← Book details Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 25

Sashe 2

Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

can nesa suka yi ta auna mutane suna yi musu ruwan duwatsu, gava daya suka tarwatsa jama' a, shi dai angon nan in dai ba karyashi suka yi ba to sun turgudashi a wani wuri don da kyar muka kwaceshia hannunsu, sai faman nisa uka yake yi yana neman taimako. Assha assha namiji da neman taimako kuma babansu 1lallai fa da gaske ne abinda ake fadi akanshi cewar shi din ba namiji bane daudu yake yi. Yaya Ibrahim ya daure fuska, wane irin zancen wofi ne wannam daga nace yana ihun kiran maza su yit aimako kuma sai ki dangantashi da daudu kin san ma'anar daudu kuwa? Wuya tana da dadi ne? In ka ji fa kayi ihun kuma taimamko ai ba laifi bane. Tace haka ne, daidai lokacin da ya mike ya nufi waje don tafiya wajen harkokinshi. Daga ni har yaya Dija babu wanda ya iya cewa wani komai bayan fitar tashi kallon juna kawai muka yi cikin wani irin yanayi da ba zan iya kwatantawa ba, da kyar na iya bude bakina na ce mata wato dai duk wani al'amari yaya Dija na ubangiji ne. Tayi maza ta ce ai shi ne madogara ta dindindin in har ka d gara da shi din kuma to baka tabewa. Duk da wannan labari mai dadi da yaya Ibrahim ya zo.da shi saukin damuwa kawai muka samu amma ba wai mun fita daga cikinta bane muna te addu'a tare da sauraron abinda zai biyo bayan abinda aka yi. Ina nan zaune a gidan yaya Dija har adadin kwanaki hudu jinin jikina har ya fara dawowa na soma farfadowa daga mummunar gigitar danayi sai ga YakumboHalima ta zo gidan don dama ta san ina nan saboda aiken da yaya Dija tayi na a gaya mata saboda ta samu kwanciyar hankali. Muna zaune g abanta muna hira bayan ta gama ian abincin da na kawo mata tana kara bam albarin abubuwan da suka faru ko ince suke faruwa sai naji ta ce, shi kam malam Habu ai ya shiga mas'ala koma ince ya shiga uku ina amfanin ace namiji baida katabus komai sai yanda akayi da shi. Da sauri yaya Dija ta ce Yakumbo bafa haka kawai bane da abinda tayi mishi. Ke matsa can ni ki bani wuri a kanshi aka fara yiwa maza asiri? Ai shi asiri da kike gani bance miki babu shi ba amma mafi yawancin lokaci hali yake tararwa, yauwa shima kuma gashi nan ya gamu da hashi gamon don dazu da safen nan nake jin albarin wai ya yanke jiki ya fadi cikin kwandunan tunatiri a kasuwarsu sai da aka ciccibo shi rangatanga aka kawo shi gida. Ni da yaya Dija salati mai kafi muka kama yi yayin da it akuma ta ci gaba da fadni, uhun menene wannan in ba bakin ciki da damuwa ba da yake nema ya haddasa mishi ciwon nan na zamani da ake fama da shi na hawan jini. Ni da yaya Dija bamu iya daukar abinda ya.samu babanmu a yanda Yakumbo Halima ta dauke shi ba wato a'inda babanmu ya shuka ne yake girba tausayin shi ne ya kamamu nan take muka soma yin kuka muna fadin, ba laifinshi ba ne Yakumbo ba laifinshi bane kune kawai baku san abinda muguwar matar nan take yiva baba ba na asirce-asirce da sihiri iri-iri. Yaicumbo ta mike tsaye nuna alamar tafiya tana fadin, to ai shi kenan ku kuka san abin yi tunda ubanku ne ni kam ni nazo na gaya muku sai kusan abinda kuke ciki. Yaya Dija ta kawo kudin mota ta bata. Tana barin gidan ta kalleni, daga irin wannan faduwar ne fa ake rasa wani bangaren na jiki, ni yasu baba Lantana ta ciccire mu a rayuwa in kuma.muka barta ta zama sanadin nakasar ubanmu muna kallo to ta gama damu don wa muke da shi kuma bayan shi din? A hankali nace mata babu musamman ma da yake kullum a cikin alkawarin neman, mana dangin ubanmu kike sai dai har yanzu shiru. A fusace ta juyo gareni kefa ba wani hankali ne da ke ba bakya ganin kullum a cikin mas'aloli muke bamu fita wannan ba mu sake fadawa wancan? Bain sake yin wata magana ba bayan fadin haka ne da nayi. Nan da nan muka shirya tafiya gida bayan ta tura an gayawa mijinta halin da babanmu ke ciki, a hanya sai kallonmu ake yi ana zunde ana nunamu tamkar dai ba a sanmu ba, wai dan rikicin da akayi a gidan nan ne ta ya sa mutane suke yi mana irin wannan kallon, nace mata eh tace to ai sai su yi tayi su ne abin fada baya yi musu kadan nace haka ne. Muna shiga gida baba Lantana ta soma sakin magangaiiu'ai dama da kika gudu can wajenta kika tafi ta 6oye lki to ai zancen bai kare ba in ma kuma yi kukayid on ku kunyatani in tozarta gaban mutane to ba ni kuka yiwa ba ubanku kuka yiwa shi kuka kunyata kuka tozarta kuka nunawa jama'a cewa shi din ba komai bane a wurinku bai kuma isa da ku ba ko ba komai kuma ni kam ai gani nan a zaune daram lafiyata kalau shi ne bakni cikinku yake sashi yanaa tintsirewa a cikin jama'a yana faduwa, in kuka yi sanadinshi bukatarku zata biya tunda dama fatanku kenan gashi can a kwance magashiyan ai cikin yardar ubangiji bakin cikin ku ne zai yi sanadinshi. Wani irin mummunan faduwar gaba na samu abinda na tabbatar kuma shi ne itama yaya Dija abinda ta ji kenan saboda zaburar da naga tayi ta nuf dakin da yake kwance. Ku daiyi a hankali kar ku takamin leda da kafafuwanku masu datti don yanzu na gama gogeta babu kuma komai na uwarku a ciki balle ace za a shiga min da gadata. Halin da babanmu yake ciki yafi gaban bayani numfashi yake yi sama sama ga kuma karin ruwa ana yi mishi. abinda muka tabbatar shi ne wadanda suka dawo da shi ne sukazo da wanda ya dan dubashi da gani har yaya-Dija kuka muke yi saboda bamu taba ganinshi cikin halin rashin lafiya irin wannan ba. Ai ba ku yi kuka ba tukunna sai randa kukayi mishi farat daya ko kukayi mishi sanadin hannu da kafa ranar ne zaku gane kunyi kuskure, ai kun san ni dai ba-zan yi zaman jinya ba ko balle inje ina hidima da dawaniyar najasa. Yaya Dija ta mike tsaye ta kalleta rike da labulen dakin nata-da tayi tace mata, matan arziki ai su ne masu hidima da jinyar mazajensu don neman albarka da rahamar ubangiji ai ke ubangiji ba zai yi miki wannan alherin ba ba zai jarrabi wani da jinyar da za ki yi hidimarshi ba balle ki samu wannan alherin. Yaya Ibr him ya shigo ya samesu nan take ya soma yiwa yaya Dija fada, ke da kika zo kika samu wannan al'amarin kum mre ya kaiki tanka wata magana. Ya juya ya fita bayan ya bamu umarnin kintsa baban namu don tafiya asibiti. Muna kokarin kintsa shin baba Lantana bata fasa magana ba ba, ba dai ke ce mai daure mata gindi ba? Yarinyar da ta san taje kwanan gida gidan saurayi an kamata tana yin hakan yafi a kirga anyi nufin aurar da ita don neman mata rufin asiri kin sata ta gudu taje wajenki kin 6oye ta? To da albarkar masu albarka sai ta durkusa a tsakiyar dakinku ta haifar muku dan shege kuma kun goyashi a bayanku ke da ubanku da yake biye muku, babu wanda ya sake tanka mata. Gwajin farko a asibiti likita ya bayar da tabbacin hawan jini ne ya yi mishi yawa yake nema ya taba mai zuciya kan haka ya bashi gado aka kwantar da shi a dakin masu cutar hawan jini. Yaya Dija da mijinta suka koma gida ni kuma na zauna tare da shi, ban san yanda akayi ba cikin dare sai ga Sallau ya zo, sannu Mero. Na ce mishi yauwa ba tare da na daga kai na kalleshi ba, yaya mai jikin? Nace da sauki. Ya ja ya tsaya yana kallon baba nima na ci gaba da al'amurana, na ce ko zan karbe ki ne kije gida ki huta in kwana tare da shi in yaso da sate sai ki zo ki karbeshi? Lokacin ne na san na dago na kalli Sallau da nufin tanbayarshi shi kuma a waye dinshi da za mu yi irin wannan canjin ji da shi? Yanayin da na gani a tare da shi ne ya hanani yin hakan cikin natsuwa sai na ce msihi a'a Sallau jeka gida kawai abinka na gode. Bai tafin ba sai ya tsaya muka kwana tare a asibitin, yanda kuma banyi abcci ba haka shima bai yi ba. Da sassafe yaya Ibrahim ya zo duba mu ya kuma kawo mana abin karyawa da zai tafi ya kawo kudi ya ba ni ya ce in rike a hannuna ko za a nemi wani abu, nace mishi to tare da godiya. Yaya Dija bata zo ba sai da ta kammala abincin ranar gidanta ta zo mana da shi hakan Yakubo Halima ta kawo mana tuwon dare. Mutanen unguwarmu makwabta, abokan zaman baba na kasuwa suka yi ta zirga-zirgar zuwa don dubashi duk wanda yazo kuma zai kawo wani dan alheri ya bayar sai dai kalamand a suke f rtawa ne basa yi min dadin ji kai rashin van uwa kow ani tsayayye bai da dadi in banda haka yaushe za a ce yarinyar da ta ja maka irin wannan tozartar tayi maka sanadin wannan mumnunan ciwon ita ce kuma mai yin jinyarka to yaushe ma kuma zaka warke? Hankalina tashi yake yi a duk lokacin da na ji suna fadin hakan in kasa fahimtar abinda na yi na tozarta babana, kamo ni da aka yi a gidan su Mubarak ne tozartawar da suke magana a kai ko kuwa watsa taron masu daurin auren da yara suka yi? To ko ma dai menene sai nake ganin tamkar in har da adalci cikin almarin ba laifi ne da ya dace a daukeshi a doramin ni kadai a kaina ba. Tunda baba Lantana ta gane irin zirga-zirgar da mutane suke yi wajen zuwa asibiin sai itama ta soma zuwa kulum
Chapter 2 · 0% Book details