Sashe 4
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daya aka yi min ba kaloli ne daban-daban kara fito da sabbima suke yi, baki ciki in ya dameni sai inji kamar in gudu in yi tafiyata in tafi can inda babu wanda ya sanni in yi zamana sai kuma ince to babana fa, wa zai yi min jinyarshi? Yaya Dija fa ita me tayi min da zan tafi in barta? Sai in tsinci kaina dayin wani tunanin ince to ai ina ji ana cewa babu wam dauwamammen abinda ya ke zuwa ya tabbata, in dai ba ik n ubangiji bane don haka duka binda ake yi zai wuce in rudi kaina da cewar da nake yi nayi na wai watarana sai labari ina fadin hakan kuma zanji zuciyata tana tambayata to yaushe ne naki wataran zai zo? Wanda ni kaina ban sani ba ina raye ne zanga wataran ko sai na mutu ban sani ba tunda ni kam ai kullum al'amurana kara cabal6alewa suke yi bakin cikina kuma yana kara karuwa. Yaya Dija ta zo duba jikin babanmu samuna da tayi cikin wani irin hali ya yi matukar bat amata rai saukin abin ma shine da muka san ba ku yi komai ba amma da ya karbi wanna mahaukaciyar kyautar da kikayi mishi ai da bamu san iyakacin bala' in da muke ciki ba a yanzu amma yanzu kina yin aure shi kenan mijin da ya aurehi da duk wani wanda ya danganceshi zai ce karya ne sharri kawai aka yi mana mai yin sakamakon kuma zai yi mana wato da Mubarak ya taba ni da musibar ta wuce haka kenan bata tsaya ba ni amsar maganar ba sai ta ce min Umman Mubarak ta aiko da kayaiyakinki da suke wajenta ciki kuwa har da wani bakin karfe ta tsareni sosai da idonta kafin ta buda baki ta tambayeni kin gane abinda hakan ke nufi? Nace mata eh, bata bar ni ba sai ta ce min me yake nufi? Cikin natsuwa na ce mata kar in sake shiga gidansu tayi maza ta ce to madalla gara da kika gane hakan, da ya karbi kyautar da kikayi mishin ma da irin korar da sukayi mishi kenan koma su yi wadda ta fita. Ko yake ko dan Umma bata yiwo min irin wannan aiken ba nima ba zan sake dosan gidansu da nufin wata mu'amala ba saboda abin kunyar da ya faru ga kuma irin abinda hakan ya zamewa Mubarak amma kuma sai naji tamkar ba ta yi min adalci ba ko kadan ban ji dadin abinda tayin ba don kuwa ita din uwa na dauketa duk da da itama na sani don Mubarak din take yi min duk wani abinda take yi min. A wannan lokacin sai na rinka iin tamkar tubeni aka yi sirara aka jefar da ni cikin taron jama'a da bani da kowa a cikinsu balle wani mai taimako amma kuma ban yarda na munawa yaya Dija tsananin damuwata ba don kar in kara mata tata damuwar tunda har itama marasa atuncin yaran unguwarmu in suka hangota rera mata wakokin suke yi kasa-kasa amma ba da karfi ba kamar yanda suke yi min. Sannu a hankali sai babana ya saau sauki har ya Soma fita kasuwarshi saboda tababcin da likita ya bayar na jinin nashi ya sauka amma ba ana nuiin ya warke ba ne shi jini in ya riga ya soma hawa to ba a daina sha mishi magani don ko wane loakci zai 1ya tashi, wannan shi ne bayanin da likitan ya yi mana a ranar da mukaje ganinshi ni da baban nawa. To Dr. Meke kawo ciwon hawan jini? Na yi mishi tambayar don in kara sani, sai ya ce min akwai jinsin mutanen da ke da jini wanda yake da irin wannan matsalar su ne masu yin ciwon a dalilin sun gajeshi sannan Wasu yakan sansa a dalilin tsananin damuwa ko kuma yanayin abincin da ake ci shi yasa yake de kyau mu rinka kula da abincinmu mu kiyayi abubuwa marasa amfani irinsu gishiri, barkono, kanwa da makamantansu, sannan mu rinka yawan motsa jiki, motsa jiki yana da amfani kwarai ga lafiyar jikiumu kin gane? Nace mishi eh Dr. Na gode. Rike wannan bayanin da likita ya yi min da nayi sai na ejiyewa kaina ya zama ka'ida kullum in baiwa babana magani kwaya daya da kuma yayi min korafi kan maganin yana sashi yawan taba ruwa sai na mayar mishi da shan amganin nashi a lokacin dare haka nan jin saukin babana baisa na fita hanyar kula da abin karyawarshi ba ko da kuwa iyakar abinda nake da shi kenan saboda na iga na gane har da yunwa cikin rashin alfiyar tashi, ina kuma yawan gaya mishi cwar baba ka rinka shan timatir in ka gansu masu kyau kana kuma cin danyar kubewa kar kuma ka rinka yarda mai kankana ko ayaba yana wuceka baka saya kaci ba komai kankantarshi ya ce min to. Baba Lantana dake yawan kasa kunne wajen sauraron maganarmu ta ce eh 'yan kudin da yake kawowa wadanda dama ba isar mutane suke yi ba su ne.kike koya mishi yanda za tinka cinyesu a waje ba saboda. sharrinki kankana da ayaba kuma maganin me suke in ba iya shege ba. Babana ya fara fita kasuwa sai dai abin mamaki shi ne ashe wai har shima bai tsira daga wakar da ake reramin din ba in an ganshi sai a yi tayi wasu 'yan iskan su rinka nunashi suna fadin shi ne mutumin da aka kama' yarshi a dakin saurayi har a dalilin hakan mijin da zai aureta ya ce ya fasa auren shi sauranyin ubanshi ya koreshi a gidan shi amma shi yana tashe da tashi 'yar a gabanshi sai ma kara sonta da ya yi. Wasu su ce to ance duk abin da take samowa shi take ba wa, ai mafi yawancin iyaye yanzu in dai ya'ya zasu basu kudi to magana ta Kare sai su yi abinda suka ga dama suna kallo kai amma kuwa to tir, wato shi yana can yana kici-kici da tashi matar itama ana can ana kici-kici da ita kenan? Sai a kwashe da dariya. Su m a yaran dake cincirindon sayen timatirin babana har ana layi ba a barsu a baya ba sun daina yayen su ng suka hanasu ko su suka hana kansu saye sai su saka sauri hatta rijiyar gidanmu da bata kafewa wacce kullum baba Lantana ke fada da masu zuwa diban ruwan cikinta su ma yanzu ba a zuwa diba. A wannan lokacin kusan kullum sai anyi kwashen timatir babana ya zama bage tuni sai jarinshi ya soma rushewa sai mai kawo kwandunan timatir attarugu tattasai albasa alaiyahu kubewa masu yawa sai ya zamo da kyar ake hada kudin daidai don haka in tsaya fadin an shiga wani halima a gidanmu na tsaya bata baki ne kawai. A wannan lokaci saboda samun wuri Asabe abinda ta ga dama talke yi min ina kallonta bana cewa komai sabdoa yanzu yanzun nan ne zata fara rera min waka in taga fuskata ta canza ta ce ba ni na kar zomon ba raiayc kawai aka bani, bana tanka mata don nasan bani da yanda zanyi da ita in karfin dambe ne ta jini gatan da nake da shi din da yasa ake tsorona babu shi banma san inda yake ba ga kuma aiken da Ummanshi ta yi min daga gidansu wanda nasan na nuna karshen mu'amalata da su ne. Asabe tana cikin tatamin irin tsiyar da taga dama ne rannan na farka cikin dare na ganta tana kwarara amai a cikin wani kwano duk da tsananin tsoratar da tayi da ganin da nayi mata ban gane abinda hakan ke nufi ba, na hadaki da girman Ubangiji kar ki gayawa baba kin ganni ina amai ba zan sake yi miki wakar da nake yi miki ba. Naceki yi mana ni ance miki wakar ta dameni ne? Amai kam ai sai na gaya ma ta na ganki kina y1 a kwano. Tayi ta bani hakuri mamakinta yayi ta kamani ko ina ruwana da ita da uwarta da zanje ina cewa na ganta tana amai oho? Tun daga rannan Asabe ta daina nemana da tsokana a fita hanyata da abubuwa iri-ii abin sai mamaki yake ta bari sai a ranar da yaya Dija ta zo gida ne ina rakata take tanmbayata nalin da muke ciki da Aabe na bata labarin abinda ya faru sai naga ta ja ta tsaya tana kallona cikin natsuwa kafin ta ce min, akr dai ciki ne da yarinyar nan? Kai haba gashi yau na ganta ta canza to ita uwar ta ta ba zata ganc ba sai an gaya mata wacce irin shashashar uwa ceh aka? Shiru nayi cikin tsananin faduwar gaba, ciki? Na yiwa kaina tambayar a cikin raina. Ai baka cima masharranci sai ka yiwa kanka mafi yawancin lokaci ai abin da ake yiwa dan wani shi yake samun naka ki ja bakinki ki yi shiru karki yardaki yi abinda uwar ta ta zata gane tunda ita mahaukaciya ce nace mata to... Rannan ina zaune a tsakar gida ina hidimar wankin kayan babane bayan na gama nawa a yanzu bana fada da kowa saboda Sallau dai mun dan shirya da shi tun daga kwanciyar asibitin baba da kuma lura da nayi naga yana mutuntamin baban nawa, Asabe kuwa tsoro take ji karmu yi fada in fadi abinda ta roke ni kar in fada bata san ma ni ko munyi fadan ba fada zanyi ba tunda yaya Dija ta ce min kar in fada. Cikina ne ya yi wani irin kuka na tunanin da irin dadewar da nayi ban bashi wani abu na hatsi ba, na waiwaya a hankali na kalli Asabe da baba Lantana da suke zaune cikin rana wai suna shan hantsi su ma zazzare idanu suke yi nuna alamar yunwar su ke ii kamar ni tunda a yanzu duk mun zama daya ni babu su ma babu, yanda nake kaiwa Azahar ban karya ba haka su ma suke kaiwa har gara nima yunwa bata cika gigitani ta fitar da ni cikin haiyacina ba don kuwa da ana sabo ko wani kawance da ita to da na ce munyi ba a yi ne kawai yasa ba zan fadi hakan ba amma duk da haka zan