← Book details Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 25

Sashe 23

Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi ta za... Ta dakamin tsawa na kame bakina na bar maganar na koma yin kuka, tun ina yi ni kadai har itama ta shiga tayani muka yi tayi sai da muka gaji muka yi shiru. Mubarak ya saba zagina ko tsareni ya gaya min bakaken maganganu iya son ranshi a duk lokacin da ya turo maganar aurena wajen babana ya ce ba zai bashi ni din ba, to ni yake tsarewa ya gaya min duk wani abinda yake son fada, in yi bacin ran in hakura amma bai taba gayamin maganar da ta daki zuciyata ta sani bakin cki na yi kuka mai tsanani irin wannan karon ba. Na gaji, na gaji, na gaji da iin wulakanci da cin zarafin da yake yi min a kan aurena don kawai ya ga bani da auren da ina karkashin inuwar aure ai shima da bai isa ya yi min irin wadannan abubuwan da yake yi min ba don haka ya zame min dole in tsaya in yi duk wani abin da zanyi don ganin na yi auren saboda in huta da wannan wulakancin da kuma cin mutuncin kan haka yasa washegari da sassafe na yi shiri na tafi gidan Yakumbo Halima wacce ta dade tana kirana inzo muje wurin malaminta da take ta faman bani albari. Ina shiga gidan ta fara murmushi, 'yar halal kin ko ambato yanzun nan nake maganarki a zuciyata. Na tayata murmushin kafin na tsuguna na sOma gashcta tana amsawa tana kallona cikin wani irin yanayi dake baiyanar da jin dadinta. Kai wannan yarinya da iya kwalliya kike wannan kuma wane irin dinki ne? Mu ganshi. Na numa mata ta gansi sosai, to me sunanshi? Na gyara na koma na zauna cikin natsuwa, kwalliya ta fa ke kadai take burgewa. Ta yi maza ta ce wane mutum ai duk wanda ya kalleki ya san ke din gwanar kwalliya ce Mero ai rashi aurenki ba yana nufin ke din kina da wani aibu a tare da ke ba ne a'a lalura ce dake wani aljani ke gareki wanda yake biye da ke bana baki albarin abinda wannan maiamin ya gaya min a kanki ba, ai nace miki ki zo muje wurinshi don ya ce min akwai abinda zai yi ya rabaki da shi kika fi zuwa. Na ce to ai gani na zo yau Yakumbo zuwa nayi don ki kaini inda duk za ki kaini na gaji, na gaji da wulakancin da Mubarak yake yi min, na kwashe bayani duka na yi mata. Maimakon yauma ta nanata maganarta da kullum take fadi cewar shi ne ya yi min sihirin da na kasa yin aure sai naga ta yi murmushi kafin ta ee, ja'ira shagwaba da gata ne suka sashi yin abubuwan da yake yi su ma iyayen na shi ai sun yi nadamar hanashi aurenki da sukayi yanzu tunda kwanaki ai ance korar matar tashi ya yi ya ce a barshi kawai ya yi zamashi shi kadai tunda dai suna kallo an hanashi ke sun kumna yi ko oho da hakand a akayi saboda su basu damu ba ai shi ne dalilin da ya sa ita Hajiya Ummulkhairin ta kama hanya taje gidan Dijan to shi kuma babanki shima ya kafe akan ba zai basu ke ba. Na ce wannan ruwansu ne Yakumbo. Ta yi maza ta ce ruwan su ma mai ma ya kare musu bari in yi maza in shirya mu tafi tun rana bata yi zafi ba don akwai 'yar tafiyar kafa da za a taba. Nace mata to Yakumbo ai ma ni tafiyar kafa ba mas' alata ba ce na riga na saba da ita, tayi amza ta ce, aifa na tuna kin yi ta ba kadan sanda kike zuwa wajen koyon sana' ar nan gashi ya zama tarihi sai amfanin shi ake ci ko ince muke ci tunda yaushe rabon da raina ya 6aci a kan dinkuna? Ace jaruntaka babu dadi? Bari ki gani ins hirya yanzu mu tafi ba ma sai na tsaya wanka ba tsaka tsami kawai zanyi in mun dawo in ban ji kuiya ba na yi wankan. Nan da nan Yakumbo ta shirya muka kama hanyr fita, gani bata tambaya ba ya sani tambayarta, dama kin gayawa kawu ne? Ta dan yi murmushi, mu yan tsofaffini nan da auren mu ya riga ya tsufa yaushe za ace komai za mu yi sai mun tsaya wani tambaya ai shima yasan sabgogin iyali yawa ne da su. Shiru nayi na ja bakina na tsuke tunda nasan babu halin in tsaya ina tambayarta Yakunbo shi aurenn yana tsufa pe a dalilin masu yinshi sun tsufa? Bayan mun sauka a mota tafiyar kafa fosai mukayi a ciki jeji muka wuce wasu rugage muka mika cikin wani irin surkukin daji Yakumbu damun san wurin nan haka yake ai da hayar babura muka dauko a dan kauyen nan da muka wuto. Hararata tayi, kufa yaran yanzu bakuda wata jaruntaka wai ke kina so ne ki nuna min kin gaji da tafiyar kafar da ake yi ko? Na yi murmushi kawai na yi shiru muka ci gabada tafiya da kyar muka iso wata mararraba da ta ce min wannan da muke kai yanzu ita ce mai kaimu gidan nashi nace mata to. Mun samu yan daidaikun mutane da ke jiran a sallamesu amma ana sanar da shi isowar Yakunbo yace a shiga da mu. Na yi mamakin ganin mutumin da ta ce min shi ne malamin na zaci ganinshi dattijo amma sai na ganshi matashi ma'abocin tsabta da natsuwa ga sutura tamkar dai ba a cikin dajin nan yake zaune ba. Hajiya barka da zuwa, ya yi maganar cikin murya mai cike da kamala suka gaisa nima na gaisheshi. Maryamu ko? Ta yi murmushi ta ce haka aka yi kuwa malam, idonshi a kaina ya ce, ai mun gani shi mutum ai kowa da sunanshi yake yawo, gabana ya fadi jin da nayi ya ce ya gani kar dai irinsu ne kullum malamanmu suke yi mana wa'azi a kansu? Cikin Zuciyata na ke wannan tunanin. Ya jawo wani littafi ya bude yana karantawa na dan samu saukin damuwa a tare da ni ganin littafi yake karantawa su kuma malamanmu kulum suna yi mana wa'azin ne akan masu buda kasa suna masu duba ko bokaye to tunda wannan ba kasa bace littafi ne kenan ba duba bane yinshi kuma bai zamo laifi ba. Mas'alar aure ko? Ya yi tambayar ba tare da ya kalli kowa ba idonshi a kan littafin shi, ta yi maza ta ce mishi eh malam aure ne damuwar kullum sai manema sun fito mata gasu gasu kamar za a yi auren sai kuma a nemesu a rasa sun gudu, tun ina ganin laifinta ina ganin kamar ita ke korarsu har na daina jin zafinta na koma tausayi saboda na gane babu hannunta cikin lamarin. Ya girgiza kai cikin natsuwa tare da fadin, ai ba zai bari a aureta ba, wa kenan malam? Ta yi tambayar tana mai kallonshi. Ya ce mai ita mana ai wani maketacin aljani ne yake tare da ita shi ya sa babu halin tayi aure don ba zai bari ba shi yake korar mata samarin da siddabaru iri-iri suna tare da ita su rinka ganin ta caccanza musu tanayin launi lauru su ganta fara su ganta baka su ganta ja su ganta bulu ko kumna su rinka ganin fuskarta tana rabuwa biyu sai ta koma ta hade ta sake rabewa ta sake hadewa, to kinga kuwa ai babu lafiya. Yakumbo tayi maza ta ce, ko kadan cikin sanyin murya ni da kaina da ba sosai nake yarda da irin wadannan abubuwan ba jikina bari yake yi jin bayanin malamin. To yanzu yaya za a yi kenan malam? Ya ce eh to da yanda za a yis ai dai kumaaiki ne babba sai an rabata da shi gaba daya in ba a tsaya an yi hakan ba ko anyi auren kashe mijin zai yi don haka sai an yi juriya da jarumtaka. In dai za a rabata da shi ai duk wani abin da za a yi ba zai gagara ba malam a gaya mana kawai abin da za a yi. Ya ce to babu laifi akwai aiki da za a yi wanda za a bukaci sadaka mai karfi ko dai shekararrun zakaru guda bakwai ko kuma rago sannan zata rinka zuwa nan muna yi mata wani aiki har kwana bakwai in har komai ya tafi daidai to kafin cikar kwanaki bakwan din nan mijin da zata aura zai baiyana ana gamawa sai a daura auren mu kuma in ayzo to shi ne zai biya ladan aikinmu baku ba. Nan da nan Yakumbo ta shiga yi mishi godiya tare da tambayar to wanne ya yi tsakanin rago da kajin? Ya ce a'a ao na za a hada ba rago yafi sai dai in babu hali sai a yi da kajin duk daya ne. Ta ce to bari mu bada kudin ragon nawa ne zai yi? Ya ce daga fan goma zuwa sha biyar ko ashirinn duk wanda kika bayar zai yi. Na yi kasake ina tunanin ta inda kudin da ya ambata zasu fito sai kawai naga Yakumbo ta jawo lalitarta ta ciro kudi ta kirga fam goma sha biyar cif ta mika mshi, ya ce zuba nan cikin wannan kwaryar, ta bi umarnin nashi ta zuba muka yi mishi sallama muka fito. Babu abinda yafi komai yi min dadi irin cewar da ya yi kafin a kammala aikin mijina zai baiyana ana gamawa kuma sai a daura auren shi nne ma wai zai biyashi kenan nima zan yi aure babu sauran a tareni a zageni babu sauran a yi min gori, babu sauran a rinka nunani a unguwa ana fadin babu sauran sa'ata a' yan matan da ke yavwo a unguwar. Washegari da safe naje na samu babana a rumfarshi bayan na kammala shirina na dan zauna kamar zanyi mishi hira sai da na bari Sallau ya dauki kwanduna ya nufi kasuwa sai na kalli babana na ce mishi baba yaya Dija ta aiko ni wurinka wai ince maka akwa wata yarinyar bazawara mai hankali kusa da su ko za a yi magana da ita. Gabana yana faduwa na yi mshi bayanin, sai na ji ya ce to ina
Chapter 23 · 0% Book details