashin irin wannan har na manta. Watakila tun ban isa komai ba tunda in ma ban samu an yi min a gida ba to dai bana rasawa zan samu wurin Mubarak ko Umamnshi, to yanzu babu su baban nawa kuma ba shi da shi, ta lafiyar shi ma ake yi bata maganar runfa ba don ma anyi sa'a Sallau yana matukar taimakawa a kan bude rumfar babana yana cikin wani hali na rasa karfi mai yawa a tare da shi, a hakan kumna wai baba Lantana bata tausaya mishi a bata dai a bata kawai ta sani ko da kuwa babu abinda take so a baka din kusan kullum zaka sameshi ne cikin jiri ko ciwon kai, amma hakan baya hanata zama tayi ta gaya mishi bakaken maganganu ni kam ma sai nake ganin tamkar karbem ata fili da Alhaji Nalami yayi ba kairamin kara mata son kudi da neman tashin hankali yayi ba. Rannan ina jinta ita da Sallau da ya dawo daga runfa in da ya danyi aiki, bani kudin nan duka nace maka ka bani su, a'a baba in na baki su dukan gobe fa? A ci yau a ci gobe ai shine cin rana daya, kumburin ciki ne. Nace maka ka bani su, ina ce dai rumfar bata gidanku ba ce? Cikin natsuwa ya ce mata, eh baba bata gidanmu bace amma shi mai rumfar ai bai nuna min hakan ba don haka zan tattala mishi abinda yake ciki ko na samu nima in koyi sana'ar tunda dai ke baki kaini makaranta ba baki kai ni wajen koyon sana'a ba. Ina daga kwance ina jinsu ko motsawa banyi ba, cikin zuciyata na co kunfi kusa in kuka ga dama kuc inye su duka a yanzu. Ganewar da nayi Sallau da iyakacin gaskiyarshi yake mu' amala da baba na yasa nima ko kadan bana sa mishi ido kan cinikin da yake yi komai yace min kuma sai ince mishi to, bana dai sake mishi sosai don haka sai muka koma m u'amala ta matunci kawai da ganin girmanjuna, a wannan lokacin babu abinda yafi tsayamin a ai irin in kwanta da daddare in tuna gobe da safe bani da kudin da zan sayawa babana abin karyawa gashi a yanzu baba Lantana sai tayi kwana kwanaki bata yi girki ba, wai abinda ake batan baya isa a yi girki, na kuma san har da daina yarda da ayi girki aci ni a hanani da na yi ya kara sata daina yin girkin. Kan hak yasa naje na samu Sallau a rumfar baba na ce' mishi Sallau. Yayi m aza ya taso, anti Mero ai da kin jirani a gida ma zan zo. Nace e babu damuwa so nake mu yi magana. Ya ce to, nayi mishi bayanin da ya kawo kullum in kayi ciniki ka rinka cire kudin da zaka rinka saro kayan gobe abinda ya saura ka kasashi biyar kai daya baba daya baba Lantana daya ni daya, dayan kuwa a rinka sakashi cikin bankin karfe dake cikin rumfar nan, saboda bacin rana, ya ce min to. Yana dawowa kuwa da daddare ya zo ya yi min bayanin abin da aka yi da yanda ya yi kasafinsu. Yaya Dija tana iyakacin kokarinta a kan mu sai dai kuma ita din mata ce da bata iya sana'ar komai ba duk wani abinda kaga tana yi in dai na kudi ne to daga aljihun mijinta ya fito ko kuma daga abinda ta iya tattalawa na canjin cefanenta don haka sai na kudurawa kaina ba zan taba zama bani da abin yi ba, ba zan zauna bana sana'a ba, ba zan iya zama sai an bani ba, zan nemi kudi ko don in yi hidimata da ta babana ba tare dan a tsaya jiran an bani ba sai dai a sana'ar ban san wacce zan yi ba. An wayi gari yau tun asuba zuciyata take ta kai kawo kan al'amarin Asabe wacce na lura tayi matukar canzawa duk wani abin da za ta yi ta kan yi shi ne ba a yanayin da ta saba ba, hatta zamanta da tashinta amma wai har yanzu baba Lantana tana kallonta bata gane abinda take ciki ba ko kuma ta gan tayi shiru ne kawai oho. Tsawon lokaci ina wannan tunanin kafin na yi maza na kawar da wannan tunanin na koma kan nawa al'amarins aboda ganewar da nayi cewar in na tsaya kan nawa mas'alolin ma kawai sun isheni ba sai naje ina shiga harkar da ba tawa ba ce, don haka na koma lissafin tawa damuwar gaba daya kayan sakawar baba sun kare sunyi datti bani da ko sabulun da zanyi mishi wanki, nmaganin da yake sha yana gab da karewa babu kudin sayen wani ga zuwa asibitin shima ya zo da dai ace so shine samu to da na samu wani abinda na rinkayi ina samuz ko da kwaho kwabo ne don in rinka aiwatar.mana da abubuwanmu ba komai ya taso sai naje na gayawa yaya Dija ba. Gari ya waye da safe nayi abubuwan da na saba yi mana ni da babana na yau da gobe na kai mishi ruwan wanka na dawo kenan sai ga yaro dan makwabta ya shigo, anti Mero wai inji Mansur wai ki Na daga ido na kalli yaron yanda ya ambaci sunan Mansur din gatsu bai yi min dadi ba kamar in yi mishi magana sai na fasa na kame bakina nayi shiru cikin zuciyata dai na tabbatarwa kaina da cewar gimamai na gaba yana da dadi. Gyalena na dauka na yafe jikina na kama hanyar fita zuciya'a sai faman harbawa take yi don rabon a kirani inje har na mance da lissafin. Yana tsaye ne cikin zauren gidanmu kanshin shi ya gauraye ko ina. Kunyarshi ta yi matukar kamani na kasa sakewa a gabanshi saboda sanin da nayi ya ji komai yana da labarin duk kan abubuwan da aka yi tayi har wakokin da nayi ta fama da su duk nsan ya jisu, amma hakan bai hanashi zuwa wurin yaya Dija ba gashi kuma yau a gabana, me yake nufi? Yana nufin har yanzu yana kan bakanshi bai fasa aurena ba kamar yanda yaya Dija ta gaya min kome? Kan in kai karshen tunanin nawa sai naj1 ya ce min, ran yan mata ya dade ina kwana? A kidime kwarai na nemi wuri na tsuguna, yan mata yake k irana bayan tun ba yanzu ba na saba jin mutnae masu zargi suna fadin ai ni din tun ba yau ba na salwantar da budurcin nawa, yana ganin an tsuguna shima ya nemi wuri ya tayani tsugunawa. A tsarge kwarai na soma amsa mishi gaisuwar tashi tun bayan faruwar al'amuran da suka farun yau ne ranar farko da ni da Mansur uka hadu a wuri daya. Ya ya Dai Maryam? Yaya jikin baba? Na amsa mishi da sauki, 'yan maanganu kadan mukayi hirar tamu ba ta yi wani nisa ba watakila don bamu saki jiki ba tamkar dai ace muna jin kunyar juna. Takardar naira ashrin guda biyu ya. miko min wato naira arba' in ko ince fam ashirin, hannu biyu na saka na karba tare da yi mishi godiya, bai tsaya jin wata magana ba ya ce min, zan tafi sai na dan huta na fito za ki ganni, na ce mishi to. Yana tafiya na dauki takardar naira ashirin guda daya na nufi shago don yi mana sayaiya, babu wani abin da ban saya ba na kayaiyakin amfani har man shafawa da na dade bani da shi na saya, sai dai maimakon 10-0-6 da Mubarak ya koya min shafawa sai na koma man shafawa na kamfanin shield don dai in samu in kara fitar da duk wani tunanin shi daga cikin zuciyata. Na shigo gida na kama wankin babana cikin kuzari na gama nayi nawa nayi mana guga na adana mana kayanmu na gama ba tare da gajiyar aikin ta dameni ba can cikin zuciyata nace kai babu tana cikin mas'alolin da ke addabar rayuwar dan adam matukar dai shi din mai lafiya ne. Kudin da na samu wurin Mansir sai suka wattsakar da ni na samu kuzari mai yawa a tare da ni, nayi duk wani abinda ya dace, ranar asibitin babana ya zo mukaje muka daow na saya mishi magungunan da aka rubuta ba tare da na jira ko gayawa yaya Dija ba, sai da na gama komai ne sannan naje na gaya mata yanda aka yi. Tun daga wannan lokacin da Mansur ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Ghana sai gidanmu ya zamo nan ne wurinshi sai dai in baya nan, tun ina jin kunya ina nonnokewa saboda al'amuran da na san ya sani ya ji game da ni har na wattsake muka shiga harkar soyaiyar na samu natsuwa da kwanciyar hankalin da na dadeb an samu ba, na murje na yi kyau saboda nayi sa'a shima man shafawar shield din ya karbi fata ta. Yaran unguwa sun yi matukar fita harkar yi