Sashe 22
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ne? Ban ji abinda tace ba naci gaba da aikina ina istigfari kan yawan damuwar da nake yi a kan rashin aurena, na yi imani da in yi aure irin wanda sabe tayi gara ma ina zaune a gida gaban iyayena ckin haiyacina da rufin asirina, tunda ba cewa akayi in ba a yi auren ba ba za a samu rahama ba sai dai in ba a yi aikin neman rahamar ba, ba kuma raina auren Asaben nayi ba yasa na fadi haka tunda na san darajar aure yawa ne da shi ko banyi shi ba kuma na karantashi a ganewa kawai a yanda ka'idar auren yake da bayanin shi da akayi a tsari irinw anda auren Asabe ka tafiya zai yi wuya kwarai in har ana samun ladan da ake nema din kullum a cikin korafi ake a zagi miji a zagi kishiya a gaya mata irnin tsiyar da zataje ta yiwa mijin, ni kuwa ina zaune gaban iyayena cikin rufin asiri ina addinina daidai gwargwado ina neman ilimi, ina sana'ata ina kyautatawa mahaifina gwargwadon iyawa ta, a wannan loakcin banda sutura da hidimominshi har runfa nayi: nsihi sabuwa ciki da falo, kayanshi suna can ciki shi da Sallau suna wuri daya, Salau kuma yana iyakacin kokarinshi kullum babsn ayan yi min addu'a yana samin albarka. Na karaa kallon al'amarin Asabe da aurenta wanda da ni aka so a tura cikin wannan wahalar Ubangiji ya tsarcni, kullum a cikin tashin hankali da miji ake kishiya kuma ta kamata tayi amta dukan tsiya ta kaima baba Lantana da kanta tayi damara taje har gidan Nalami wai zata ramawa Asabe dukan da matarshi ke yi mata ban san yanda akay ba sai naga tadawo kaca-kaca da kamar akwal rayuIwar addini a gidan nasu to da komai ma da sauki to babu. Daga tsakar gida na soma jiwo wata magana da ta katsemin maganar zucin da nake yi saboda an fara daga murya ana yinta sama-sama alamar rayuka sun fara hassala. To bakya cewa ya sakeki, ke wacce irin sakarya ce yaya za a ce miji ne zai auna maka hatsi abincin da ba zai isheka ba babu kudin cefane babu koami sai abinda kishiya ta baka, sannan in abincin bai isa ba sai ace. kai ne ka rasa, wannan wane inn zalinci ne, Sannan in dare yayi ya zo ya fada miki da yunwar da komai ba dama ki ki yarda da shi, ke ko irin 'yar tirjiya da yangar nan da mata ke yi a rarashesu a yi musu abinda suke so baki iya ba. Ai rufeni da duka yake yi yana ganin alamar zan yi mishi tawaye sai kawai ya tashi ya zauna ya yi ta jigbata da duka wai ladan hatsinshi da na wuni ina ci, baba Lantana tayi shiru kamar yanda Asaben' ma ta tayata yin shiru, imawa cna na ji ta ja wani mummunan tsaki da bai da dadin ji kafin daga baya ta bishi da fadin, kai Nalanni dai tsnanne ne. Shi ne nace to ko zance ya sake nin ne kawai? Da saun ta ce ys sakeki mana tun yaushe nake gaya miki hakan? Ta dan rage nurya kadan ta ce, to amma fa ba Zai yarda in abr mishi wannan yaron a can ba ya ce wai zaunana ya ke yi na barin gidan shima zai bari wannan dai ya yarda nashi ne tunda yana kama da ya'yanshi amma si wannan ai bai ga ta inda ya daukoshi ba shi ne nace ko zan kawo miki shi ne kawai in bar mishi wannan din: wahalar da nake sha tayi min yawa kajin mafa day ake bani figarsu yana bani sisi-sisi ina samun na sabulu yanzu ta hanashi bani ko kwabo wai... Ni da nake kashc da kunne in ji abinda baba Lantana zata fadi kan kawo mata dan da Asabe ta ce Za ta yi sai naji ta hassala ta daka mata tsawa, ke barni haka da wannan mugun albari naki sakarya kawa shashasha sauna mara zuciya ace mutum bai da wani aici sai na bayar da mugun labari? Ki dauko yaro ki kawo min ya zama duk tattakar da ya yi miki a banza kenan ko me? Wannan yaro ai dole ne ya girmaa gidanshi ladan sukurkutaki da ya yi ya maida ke wata yamutsattsiyar tsohuwa, tsinannan mutum kawai. Na ce oh oh ta kacame tsakanin siriki da sirika, ina zaune kan kekena ina dinkin kayan dana gama yankawa zuciyata tana tunaina al'amarina irin kokarin da baba Lantana tayi na ganin ta sa babana ya baiwa Alhaji Nalami aurena duk da tafi kowa saninshi da duk wani al'amarinshi tunda tun a loakcin ta sha gaya min cewar in dai matar Nalami tana nan a yanda ta santa ai zata yi mata magani na to gashi abin baiyo kaina ba sai ya fada a kan yarta nan take na tuna da karin amganar hausawa da ke cewa wai, mugunta fitsarin fako, in kayi sai ya dawo maka kanka. Kwalliya mai kyau nayi a ranar da na yi nufin kaiwa masu kayan kayansu, doguwar riga na sanya har Rasa ta farar atamfa da aka yiwa ratsi da kananan filawowi koraye da bulu, saman rigar na yi shi a matse yayin da na yiwa tsakiyar yankan umbrella ya sauka har Kasa, dankwalin yadin' atamfar ne a kaina na yi dauri mai kyau sosai na sanya yan kunne kanana na yafa farin gyale madaidaici a-kafadata yayin da na kawata hannayena da adon awarwarai, agogo da zobuna biyu na zinari daya kuwa na azurta da aka yava kira mai kyau na shuri takalmana silifas 1masu igiya a baya yan Italy da suka kara kawatamin kwaliyar tawa, nasa garkamemen kwado na kulle kofar dakina a dalilin gajiyar da na yi da biyan mutane atamfofinsu da suke bata don haka nama canza kofar dakin gaba dayanta. Na baro gida rike da ledar kayan dinki da kuma pos a hannuna bayan na gayawa babana inda zani, yar tafiyar da nayi ba wata mai yawa bace na ja na tsaya don tarar mashin din da zan hau. Wat ke me yasa bakya in magana ne? Sau nawa nake gaya miki in zaki fita ki daina amfani da turare ki kuma daina hawa mashin bana so. Ban kalteshi ba balle in bashi amsa iyaka dai nasan nayi mamakin ji ko ganinshi a wannan lokacin tunda nasan ya taf Legos bar kima san da dawowar tashi ba. Amma shi baba tsareki da ya yi a gida kike ta wannan zaman a gabanshi yana ganin kamar ya yi mishi daidai? Shi bai san kin kai kowane irin munzali bane, bai san kinas ha'awa ba? Ke ba za ki gaya mishi kina da mas'ala ba? A muku mukuns anyin nan kin fito za ki je ki kai akyan da kika dinkawa wasu in kina gidan aurenki mijinki zai yarda da haka? Gaskiya na gaji da ganinki a haka yanzu fa Rumasa'u ya' yanta biyu ne. Maganar ta dak zuciyata a hankali na tunawa kaina da kullum muka gamu da shi bama rab wa sai ya san yanda yayi ya sokamin abkar maganar da ta tsaya mina raina. To wai ni ina abinda ya dameka da ni ne? Kaga ni na damu da kai e? Kaga ina. daga ido ina kallcka ne balel in san abinda kake ciki? Ina dalilin da kake nema ka maida mahaifina abokin wasanka, kullum ka ganni sai ka san abinda ka fada a kanshi. Ban maidashi abokin wasa ba Mero amma gaskiya zan gaya miki yana 6ata min rai don me zai hanani ke? Don... Na yi maza na katseshi, in ya hanaka ni sai ka rinka gaya mishi magana a kan ido na wane hurumi ke gareka na yin hakan? Nace bana sonka nace ka fi ta harkata nace ina kwai wani mutumin da zance na tsana a yau to kai ne don me ba za ka yi zuciya ka fi ta hanyata ba? Ranshi ya yi amtukar 6aci da kalarman da nayi mishin, wani irin kallo ya yi min irin wanda shi kadai ya san abinda yake nufi da kallon, kina ganin kamar ba za a iya fita harkar taki bane? Kina ganin kamar in an fita harkar taki wani abu zai faru ne da kike wannan cika bakin? To ni don na fita harkar ki ma menene Maryamu? Ai ni ina da mace a gida har da ya'ya kece kike zaune ke kadai kece kike rayuwa cikin kewa da kadaici, duk sanyin da ya taso ya kare a kanki kina zaune kan kujerar dinki, ni ai da aurena sannan karya kikeyi kice bakya sona in bakya sona me ya hanaki yin aure? Fitar da wani ki aura mana ki zauna kema a dakinki ki dandani dadi da zumar dake cikin auren sakarya kawai sokuwa shashsha wacce babu halin a batawa mutum rai ya gaya mata ta tausaya mishi, sai ta ce zata bishi da bakar magana sau dubu nawa yake so in turo mishi mutane kafin ya yarda ya bani ke? Me nayi mishi a rayuwa i banda adalci. Sauri nayi na tari mashin babur na dale kai muka tafi don kar bakin ciki da dacin da nake ji a zuciyata ya sa in fara yin kuka a gabanshi. Zagin da ba a taba yi min ba yi min, yayi min gorin aure da 'ya'ya da... na kasa karasa bayanin nawa na shiga yin kuka sosai da sosai, tana ta bani hakuri, jimawa can kuma sai ta nisa ta ce, nima dai abin yana damuna ina mamakin yanda baba ya ja ya tsaya ya ki baiwa Mubarak aurenki bayan nima nayi iyakacin tunanina ban gano laifin da ya yi mishi ba to inma ya yi a yafe mishi mana, Umma ma fa kwanaki tazo gidan nan maganar kuma ce ta kawo ta na kuma san ba dadi ne ya sa ta yin hakan ba, to ya bashi ke din mana kawai a huta, zan sake zuwa wajen baba in sake rokonshi inji.. Kan ta karasa na yi mata wata irin rantsuwa mai karfi kafin na ce mata, ba zan taba aurenshi ba har abada ba zan taba aurenshi ba bana sonshi bana son shi ko da sunanshi ne a kusa da ni da in aureshi gara ma in