← Book details Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 25

Sashe 21

Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haka na yi maza na shige cikin gidanmu na barshi a nan wurin yana tsaye. Ko badan ban i haushin hana Mubarak aurena da babana yayi ba saboda tuni ya riga ya fita min a rai bana kallonshi inji zuciyata ta rayamin abubuwan da ta saba raya mina game da shi a baya sai dai in ganshi in ji faduwar gaba ko in ganshi in ji haushi da takaicin shi sun kamani. A wannan lokacin ne kuma baba Lantana ta fito da wani irin salo a gidanmu duk wani wanda ya zo wurinta in suna hira bata kai karshen hirar sai ka ita tana gaya mishic ewar ita wannan zama da take yi ma ai ya kusa ya zama haramtaccen zarna, abokin hirar ta ta ya ce, haramtaccen zama kuma, Lantana sai ta ce eh to haramtacce mana tunda abinda ake yiwa zaman yayi karanci ace niji kana kallonshi yana kallonka shimfidarku daya amma sai ya sahfe kwana da kwanaki babu komai, babu wani motsi a can babu a tukubya ma babu ana yin zaman haka ne ai ni yanzu kiris nake jira don ma dai kawai kar ka tafi ne ya zama ka tafi ka bar ladanka. Haba Lantana haba Lantana yanzu ke a yanda kike din nan sai kin yi korafi kan irin wadannan al'amuran, m utumin da ko lafiya bata isheshi ba, tace a'a ni ban wuce ba sannan tun a can baya ma da yake da lafiyar me aka yi ne da za a ce yanzu in hakan ta faru kar in yi magana? Yaya Dija na baiwa labarin kalaman nata ita ce ta faiyacemin abinda take nufi, kasar kullum sai ta tasa babana a gaba tana yi mishi hirar gidan mijinta na baya, haushi da takaici ya yi ta kama ni na yanda sau daya babana ya kasa cewa ya sauwake mata nashi auren taje ta koma gidan mijin nata na bayan, yawan fadan da take sashi a gaba da yi kIsaa kulium da yi ya sani bashi shawarar dawo da kwana dakin Sallau don ya rinka samun wadataccen bacci saboda mas' alar hawan jininshi, kamar bai ji shawarar tawa ba daga baya kuma sai naga ya koma dakin. Wata gomas ha daya cif nayi ina zuwa makarantar koyon sana'a ta Markas kafin aka yayemu saboda yarda da aka yi cewar mun iya mu gomas ba biyar aka yiwa yayen aka kuma yi mana kyautar dinki saboda gamsuwar da akayi da kwarewarmu, ko kafin nan kuwa nikam na dan dau loakci ina taba dinkina a gida a kekcn da yaya Dija ta saya min don haka dana samu wannan kyautar sai kekunana suka'zama guda biyu. Naso kwarai in koma Karkas in sake shiga wani ajin daga cikin azuzuwan sana'o'in dake wurin in kara koyon wata sana'ar haikan bai yiwu ba saboda karatun da nake yi a makarantar asidini mai zurfi, karatu ne dake bukatar sadaukarwa mai yawa banda haka kuma ga lalurar babana ta yawan rashin lafiya don haka sai na hakura. Tunda aka yayena a wuTin koyon dinki na soma yin dinkin sosa a gida sai mas'alolin da suka danganci babu sia yi matukar yi min sauki bana asa na sabulun wanka ko wanki bana rasa ta yin break a makaranta wani lokaci ma nakan raka babana asibiti ne ba tare da na shedawa yaya D1ja ba balle inje ina jiran abinda zata bamu wannan-shi ne abidna yafi komai faranta min rai na. Shekaru uku ne yau tun bayan faruwar abinda ya faru tsakanina da Mubarak cikin shekarun nan kuwa nayi abubuwa masu yawa wanda kasancewata a yau ni din kwararriyar tela tace gani a fada a kuma kwaikwaya, ni din kuma gwanar girki ce saboda na koma makarantar Markas na sake shiga ajin koyon girki nau'o'inshi kuma malamaina na Markas irinsu malama Hindu da Basma wadanda mukayi matukar shakuwa a dalilin kulawar da suka nuna a kaina sunyi min taimako mai karfi wanda a daliiinshi na samu shiga exam center dake kusa da Markas din na samu rubuta jarrabawar dana samu mallakar takardar shedar gama karatun secondary indana samu credit guda hudu da pass biyu saura f9. A 6angaren da nake ganin kamar na yi nasara kenan, a daya bangaren kuwa Ina nan kamar yanda dama nake aure ya gagara babu kurna yanda banyi ba in yi shi hakan bai yiwi ba, zan iya cewa garama da da yanzu a lokacin da kuka sanni samarin sukan dan zo auren ne basa tsayawa a yi saboda wasu dalilai to a yanzu babu bani da wani wanda zan ce wannan saurayina ne. Mutanen unguwarmu tun suna nunani suna yin bayant a kaina zuciyata tana lissafi ta karyata maganar ta su har na hakura na fita harkarsu ta barsu su fadi duk abinda suka ga dama. Tun ban a kama maganar mutane irin su Yakumbo Halima da suke fadin cikin biyu dai alkwai abu daya ko dai anyi min sihiri ne ko kuma ma aljani ne ya aureni ya hanani yin aure har na soma shiga rudani ina tambayar kaina to menene mas'alata, tuni dai na daina yin kawaye don na gaji da aurar da su da akeyi ana barina a wannan lokacin in har ina da wata kawa to kekena ne da kuma dinkina sai ko kwalliyar da nakeyi don kuwa ba sai an gaya min ni da kaina na san mu'amalar da nayi da malamaina na Markas irinsu Malama Hindu da Basma ya koya mina bubuwa iri-iri da suka danganci mace kwalliya, kamewa, mutunta kai, iyaka dai har yanzu hakan baisa na samu mijin da ya tsaya ya aureni ba su ma kamar yaya Dija sukan ce min wai lokacin auren nawa ne bai zo ba sai in yi murmushi kawai in yi shiru cikin zuciyata kuwa tambayar kaina nake yi ko yaushe ne lokacin oho? Saboda a wannan lokacin har na gaji na soma tambayar kain to koma dai ni din ina cikin matan nan ne da ba a halitt musu mazan auren ba? Tun ina kin yarda in yi amfani da abubuwan da Yakumbo Halima take bani in yi amfani da su na farin jini da wai maganin sihiri da kullum take zargin wai Mubarak ne ya yi min in yi murmushi in ce mata Mubarka bai ma yarda da irin wadannan abubuwan ba Yakumbo shi fa dan boko ne ma digiri biyu ne da shi ya ma sake komawa karatunshi don neman na u yaushe zai zauna yana irin wadanann abubuwan? Sai ta ja tsaki bayan ta gallamin uban harara ta ce, ai sai ki yi dama in kana son mutum ai baka iya ganin laifnishi, ince mata ba haka bane Yakumbo ai ni yanzu bana son Mubarak abin da na sani ne kawai nake gaya miki, ta ce to baki san komai ba incem ata to na yarda. A wannan lokacin ta kaima ina zama in yi kuka ins hare bawayena tun ina yi ni kadai har ta kaima ina yi a gaban yaya Dija, menene mas'alar da ta hanani yin aure? Bani da fasali ne? Ta girgiza kai uh uh kina da shi daidai gwargwado, bani da tsabta ne? Ta sake cewa uh h kina da ita kin kuma iya kwalliya kina kuma yi iina da kamun kai da natsuwa gashi kin yi karatunki kina ma kai tunda har yanzu kina yi to amma lokacin auren bai zo ba, Maryam mijin naki ne baizo ba d on haka bani da yanda zai yi sai dai in yi ta baki hakuri in kuma kara rokon ki ki kara tsare mutuncinki komai zai wuce har kiga kina bayar da labarin al'amarin, ni dai nasan duk waenda ya yi dace da samun babbar mata mai aikairori iri-iri, in yi murmusbi ince yaya Dija kenan kenan kina dai gaya min hakan ne kawai don in ji sanyi a raina. Ita dakanta yaya Dija duk da irin wadannan kalaman sanyaya zuciyar da take yi min ta sha gaya min cewar rashin aurena ya katse mata baccinta ya gusar mata da nishadinta ya sanyata ta ji zuciyarta ta kutata don haka mu yi ta istigfari muna rokon gafarar Ubangiji, in ce mata to wataran kuma in dan zolayeta ince mata ba kince zai wuce ba? Ta yi maza ta ce, kamar yanzu kuwa in har muna raye to zamu sheda wucewarshi. Yaya Dija ya ce a wurina da ta zame min uwa ita nake kallo a matsyain uwa saboda duk abinda take yi min yi take yi da iyakacin iyawarta tana da ya'ya maza da mata amma bata hada su da ni ba, na sha jin matan gidansu suna cewa ai ita wai kanwarta ta fiye mata kowa tunda ita ita kadai ke gareta ba kuma zata sake 'yar uwa irinta ba tunda uwar da zata haifar mata wata bata nan ba wadannan kalaman ne suka sa zuciyata yarda da yaya Dija bata hadani da kowa ba a aiyukanta ne a kaina shi yas anima bana wasa da ita duk abinda tace min to k wai nake cewa bana yi mata musu. Ina zaune a dakin ina yankan kayan da nake nufin dinkawa a wannan satin wanda na ankon wani biki da za a yi ne a unguwarsu aya Dija aka kawomin ina yankan cikin natsuwa da kwanciyar hankali saboda daga ni har dakin nawa tsab muke sai kanshi muke yi, bana tunanin komai cikin raina aiki na kawai nake yi sanda Asabe tayi sallama ta shigo cikin dakin, ashe kina ciki? Nace eh Asabe ki zo ne? Ta ce min, ina kwana? Ina amsawa ina matukar jin tausayinta gaba daya t a canza ko rigar nono a wannan lokacin na ganiyar kuruciya bata iya sakawa, tsabtar ta duk ta kare kullum ka ganta gara jiya da yau ba ita ba ba 'ya'yanta kullum yanzu sai tazo gida kullum kuma da mas'alar da zaka ji tana fadi baba Lantana tayi tayi ta daina shiga dakina tana gaisheni ta ki dainawa, ban sani ba ta canza hali ne ko kuma sule biyun da nake baiwa ya'yanta in zasu tafi ne ya hanata daina wa oho? A wannan lokacin wanda. bai yiwa Asabe sani na hakika ba ba zai ganta ya ganerta ba ga karni da take yawo a ciki. Kin fito daga dakin kanwar uwar taki
Chapter 21 · 0% Book details