← Book details Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 25

Sashe 15

Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ni ba zan zamo wani sabon al'amari a wurina ba don sunnar magabata ya bi zan kumaci gaba da girmamashi tare da soyaiyar da muka yi wa juna saboda mun yi ta mun gama ta ba tare da ta yi min wani sanadi na wulakanci ko tozarta ba a wurin jama'a, na kuma gode maka da baka yi amfani da kuskurena da wautata da sakarcina da sokoncin da na rayu a ciki a dalilin bani da mafadi ya sani nayi a kanka ba da ka yi amfani da damar da wadancan abubuwan suka sanyani na baka a kaina da ka yi dalilin da na kara zama shashasha sokowa sakarya ce ta aikata kuskure a rayuwarta, kuskure kuma har abada, don haka duk abinda ya faru tsakanina da kai tun daga farkonsa har zuwa karshensa kus... Ban kai karsen maganar da zanyi ba sai kawai na ii kafafuwana sun zurma cikin kwatar dake bayana, nayi maza na kalleshi cikin tsananin bacin rai nan take kuma na sake dago idanuwan nawa suka hadu da na Mubarak dake yi min wani irin kallo, yanayin da na gani a tare da shi ya tabatar min da cewar ba ji nayi kama ba shine ya hankadani cikin kwatar da na zurma. Kar ki sake yin kuskuren kallon idona ki ce za ki yi min rashin kunya irin wanda kika yi min yau in kuwa ba ki ji kashedinda na yi miki to za ki gane baki da wayo, sakarya kawai sokuwa shashasha mara wayo wacce rashinmafadi ya hanata sanin abinda ya dace da ita. Yana gama fadin hakan ya ja wani mummunan tsaki ya wuce yayi tafiyarshi ya barni cikin kwatar ko a jikinshi. Da kyar na iya zare kafafuwana daga cikin kwatar takalmana kuwa asararsu nayi don kafafuwan nawa kadai na iya zarewa, a hakana rinka diddingisawa na doshi gidan Yakumbo Halima cikin zuciyata dai ni kadai nasan abinda nake ji game da Mubarak, na tsaneshi na kishi na rinka jin wani irin ciwo a zuciyata game da shi, babu abinda ke kai kawo a zuciyata in banda na tunanin yanda zanyi in dau fansa a kanshi kan irin wulakancin da ya yi min, da dai ace so shi ne samu to da na tashi daga wannan unguwar na koma wata don in yi nesa da shi in dains ganinshi dan ya daena shiga harkokina. A haka na shiga gidan Yakumbo Halima, tana ganina ta kama yin salati, wane irin rashin dabara ne wannan Mero? In zaki fada kwata sai kuma ki fada da kafa duka biyu kamar wata yarinya 'yar karama? Ban iya ce mata komai ba kuka kawai na kama yi don daman daurewa kawai nayi na hana kaina soma kukan tun daga waje. Cikin hanzari ta tsame hanunta daga cikin kullin danwaken da take jefawa da sauri ta iso inda nake tsaye ina ta faman kuka. Haba Mero haba Maryamu da so don kin shiga kwata kuma sai ki tsayakina kuka? Ai tsautsayi ne shi kuwa kin ji ance bai wuce ranar shi ba, bari in kwara miki ruwa a kafar in wanke miki dagwalon sai ki shige bandaki ki yi wanka ki canza kayan jinki da wasu. Har nayi wanka na fito na gama abinda zanyi duka na zo wurin Yakumbo Halima na zauna ina tayata jifan danwakenta idanuwana basu daina zubar da hawaye ba, na kasa gane dalilin bakaken maganganunshi musamnman gorin da yayi min kan fasa aurena da Mansur ya yi sunyi min ciwo da yawa. Rarrashi, banbaki da wayon da Yakumbo Halima tayi tayi min ya sani kwashe bayani duka na yi mata. Dama ashe zancen da nake ji a gari na bar yanzu baku rabu da juna ba gaskiya ne? Tsuru na yi ina kallon Yakumbo ashe kuskure nayi da na yi mata wannan bayanin, ashe da ma kadan take jira da ni, to kuwa ba zai barki ki yi aure ba kin ji na gaya miki ke ya hanaki aure ya tsareki a waje a cikin gida kuma yana tare da matarshi duk tsiyar da yake yi mata wanda ke sanyata zirga-zirgar yaji tun da dai yana kusantarta ya biya bukatarshi a tare da ita ai aikin banza ne karyar iya shege kuma yake yi wanda bai Son mata ai baya kusantarta indai har da gaske yakeyi yanzu da ta tafi kwanan nan iyayenta suka aiko a gayawaAlhaji Muhammadu cewar tana da ciki wata biyu yayi musun cikin? Ba cewa sukayi sun janye sakin da yayi mata ba sukaje suka dawo da ita dakinshi kuma suna nan tare su na zamansu ana tarairayarta ana murna zata haifar m usu da ko ya, shi ne ke ba za ki yi zuciya ki kama mutuyncin kanki ki fita harkarshi ba sai ki je kina biye mishi kuna lalacewa tare... ta kama kuka irin wanda bai kwatantuwa. Jikina ya kama 6ari hankalina ya yi mummunan tashi ganin irin kukan daYakumbon keyi, na rantse aiki Yakumbo... kan in fadi abinda nake nufin gaya matan tuni ta rufeni da duka da hannaycnta duka biyu, rantsuwar karya zaki yi min saboda kin maidani shashashar uwa to ai ni da yaya Ramatu duk daya muke uwa daya uba daya muka tasha nono ta bani da kike nema ki maidani mara mutunci. Tana kuka take wannan bayanin. Tuni nima na shiga nawa kukan, ba don dukan da tayi min din ba sai don bakin cikin al'amarina da bakni cikin yanda na zamo gaba daya iyayena da jama'ar gari suka yarda da cewar lalacewa mukeyi ni da Mubarak, yaya Dija ce kawai na tabbatar ta yarda da maganar da nayi m ata na babu komai a tsakanina da shi don ta babans kuwa ba zan iya cewa koami ba tundaban taba jin ya bude bakinshi ya fadi wata magana ba balle in san a wane hali ya dauki lamarin. Ban san abinda ta gani ba ko abinda ya faru ba naga maimakon dukan da take ta kai min da hannayenta duka biyu ta jawoni jikinta ta kankame da karfinta kuka mai yawa ta yi kafin daga bisani ta sakeni, ki yi aure Maryamu ki yi aure abinda kawai zan gaya miki kenan. Magaiar da ta fara yi kenan bayan ta gama kukan nata. Cikin sauri na ce mata to Yakumbo ba tare da na san wanda zan auran ba sai dai kawai don in kwantar mata da hankali. Alkawarin da nayi wa Yakumbo Halima na cewar zanyr aure ya sans himmatuwa wajen ganin na fidda mijin aure ko da kuwa wane iri ne babu maganar tsayawaduba cancanta balle a yi maganar zabe, aure kawai nake so in yi ko zan samu in fita daga zargin da ake yi min na akwai wani abinda ke faruwa tsakanina da Mubarak na lalacewa sannan yin auren nawa zai zamo dailin da zan bar unguwarmu in yi nesada ita in daina ganin Mubarak wanda a yanzu na tabbatarwa kaina da cewar in har akwai wani mutumin da na tsana a rayuwata a halin da nake ciki to shi ne na tsani Mubarak, na tsani duk wani abinda ya shafeshi, na tsani duk wani labari da ya danganceshi, musamman ma labarin matarshi da cikin dake gareta wanda kuma ya zamo shi ne labarin baba Lantana da take wuni tana bayarwa ta rinka fadin karyar banza karyar wofa, yana kinta yake kwabewa a gabanta? Sai kuma ta ja wani mummunan tsaki ta ce, ku dai da ya mayar sakarkaru ke da ubanli sai ku yi tayi ya rinka samunki yana rage gajiyarshi ta rana a kanki tunda haka kuka zaba. Rabon da in tankawa baba Lantana ko wani nata wata magana har na manta saboda abinda nake ji yafi karfin duk wasu maganganun na ta ciwo a raina. Rannan ina tsaye tare da wani sabon saurayi da nayi wanda inda ya biye min da ko kwana goma bai yi da fara zuwa wurina ba ya turo iyayenshi aka daura mana auren saboda irin karbar da na yi mishi da kuma za a tsareni a tambayeni dalili na na yin irin wannan bare-baren a kanshi abu guda da zan iya fadi kawai shine ba dan unguwarmu ba ne ina son aurenshi ne kawai don in samu in yi nesa da unguwar in banda haka babu wani dalili. Ina tar da shi muna hira a kofar gidanmu sai kawai ga Mubarak tamkar daga sama aka jehoshi, gabana ya yanke ya fadi saboda ganin inda muek zaune ya tunkaro gauan-gadan nayi maza na kawar da kaina daga gareshi saboda irin kallon da na lura yana yiwa wanda muke tare da shi din wanda shima na gane ya tsargu da Mubarak din. Yana isowa sai na ji ya ce mishi, malaml afiya na ganka anan wurin? Da sauri mutumin ya daga ido ya kalleshi latiya? Ban gane tambayar taka ba, ya zuba mishi ido cikin natsuwa yana kallonshi, wannanai iyalina ce baka ji abidna ke tsakanina da ita ba ne? Ya shiga waige-waige hankalinshi a tashe jin da ya yi Mubarak ya ce mishi ti din iyalinshi ce. Ai ban san matar aure ce ba ni asanina... Kan ya karasa bayanin ya yi maza ya ce mishi, bar nan kawai tun kafin abin ya kai ga ranka ya baci. Yanzu kuwa in ji mutumin, ko raina b a zai baci ba ma ai da sanina b za ni wurin iyalin wani ba, ita ta ha'ince ni ta boye min gaskiya, ya kama hanya ya yi tafiyarshi, nima na mike na shiga gida na barshi a wurin ban tsaya jin wata magana tashi ba. Ina gida akan gadona a kwance ina tunanin al'amarin cikin zuciyata dai nasan babu mutumin da yake shiga harkokina yake takuramin yake bata min rai yake sanyani bakin ciki a rayuwata irin Mubarak sai daiban san yanda zanyi da shi ba tunari mai tsanani na shiga ciki har daga karshe na yankewa kaina hukuncin komawa gaban Yakumbo Halima in gaya mata abinda ke faruwa don kar ta dauka ban ji maganar da tayi min na inf ito da miji ba. Na gyara na yi kwanciyata da tunanin na kaiwa Yakumbo Halima bayanin abinda Mubarak kc yi min. Ina kokarin tilasta kaina yin bacci kenan sai na ji Asabe tana kwalawa sunana kira, cikin irin muryar tsoro ne ya kanani saboda sanin
Chapter 15 · 0% Book details